Ban taɓa ganin ma'abocin gashin kai ba mafi kyau a cikin kayan ado jajaye (mayafi da kwarjalle saƙar Yaman) kamar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ba -
Bara’u ɗan Azib - Allah Ya yarda da shi - yana bada labarin cewa shi bai taɓa ganin wani mai gashi ba, wanda gashin kansa mai tsawo ne ya kai kafaɗu, kuma yana sanya mayafi da kwarjalle baƙaƙe alhali a cikinsa akwai zanen ja mafi kyau kamar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ba -, ya kasance daga cikin siffofinsa na halitta shi mai nisan abinda ke tsakanin kafaɗu ne, mai yalwar ƙirji, kuma ya kasance mai tsakatsakiyar daidaituwa tsakanin tsawo da gajarta.
- Bayanin wasu daga cikin siffofin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - masu kyau a zahiri na kyawun gashi da faɗin ƙirji, da kyawun daidaituwa, da makamancin haka.
- Son sahabbai masu girma - Allah Ya yarda da su - ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, har cewa su suna hakaitowa kuma suna ruwaito ɗabi'unsa da siffofinsa na jiki da kuma na ma'ana ga na bayansu.
صحيح البخاري (4/ 188) (3551). صحيح مسلم (4/ 1818) (2337). تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، لعبد الله البسام (ص730).