عَنِ الْبَرَاءِ رَضيَ اللهُ عنه قَالَ: مَا رَأَيْتُ مِنْ ذِي لِمَّةٍ أَحْسَنَ فِي حُلَّةٍ حَمْرَاءَ مِنْ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، شَعْرُهُ يَضْرِبُ مَنْكِبَيْهِ، بَعِيدَ مَا بَيْنَ الْمَنْكِبَيْنِ، لَيْسَ بِالطَّوِيلِ وَلَا بِالْقَصِيرِ.
Daga Bara’u - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Ban taɓa ganin ma'abocin gashin kai ba mafi kyau a cikin kayan ado jajaye (mayafi da kwarjalle saƙar Yaman) kamar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ba - gashinsa yana taɓa kafaɗunsa, mai nisan abinda ke tsakanin kafaɗu ne, shi ba dogo ba ne ba kuma gajere ba ne.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Bara’u ɗan Azib - Allah Ya yarda da shi - yana bada labarin cewa shi bai taɓa ganin wani mai gashi ba, wanda gashin kansa mai tsawo ne ya kai kafaɗu, kuma yana sanya mayafi da kwarjalle baƙaƙe alhali a cikinsa akwai zanen ja mafi kyau kamar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ba -, ya kasance daga cikin siffofinsa na halitta shi mai nisan abinda ke tsakanin kafaɗu ne, mai yalwar ƙirji, kuma ya kasance mai tsakatsakiyar daidaituwa tsakanin tsawo da gajarta.
Fa’idoji
- Bayanin wasu daga cikin siffofin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - masu kyau a zahiri na kyawun gashi da faɗin ƙirji, da kyawun daidaituwa, da makamancin haka.
- Son sahabbai masu girma - Allah Ya yarda da su - ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, har cewa su suna hakaitowa kuma suna ruwaito ɗabi'unsa da siffofinsa na jiki da kuma na ma'ana ga na bayansu.
Madogara
صحيح البخاري (4/ 188) (3551).
صحيح مسلم (4/ 1818) (2337).
تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، لعبد الله البسام (ص730).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ عَائِشَةَ أُمِّ المُؤمنينَ رضي الله عنها قَالَتْ: كَانَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يُعْجِبُهُ التَّيَمُّنُ، فِي تَنَعُّلِهِ، وَتَرَجُّلِهِ، وَطُهُورِهِ، وَفِي شَأْنِهِ كُلِّهِ.
Daga Aisha Uwar Muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce : Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance damantawa tana kayatar da shi, a sanya takalminsa, da taje kansa, da tsarkinsa, kai da sha'aninsa duka.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana so kuma yana fifita cewa ya fara da dama a al'amuransa masu dacewa da girmamawa, daga cikin hakan: Ya fara da kafar dama a sanya takalminsa, kuma yana farawa da dama a taje gashin kansa da gemunsa a tajesu da shafa musu mai, a alwalarsa kuma yana gabatar da dama akan hagu daga hannaye da kafafuwa.
Fa’idoji
- Nawawi ya ce: Wannan ka'ida ce tabbatacciya a shari'a, ita ce: cewa abinda ya kasance daga babin giramamawa da daukaka, kamar sanya tufa da wanduna da huffi da shiga masallaci da asuwaki da sanya kwalli, da yanke farce, da rage gashin baki, da taje kai shi ne yi masa kum, da cire gashin hammata, da aske kai, da sallama daga sallah, da wanke gabban alwala, da fita daga bandaki, da ci da sha, da musafaha, da sumbatar (Alhajarul Aswad) bakin dutse, da wanin hakan na abinda yake a cikin ma'anarsa anso damantawa a cikinsa. Amma abinda ya kasance kishiyarsa kamar shiga bandaki, da fita daga masallaci da face majina, da tsarki, da tube tufafi da wanduna da huffi da abinda ke kama da hakan, to an so haguntawa a cikinsa, wannan saboda girmama dama da kuma daukakarta.
- "Damantawa yana kayatar da shi". Ya kunshi: Farawa a cikin ayyuka da hannun dama, da kafar dama, da bangaren dama, da bada abu da dama.
- Nawawi ya ce: Ka sani cewa daga gabban alwala a kwai wadanda ba’a son damantawa a cikinsu; shi ne kunnuwa da tafuka da kundukuki kai za'a tsarkakesu ne karo daya, idan hakan ya wuyata kamar a hakkin mai dungu da makamancinsa; sai a gabatar da dama.
Madogara
صحيح البخاري (1/ 45) (168).
صحيح مسلم (1/ 226) (268).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن أبي جُحَيْفَةَ وَهْبِ بْنِ عَبْدِ اللَّهِ السُّوَائِيِّ رضي الله عنه قال: «أَتَيتُ النَبِيَّ صلى الله عليه وسلم وهو في قُبَّةٍ لَهُ حَمرَاءَ مِن أَدَمٍ، قال: فَخَرَج بِلاَل بِوَضُوءٍ، فمن نَاضِحٍ ونَائِلٍ، قال: فَخَرَجَ النبِيَّ صلى الله عليه وسلم عليه حُلَّةٌ حَمرَاءُ، كَأَنِّي أَنظُرُ إلى بَيَاضِ سَاقَيهِ، قال: فَتَوَضَّأ وأَذَّن بِلاَل، قال: فَجَعَلَتُ أتَتَبَّعُ فَاهُ هَهُنَا وهَهُنَا، يقول يمِينا وشِمالا: حَيَّ على الصَّلاة؛ حيَّ عَلَى الفَلاَح. ثُمَّ رَكَزَت لَهُ عَنَزَةٌ، فَتَقَدَّمَ وصلى الظُهرَ رَكعَتَين، ثُمَّ لَم يَزلَ يُصِلِّي رَكعَتَين حَتَّى رَجَعَ إِلى المَدِينَة».
Daga Abu Juhaifa Wahb Dan Dan Abdullahi Al'suwa'i -Allah ya yarda da shi- "Najewa Annabi: -Amincin Allah su tabbata a gare shi- kuma shi yana sanye Malafa Ja ta fafa, sai Bilal ya fito masa da abin Alwala cikin su wasu na yayyafa ruwa wasu kuma suna shafaw" sai ya ce: sai Annabi ya fiuta da Riga Ja, kuma ni ina ganin farin Digadiginsa, sai ya ce, sai yayi Alwala kuma Bilal yayi kiran Sallah, sai ya ce, sai na rika bibiya bakinsa nan zuwa nan yana cewa hagu da dama: Ku taho izuwa Sallah; ku taho Izuwa Rabauta, sannan na kafa masa sanda, sai ya gabato sannan yayi Sallar Azahar Raka'a biyu, sannan bai gushe yanayin sallah ba Raka'a biyu har bayan nan har ya dawo Madina"
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi tsira da amincin Allah ya sauka a wani waje mai tudu kadan daga Makkah,sai Bilal ya fito ya yi alwala da sauran ruwan alwalar Annabi tsira da aminci su tabbata a gasre shi,sai mutane suka zo suna ta tabarruki da wannan ruwan alwala,sai Bilal ya yi kiran salla: sai Abu Juhaifa yace:sai na rika bibiyar bakin Bilal, yana jujjuya wa a dama da hargu yayin da ya zo"ku taso zuwa ga sallah,ku taso zuwa ga rabo: don mutane su ji,ko don su wadannan jumloli suna kwaditar da a zo sallah ne,sannan sai aka kafa wani dan gajeren mashi don ya zama sitirar sallarsa,sai ya sallaci azahar raka'a biyu,sannan bai gushe ba yana sallatar salla mai raka'a hudu bibbiyu har ya koma ko don kasancewarsa matafiyi
Madogara
الإلمام بشرح عمدة الأحكام لإسماعيل الأنصاري، ط1، دار الفكر، دمشق، 1381هـ.
تيسير العلام شرح عمدة الأحكام للبسام، حققه وعلق عليه وخرج أحاديثه وصنع فهارسه: محمد صبحي بن حسن حلاق، ط10، مكتبة الصحابة، الإمارات - مكتبة التابعين، القاهرة، 1426 هـ.
تنبيه الأفهام شرح عمدة لأحكام لابن عثيمين، ط1، مكتبة الصحابة، الإمارات، 1426هـ.
عمدة الأحكام من كلام خير الأنام صلى الله عليه وسلم لعبد الغني المقدسي، دراسة وتحقيق: محمود الأرناؤوط، مراجعة وتقديم: عبد القادر الأرناؤوط، ط2، دار الثقافة العربية، دمشق ، بيروت، مؤسسة قرطبة، 1408 هـ.
صحيح البخاري، تحقيق: محمد زهير بن ناصر الناصر، ط1، دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم: محمد فؤاد عبد الباقي)، 1422هـ.
صحيح مسلم، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي، دار إحياء التراث العربي، بيروت، 1423 هـ.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن جابرٍ رضي الله عنه : أَنَّ رسولَ اللهِ صلى الله عليه وسلم دَخَلَ يومَ فَتْحِ مَكَّةَ وعليه عِمَامَةٌ سَوْدَاءُ.
عن أبي سعيدٍ عمرو بنِ حُرَيْثٍ رضي الله عنه قال: كَأَنِّي أَنْظُرُ إلى رسولِ اللهِ صلى الله عليه وسلم وعليه عِمَامَةٌ سَوْدَاءُ، قَدْ أَرْخَى طَرَفَيْهَا بَيْنَ كَتِفَيْهِ.
في رواية: أَنَّ رسولَ اللهِ صلى الله عليه وسلم خَطَبَ النَّاسَ، وعليه عِمَامَةٌ سَوْدَاءُ.
Daga Jabir, yardar Allah ta tabbata a gare shi: - Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya shiga ranar da aka ci Makka da bakar rawani a kansa. Daga Abu Saeed Amr bin Harith - yardar Allah ta tabbata a gare shi - ya ce: Kamar dai ina kallon Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - tare da bakar rawani a kansa, wanda karshensa ya yi sassauci tsakanin kafadunsa. A wata ruwaya: Cewa Manzon Allah –SAW- ya yi wa mutane jawabi, kuma yana da bakar rawani a kansa.
Muslim ne ya rawaito shi duka Riwar ta sa biyunDarajaIngantacce ne
Madogara
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي، ط1، دار ابن الجوزي، الدمام، 1415ه.
تطريز رياض الصالحين، للشيخ فيصل المبارك، ط1، تحقيق: عبد العزيز بن عبد الله آل حمد، دار العاصمة، الرياض، 1423هـ.
دليل الفالحين لطرق رياض الصالحين، لمحمد علي بن محمد بن علان، ط4، اعتنى بها: خليل مأمون شيحا، دار المعرفة، بيروت، 1425ه.
رياض الصالحين للنووي، ط1، تحقيق: ماهر ياسين الفحل، دار ابن كثير، دمشق، بيروت، 1428هـ.
رياض الصالحين، ط4، تحقيق: عصام هادي، وزارة الأوقاف والشؤون الإسلامية القطرية، دار الريان، بيروت، 1428هـ.
صحيح مسلم، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي، دار إحياء التراث العربي، بيروت.
كنوز رياض الصالحين، مجموعة من الباحثين برئاسة حمد بن ناصر العمار، ط1، كنوز إشبيليا، الرياض، 1430هـ.
مرقاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح، للقاري، ط1، دار الفكر، بيروت، 1422هـ.
المعجم الوسيط، مجمع اللغة العربية بالقاهرة، ط2، دار إحياء التراث العربي، بيروت - لبنان.
المنهاج شرح صحيح مسلم بن الحجاج، للنووي، ط.2، دار إحياء التراث العربي – بيروت، 1392ه.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن أبي رمثة التيمي رضي الله عنه قال: رأيتُ رسولَ اللهِ صلى الله عليه وسلم وعليه ثَوْبَانِ أَخْضَرَانِ.
Daga Abu Ramtha al-Taymi - yardar Allah ta tabbata a gare shi - ya ce: Na ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - tare da koren tufafi biyu a kansa.
Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Al-Nasa'i Ya Rawaito shi - Abu Daud Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shi - Al-Darumi Ya Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Abu Ramtha, Allah ya yarda da shi, ya ruwaito cewa ya ga Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana sanye da koren tufafi.
Madogara
دليل الفالحين لطرق رياض الصالحين، لابن علان، نشر دار الكتاب العربي.
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، نشر: مؤسسة الرسالة، الطبعة الرابعة عشر، 1407ه - 1987م.
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين، نشر: دار الوطن للنشر، الرياض، الطبعة، 1426ه.
شرح صحيح البخارى، لابن بطال، تحقيق: أبو تميم ياسر بن إبراهيم، ط2، مكتبة الرشد، السعودية، الرياض، 1423هـ.
سنن الترمذي، محمد بن عيسى الترمذي، تحقيق وتعليق: أحمد محمد شاكر ومحمد فؤاد عبد الباقي وإبراهيم عطوة عوض، شركة مكتبة ومطبعة مصطفى البابي الحلبي - مصر، الطبعة الثانية، 1395هـ - 1975م.
مسند الإمام أحمد بن حنبل، المحقق: شعيب الأرنؤوط - عادل مرشد، وآخرون إشراف: د عبد الله بن عبد المحسن التركي، مؤسسة الرسالة، الطبعة الأولى، 1421هـ - 2001م.
سنن أبي داود، سليمان بن الأشعث، المحقق: محمد محيي الدين عبد الحميد، المكتبة العصرية، صيدا - بيروت.
السنن الكبرى، للنسائي، حققه وخرج أحاديثه: حسن عبد المنعم شلبي، أشرف عليه: شعيب الأرناءوط، مؤسسة الرسالة، بيروت، الطبعة الأولى، 1421هـ - 2001م.
مسند الدارمي، عبد الله بن عبد الرحمن بن الفضل الدارمي، التميمي، تحقيق: حسين سليم أسد الداراني - دار المغني للنشر والتوزيع، المملكة العربية السعودية الطبعة الأولى، 1412هـ - 2000م.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن أم سلمة رضي الله عنها قالت: كان أَحَبَّ الثِّيَابِ إلى رسولِ اللهِ صلى الله عليه وسلم القَمِيصُ.
A kan Ummu Salamah - yardar Allah ta tabbata a gare ta - ta ce: Mafi soyuwar tufafi ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - shi ne taguwa.
Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Abu Daud Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Tufafin da aka fi so ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - shi ne taguwa. Saboda ba a iya gani fiye da tufafi da alkyabbar, kuma saboda yanki daya ne da mutum zai sa sau daya, ya fi sauki fiye da sanya Ezar farko sannan kuma rigar ta biyu. Amma duk da hakan, idan kana cikin kasar da ta saba da sanya shudaye da riguna, kuma ka sanya irin su, to babu laifi a muhimmin abu kar ka sabawa tufafin mutanen kasarka har ka fada cikin shahara, kuma Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya hana sanya shahara.
Madogara
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، نشر: مؤسسة الرسالة، الطبعة: الرابعة عشر، 1407ه 1987م.
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين، نشر: دار الوطن للنشر، الرياض، الطبعة: 1426ه.
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، للهلالي، نشر: دار ابن الجوزي.ط1، دار ابن الجوزي، الدمام، 1415ه.
سنن الترمذي، نشر: شركة مكتبة ومطبعة مصطفى البابي الحلبي – مصر، الطبعة: الثانية، 1395هـ - 1975م.
سنن أبي داود، تحقيق: محمد محيي الدين عبد الحميد، نشر: المكتبة العصرية، صيدا – بيروت.
مسند الإمام أحمد بن حنبل، تحقيق: شعيب الأرنؤوط - عادل مرشد، وآخرون، نشر: مؤسسة الرسالة، الطبعة: الأولى، 1421هـ - 2001م.
مختصر الشمائل المحمدية، للألباني، نشر: المكتبة الإسلامية – عمان – الأردن.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comKowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com