عن أنس بن مالك رضي الله عنه قال: كَانَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَحْسَنَ النَّاسِ خُلُقًا.
Daga Anas Dan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance ya fi kowa kyawawan ɗabi’u.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance ya fi kowa cikar kyawawan ɗabi’u, yana da wannan rigayar a dukkanin kyawawan ɗabi’u, kamar kyakkyawar magana, bayar da kyauta, sakin fuska, rashin cutarwa, juriyarsa ga mutane.
Fa’idoji
- Cikar ɗabi’un Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.
- Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, shi ne babban abin koyi a kyawawan ɗabi’u.
- Kwaɗaitarwa a kan koyi da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a kyawawan ɗabi’u.
Madogara
صحيح البخاري (8/ 45) (6203).
صحيح مسلم (4/ 1805) (2310).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 670).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمصطفى الخِن وغيره (1/ 524).
كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (9/ 57).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (3/ 556).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comقال سعد بن هشام بن عامر -عندما دخل على عائشة رضي الله عنها-: يَا أُمَّ الْمُؤْمِنِينَ، أَنْبِئِينِي عَنْ خُلُقِ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، قَالَتْ: أَلَسْتَ تَقْرَأُ الْقُرْآنَ؟ قُلْتُ: بَلَى، قَالَتْ: فَإِنَّ خُلُقَ نَبِيِّ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَانَ الْقُرْآنَ.
Sa’ad Ɗan Hisham Ɗan Amir ya ce: A Lokacin da ya zo wurin Nana Aisha Allah Ya yarda da ita: Ya uwar Muminai! Ki ba ni bayani kan ɗabi’un Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, sai ta ce: A she ba ka kasance kana karanta Alƙur’ani ba ?? Na ce: Ina karantawa, ta ce: To, ɗabi’un Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi sun kasance Alƙur’ani ne.
Muslim ne ya rawaito shi a cikin wani dogon hadisiDarajaIngantacce ne
Sharhi
An tambayi Uwar Muminai A'isha Allah Ya yarda da ita, a kan ɗabi’un Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi sai ta amsa, da jawabi gamamme, ta kuma mayar da mai tambayar zuwa Alƙur’ani mai girma wanda ya ƙunshi dukkanin siffofi na kamala, sai ta ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana ɗabia’antuwa ne da ɗabi’u na Alƙur’ani, abin da Alƙur’ani ya yi umarni ya yi, kuma abin da Alƙur’ani ya hana ya nisance shi, sai ɗabi’unsa suka kasance aiki da shi da tsayawa inda ya iyakance, da ladabtuwa da ladubansa da ɗaukar izina da misalai da ƙissoshinsa.
Fa’idoji
- Kwaɗaitarwa a kan koyi da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a ɗabi’antuwarsa da ɗabi’un Alƙur’ani.
- Yabon kyawawan ɗabi’un Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, kuma sun kasance daga alkukin [hasken] Wahayi suke.
- Alƙur’ani ne tushen dukkanin kyawawan ɗabi’u.
- Ɗabi’u a Musulunci sun ƙunshi addini dukkansa, ta hanyar aikata umarni da kuma barin hani.
Madogara
صحيح مسلم (1/ 512) (746).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (3/ 308).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (6/ 660).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمصطفى الخن وغيره (2/ 1253).
كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (21/ 556).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «اللهُمَّ إِنَّمَا أَنَا بَشَرٌ، فَأَيُّمَا رَجُلٍ مِنَ المُسْلِمِينَ سَبَبْتُهُ أَوْ لَعَنْتُهُ أَوْ جَلَدْتُهُ فَاجْعَلْهَا لَهُ زَكَاةً وَرَحْمَةً».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Ya Allah ! Kaɗai ni mutum ne, duk mutum daga cikin musulmai da na zage shi ko na tsine masa ko na dake shi to Ka sanya hakan ya zama tsarki da rahama gare shi».
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbat agare shi - ya yi addu'a sai ya ce: Ya Allah ? Kaɗai ni mutum ne, ina yin fushi kamar yadda ɗan Adam yake yin fushi, duk muminin da na cutar da shi ko na zage shi na aibanta shi, ko na tsine masa na yi masa mummunar addu'a da korewa daga rahamarKa, ko na dake shi da bulala, to ka sanya hakan ya zama tsarkaka da kusanci da tsarkakewa da kaffara da kuma rahamar da zaka yi masa rahama da ita.
Fa’idoji
- Girman ɗabi'un Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
- Ibnu Hajar ya ce: A cikin Hadisin akwai cikar tausayinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga al'ummarsa da kuma kyawawan ɗabi'unsa da karamcin zatinsa, inda ya fuskanci abin da ya afku daga gare shi da gyarawa da kuma girmamawa.
- Nawawi ya ce: Idan an ce: Ta yaya zai yi mummunar addu'a akan wanda bai cancanci mummunar addu'a ba ? ko ya zage shi ko ya tsine masa da makamancin hakan? Amsa ita ce abin da malamai suka amsa da shi, a taƙaice ta fuska biyu: Na farkonsu: Abin da ake nufi da wanda bai cancanci hakan ba a wurin Allah - Maɗaukakin sarki -, haka a cikin baɗinin al'amari, sai dai cewa shi a zahiri ya cancanci hakan, sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya bayyanar da cancantarsa ga hakan da alamu na shari'a, kuma ya zama a baɗini al'amari bai cancanci hakan ba, kuma shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - abin umarta ne da yin hukunci a zahiri, Allah ne Yake jiɓintar sirrika. Na biyu: Cewa abin da ya faru na zaginsa da mummunar addu'arsa da makancinsa to ba abin nufi ba ne, kai shi yana daga abin da al'adar larabawa ta gudana da shi a cikin sadar da zancensu ba tare da niyya ba. Kamar faɗinsa: Damanka ya talauta, da ciwo ya sameka a fata da maƙogwaro, a cikin wannan hadisn: (Kada shekarunka su yi yawa), a cikin hadisin Mu'awiya: Kada Allah Ya ƙosar da cikinka, da makamancin haka, basa nufin wani abu daga haƙiƙanin addu'a, sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ji tsoron kada amsa addu'ar ta dace da wani abu daga hakan, sai ya roƙi Ubangijinsa - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka - ya kwaɗaitar da ya sanya hakan ya zama rahama da kaffara da kusanci da tsarkakkewa da kuma lada, kaɗai hakan yana bayyana ne daga gare shi a lokaci kaɗan daga cikin zamaninsa, Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai kasance mai alfasha ba, haka ba ya ɗorawa kansa yawan yin alfasha, kuma ba mai yawan tsinuwa ba ne, ba kuma mai ɗaukar fansa ne da kansa ba.
Madogara
صحيح البخاري (8/ 77) (6361).
صحيح مسلم (4/ 2007) (2601).
عمدة القاري شرح صحيح البخاري (22/ 310).
إرشاد الساري لشرح صحيح البخاري (9/ 207).
Wannan hadisi a HadeethEnc.com