Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

To, ɗabi’un Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi sun kasance Alƙur’ani ne

قال سعد بن هشام بن عامر -عندما دخل على عائشة رضي الله عنها-: يَا أُمَّ الْمُؤْمِنِينَ، أَنْبِئِينِي عَنْ خُلُقِ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، قَالَتْ: أَلَسْتَ تَقْرَأُ الْقُرْآنَ؟ قُلْتُ: بَلَى، قَالَتْ: فَإِنَّ خُلُقَ نَبِيِّ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَانَ الْقُرْآنَ.
Sa’ad Ɗan Hisham Ɗan Amir ya ce: A Lokacin da ya zo wurin Nana Aisha Allah Ya yarda da ita: Ya uwar Muminai! Ki ba ni bayani kan ɗabi’un Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, sai ta ce: A she ba ka kasance kana karanta Alƙur’ani ba ?? Na ce: Ina karantawa, ta ce: To, ɗabi’un Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi sun kasance Alƙur’ani ne.
Muslim ne ya rawaito shi a cikin wani dogon hadisiDarajaIngantacce ne
Sharhi

An tambayi Uwar Muminai A'isha Allah Ya yarda da ita, a kan ɗabi’un Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi sai ta amsa, da jawabi gamamme, ta kuma mayar da mai tambayar zuwa Alƙur’ani mai girma wanda ya ƙunshi dukkanin siffofi na kamala, sai ta ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana ɗabia’antuwa ne da ɗabi’u na Alƙur’ani, abin da Alƙur’ani ya yi umarni ya yi, kuma abin da Alƙur’ani ya hana ya nisance shi, sai ɗabi’unsa suka kasance aiki da shi da tsayawa inda ya iyakance, da ladabtuwa da ladubansa da ɗaukar izina da misalai da ƙissoshinsa.

Fa’idoji
  1. Kwaɗaitarwa a kan koyi da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a ɗabi’antuwarsa da ɗabi’un Alƙur’ani.
  2. Yabon kyawawan ɗabi’un Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, kuma sun kasance daga alkukin [hasken] Wahayi suke.
  3. Alƙur’ani ne tushen dukkanin kyawawan ɗabi’u.
  4. Ɗabi’u a Musulunci sun ƙunshi addini dukkansa, ta hanyar aikata umarni da kuma barin hani.
Madogara

صحيح مسلم (1/ 512) (746). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (3/ 308). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (6/ 660). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمصطفى الخن وغيره (2/ 1253). كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (21/ 556).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
SIFFOFINSA NA HALITTA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com