Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Ban taɓa ganin ma'abocin gashin kai ba mafi kyau a cikin kayan ado jajaye (mayafi da kwarjalle saƙar Yaman) kamar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ba -

عَنِ الْبَرَاءِ رَضيَ اللهُ عنه قَالَ: مَا رَأَيْتُ مِنْ ذِي لِمَّةٍ أَحْسَنَ فِي حُلَّةٍ حَمْرَاءَ مِنْ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، شَعْرُهُ يَضْرِبُ مَنْكِبَيْهِ، بَعِيدَ مَا بَيْنَ الْمَنْكِبَيْنِ، لَيْسَ بِالطَّوِيلِ وَلَا بِالْقَصِيرِ.
Daga Bara’u - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Ban taɓa ganin ma'abocin gashin kai ba mafi kyau a cikin kayan ado jajaye (mayafi da kwarjalle saƙar Yaman) kamar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ba - gashinsa yana taɓa kafaɗunsa, mai nisan abinda ke tsakanin kafaɗu ne, shi ba dogo ba ne ba kuma gajere ba ne.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Bara’u ɗan Azib - Allah Ya yarda da shi - yana bada labarin cewa shi bai taɓa ganin wani mai gashi ba, wanda gashin kansa mai tsawo ne ya kai kafaɗu, kuma yana sanya mayafi da kwarjalle baƙaƙe alhali a cikinsa akwai zanen ja mafi kyau kamar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ba -, ya kasance daga cikin siffofinsa na halitta shi mai nisan abinda ke tsakanin kafaɗu ne, mai yalwar ƙirji, kuma ya kasance mai tsakatsakiyar daidaituwa tsakanin tsawo da gajarta.

Fa’idoji
  1. Bayanin wasu daga cikin siffofin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - masu kyau a zahiri na kyawun gashi da faɗin ƙirji, da kyawun daidaituwa, da makamancin haka.
  2. Son sahabbai masu girma - Allah Ya yarda da su - ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, har cewa su suna hakaitowa kuma suna ruwaito ɗabi'unsa da siffofinsa na jiki da kuma na ma'ana ga na bayansu.
Madogara

صحيح البخاري (4/ 188) (3551). صحيح مسلم (4/ 1818) (2337). تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، لعبد الله البسام (ص730).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
SIFFOFI NA HALITTA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com

Ban taɓa ganin ma'abocin gashin kai ba mafi kyau a cikin kayan ado jajaye (mayafi da kwarjalle saƙar Yaman) kamar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ba - · Hadisai tare da sharhi · Sabīl