Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

ƊABI'U IRIN NA (ANNABI) MUHAMMAD

Hadisai 75

Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance idan zai yi atishawa, yana sanya hannunsa - ko tufafinsa - a bakinsa, kuma ya runtse - ko matse - muryarsa da shi

عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: كان رسولُ الله صلى الله عليه وسلم إذا عَطَس وضَعَ يَدَه -أو ثوبَهُ- على فيهِ، وخَفَضَ -أو غضَّ- بها صوتَهُ.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance idan zai yi atishawa, yana sanya hannunsa - ko tufafinsa - a bakinsa, kuma ya runtse - ko matse - muryarsa da shi.
Abu Daud ne ya ruwaito shi da Kuma Tirmizi da AhmadDarajaIngantacce ne
Sharhi

(Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata aagre shi ya kasance idan zai yi atishawa: Da farko: Yana ɗora hannunsa, ko tufafinsa akan bakinsa; dan kada wani abu da zai cutar da abokin zamansa ya fita daga bakinsa ko hancinsa. Na biyu: Yana ƙanƙar da muryarsa ba ya ɗaga ta.

Fa’idoji
  1. Bayanin shiriyarsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a atishawa, da kuma koyi da shi a hakan.
  2. An so (mai atishawa ya) ɗora tufafi ko hankici da makancinsa akan bakinsa da hancinsa idan zai yi atishawa, domin kada wani abinda zai cutar da abokin zamansa ya fito daga gare shi.
  3. Kanƙar da murya a atishawa abin so ne, hakan yana daga cikar ladabi, da kuma kyawawan ɗabi'u.
Madogara

سنن أبي داود (7/ 375) (5029). سنن الترمذي (4/ 461) (2745). مسند أحمد (15/ 412) 9662). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (4/ 440). تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص528). بهجة الناظرين، لسليم الهلالي (2/ 149). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 678). كنوز رياض الصالحين لمجموعة من الباحثين (11/ 432).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Da ba dan kar na tsanantawa muminai ba - ko ga: al'ummata ba - dana umarce su da yin asuwaki a yayin kowace sallah

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «لَوْلَا أَنْ أَشُقَّ عَلَى الْمُؤْمِنِينَ -أَوْ: عَلَى أُمَّتِي- لَأَمَرْتُهُمْ بِالسِّوَاكِ عِنْدَ كُلِّ صَلَاةٍ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Da ba dan kar na tsanantawa muminai ba - ko ga: al'ummata ba - dana umarce su da yin asuwaki a yayin kowace sallah".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa shi da ba dan tsoron wahala ga muminai daga al'ummarsa ba da ya wajabta musu yin anfani da asuwaki tare da kowace sallah.

Fa’idoji
  1. Tausayin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga al'ummarsa, da kuma tsoron wahala akansu.
  2. Asali a umarnin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - (shi ne) wajabci, sai dai inda dalili ya tsayu akan cewa shi nafila ne.
  3. An so yin asuwaki da kuma (bayanin) falalarsa a yayin kowace sallah.
  4. Ibnu Daƙiƙul id ya ce: Hikima a mustahabbacin asuwaki a yayin tashi zuwa sallah (shi ne) kasancewarta halin neman kusanci ne zuwa ga Allah, sai ya hukunta ka zama a halin cika da tsafta dan bayyanar da ɗaukakar ibada.
  5. Gamewar hadisin ya ƙunshi asuwaki ga mai azimi koda bayan zawali ne, kamar salloli biyu: Azahar da la'asar.
Madogara

صحيح مسلم (1/ 220) (252). صحيح البخاري (2/ 4) (887). تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، لعبد الله البسام (ص46). تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام، لابن عثيمين (1/ 50).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan zai yi sallar Asuba sai ya zauna a wurin sallarsa har sai rana ta ɓullo tana ɗage

عَنْ جَابِرِ بْنِ سَمُرَةَ رَضيَ اللهُ عَنْهُ: أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَانَ إِذَا صَلَّى الفَجْرَ جَلَسَ فِي مُصَلَّاهُ حَتَّى تَطْلُعَ الشَّمْسُ حَسَنًا، وَقَالَ: كَانَ لَا يَقُومُ مِنْ مُصَلَّاهُ الَّذِي يُصَلِّي فِيهِ الصُّبْحَ أَوِ الغَدَاةَ، حَتَّى تَطْلُعَ الشَّمْسُ، فَإِذَا طَلَعَتِ الشَّمْسُ قَامَ، وَكَانُوا يَتَحَدَّثُونَ فَيَأْخُذُونَ فِي أَمْرِ الجَاهِلِيَّةِ، فَيَضْحَكُونَ وَيَتَبَسَّمُ.
Jabir Ibnu Samura - Allah Ya yarda da shi -: Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan zai yi sallar Asuba sai ya zauna a wurin sallarsa har sai rana ta ɓullo tana ɗage, kuma ya ce: Ya kasance ba ya tashi daga wurin da ya yi sallar Asuba har sai rana ta ɓullo, idan rana ta ɓullo sai ya tashi, kuma sun kasance suna tattaunawa sai su shiga labari cikin al'amarin Jahiliyya, sai su yi dariya shi kuma ya yi murmushi.
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Daga sunnar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa shi idan ya yi sallar Asuba sai ya zauna a wurin sallarsa har sai rana ta ɓullo a ɗage, kuma ya kasance ba ya tashi daga wurin sallarsa inda yakeyin sallar Asuba a ciknsa har sai rana ta ɓullo. Idan rana ta ɓullo sai ya tashi, kuma sun kasance suna tattaunawa sai su fara hira akan ambatan wasu daga cikin al'amuransu kafin Musulunci alhali shi ya yi shiru, sai su yi dariya wani lokaci kuma ya yi murmushi tare da su.

Fa’idoji
  1. An so yin zikiri bayan (sallar) Asuba har sai rana ta ɓullo, da kuma lazimtar wurin zaman sallar in babu wani uzuri.
  2. Bayanin abin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yake a kansa na kyawawan dabi’u da tattausan lamari, inda ya kasance yana zama tare da sahabbansa, yana sauraran zancensu da hikayoyinsu kuma yana yin murmushi tare da su.
  3. Halaccin yin hira da ambatan kwanukan Jahiliyya a cikin masallaci.
  4. Halaccin dariya da murmushi; domin cewa abin da aka hana shine yawan dariya.
Madogara

صحيح مسلم (1/ 464) (670). البحر المحيط الثجاج في شرح صحيح الإمام مسلم بن الحجاج (14/ 407). المفهم لما أشكل من تلخيص كتاب مسلم (2/ 296).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com