Uwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - tana bada labarin cewa iyalan gidan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - tun lokacin da Annabi ya zo Madina basu taɓa ƙoshi da alkama ba tsawon kwana uku ajere har (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya koma ga Allah.
- Bayanin abin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yake a kansa shi da iyalansa na ƙarancin rayuwa, domin rayuwa (ta haƙiƙa ita ce ) rayuwar lahira.
- Ibnu Hajar ya ce: Abin da yake a bayyane shi ne cewa dalilin rashin ƙoshinsu galibi ya kasance ne saboda ƙarancin abu a wurinsu, akan cewa su sun kasance sukan samu saidai suna fifita wasunsu ne akan kansu.
صحيح البخاري (7/ 75) (5416). صحيح مسلم (4/ 2282) (2970). المفهم لما أشكل من تلخيص كتاب مسلم (7/ 129). البحر المحيط الثجاج في شرح صحيح الإمام مسلم بن الحجاج (45/ 129).