Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

JINƘANSA TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARESHI

Hadisai 11

Shin bana ba ku labari ba game da Jujal, wanda babu wani annabi da ya zantar da mutanensa shi ? lallai shi mai ido ɗaya ne, kuma shi zai zo a tare da shi akwai kwatankwacin aljanna da wuta,

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «أَلاَ أُحَدِّثُكُمْ حَدِيثًا عَنِ الدَّجَّالِ، مَا حَدَّثَ بِهِ نَبِيٌّ قَوْمَهُ؟ إِنَّهُ أَعْوَرُ، وَإِنَّهُ يَجِيءُ مَعَهُ بِمِثَالِ الجَنَّةِ وَالنَّارِ، فَالَّتِي يَقُولُ إِنَّهَا الجَنَّةُ هِيَ النَّارُ، وَإِنِّي أُنْذِرُكُمْ كَمَا أَنْذَرَ بِهِ نُوحٌ قَوْمَهُ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Shin bana ba ku labari ba game da Jujal, wanda babu wani annabi da ya zantar da mutanensa shi ? lallai shi mai ido ɗaya ne, kuma shi zai zo a tare da shi akwai kwatankwacin aljanna da wuta, wacce zai ce ita ce aljanna to ita ce wuta, lallai ni ina gargaɗarku kamar yadda (Annabi) Nuhu ya gargaɗi al'ummarsa da shi".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana ba wa sahabbansa labari game da Dajjal da siffofinsa da almominsa da abinda wani annabi a gabaninsa bai zantar da shi ba, daga hakan: Cewa shi mai ido ɗaya ne. Kuma Allah - Maɗaukakin sarki - Ya sanya masa kwatankwacin aljanna da wuta, gwargwdan ganin ido. Sai dai aljannarsa wuta ce, kuma wutarsa aljanna ce, wanda ya bi shi zai shigar da shi wannan aljannar a abinda mutane suke gani, sai dai cewa ita wuta ce mai ƙuna, wanda ya saɓa masa zai shigar da shi wutar a abinda mutane suke ganinsa, sai dai ita aljanna ce mai daɗi. Sannan annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi gargaɗi daga fitinarsa kamar yadda (Annabi) Nuhu ya gargaɗar da mutanensa shi.

Fa’idoji
  1. Girman fitinar Dujal.
  2. Tsira daga fitinar Dajjal tana kasancewa ne da gaskiyar imani da fakewa zuwa ga Allah - Maɗaukakin sarki - da neman tsari da Allah daga gare shi a tahiyar ƙarshe, da haddace ayoyi goma daga farkon surar Kahfi.
  3. Tsananin kwaɗayin annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga al'ummarsa, lokacin da ya bayyanawa musulmai siffofin Jujal abinda wani annabi kafin shi bai bayyana shi ba.
Madogara

صحيح البخاري (4/ 134) (3338). صحيح مسلم (4/ 2250) (2936).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Lallai cewa Annabi ya kasance yana Sallah kuma ya na dauke da Umama Yar Zainab Yar Annabi

عن أبي قَتَادَةَ الأَنْصَارِيِّ رضي الله عنه قال: «أن رسول الله صلى الله عليه وسلم كان يُصَلِّي وهو حامل أُمَامَةَ بنت زينب بنت رسول الله صلى الله عليه وسلم ». ولأبي العاص بن الربيع بن عبد شَمْسٍ رضي الله عنه : «فإذا سجد وضعها، وإذا قام حملها».
Daga Katada Al'ansary ya ce: "allai cewa Annabi ya kasance yana Sallah kuma ya na dauke da Umama Yar Zainab Yar Annabi"
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi ya kasance yana Daukar Yar Diyarsa kuma ita Umama Diyar Zainab kuma a halin yana cikin Sallah, yadda yake sanya ta a kafarsa idan ta tsaya, to idan yai ruku'i ko yayi sujada sai ya ajiye ta a kasa don son da yake mata da kuma tausayawa

Madogara

تيسير العلام للبسام الناشر: مكتبة الصحابة، الأمارات - مكتبة التابعين، القاهرة الطبعة- العاشرة، 1426 هـ - 2006 م . تنبيه الأفهام للعثيمين -طبعة مكتبة الصحابة الامارات - مكتبة التابعين- القاهرة- الطبعة الأولى 1426. صحيح البخاري -أبو عبد الله محمد بن إسماعيل بن إبراهيم بن المغيرة الجعفي البخاري، تحقيق محمد زهير بن ناصر الناصر - الناشر : دار طوق النجاة -الطبعة : الأولى 1422هـ. صحيح مسلم المحقق: محمد فؤاد عبد الباقي - الناشر: دار إحياء التراث العربي – بيروت. تأسيس الأحكام -أحمد بن يحيى النجمي- دار المنهاج- القاهرة- مصر -الطبعة الأولى.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Lallai cewa Allah Maigirma da Daukaka ya nade mun kasa, sai da nagano daga bangon gabas zuwa bangon yamma , ku ma cewa lallai Al'umma ta Mulkinta zai kai inda aka nunamun, kuma anbani Taskoki biyu Ja da fara.

عن ثوبان رضي الله عنه أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: "إن الله زَوَى لي الأرض، فرأيت مشارقها ومغاربها، وإن أمتي سيبلغ ملكُها ما زُوِيَ لي منها. وأعطيت الكنْزين الأحمر والأبيض. وإني سألت ربي لأمتي أن لا يهلكها بسَنَةٍ بعامةٍ، وأن لا يُسَلِّطَ عليهم عدوا من سوى أنفسهم فيَسْتَبِيحَ بَيْضَتَهُمْ؛ وإن ربي قال: يا محمد، إذا قضيتُ قضاءً فإنه لا يُرَدُّ، وإني أعطيتك لأمتك أن لا أهلكهم بسنة عامة، وأن لا أُسَلِّطَ عليهم عدوا من سوى أنفسهم فيَسْتَبِيحَ بَيْضَتَهُمْ ولو اجتمع عليهم مَنْ بأقطارها، حتى يكون بعضُهم يُهْلِكُ بعضًا ويَسْبِي بعضُهم بعضًا". ورواه البرقاني في صحيحه، وزاد: "وإنما أخاف على أمتي الأئمةَ المضلين، وإذا وقع عليهم السيف لم يرفع إلى يوم القيامة. ولا تقوم الساعة حتى يلحق حي من أمتي بالمشركين، وحتى تعبد فِئامٌ من أمتي الأوثان. وإنه سيكون في أمتي كذابون ثلاثون؛ كلهم يزعم أنه نبي، وأنا خاتم النبيين لا نبي بعدي. ولا تزال طائفة من أمتي على الحق منصورة لا يضرهم من خذلهم حتى يأتي أمر الله تبارك وتعالى".
Daga Thauba -Allah ya yarda da shi- cewa Annabi ya ce: "Lallai cewa Allah Maigirma da Daukaka ya nade mun kasa, sai da nagano daga bangon gabas zuwa bangon yamma \, ku ma cewa lallai Al'umma ta Mulkinta zai kai inda aka nunamun, kuma anbani Taskoki biyu Ja da fara, kuma ewa Al;umma ta Mulkinta zai kai duk inda aka nuna mun, kuma anbani Taskoki biyu Ja da kuma fara, kuma cewa ni na roki ubangijina kada ya halaka Al'ummata da Annoba, kuma kada ya Dora akanta Abokin gabar wanda ba daga cikinsu ba wanda zai hallaka su, kuma Ubangijina ya ce: Ya kai Muhammadu, idan na hukunta kaddara ta to babu mai maida ta, kuma cewa na masa cewa Al'ummarka bazan Halaka su da Annoba ba, kuma ba bazan dora musu Abokin gaba ba sai daga cikinsu wanda zai kuma ya hallakasu koda kuwa duk Mutanen Duniya zasu taru don ganin bayansu, ta yadda wasu zasu rika kashe wasu kuma
Ibnu Majah ne ya Rawaito shi - Abu Daud Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shi - Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Wannan Hadisi ya kunshi abubuwa kamar haka masu ggirma wadanda suka kunshi Al'amura muhimmai da kuma labarai na gaskiya, kuma wanda Maigaskiya abin gasgatawa ya bada labari, cewa Allah mai girma da daukaka ta tattare masa kasa har saida ya gano abinda Al'umma rsa zata Mallaka tun daga Bangon Duniya na gabas zuwa na yamma, kuma ya bada labari cewa Allah ya bashi Taskoki guda biyu, kuma hakan ya wakana kamar yadda ya bada labarin, kuma ya ce Al'ummarsa zata Mallake Mulkin Kisa da kuma Kaisar da duk abinda suke da shi na zinari da Azurfa da kayan kawa, kuma ya bada labarin cewa ya roki Ubangijinsa kada ya hallaka Al'ummarsa da da fari, ko kuma ya dora Mata abokin gaba daga cikin kafirai wanda zai wanda zai Mamaye garuruwansu kuma ya karar da Jama'arsu, kuma Allah ya amsa masa na farko, kuma ya amsa masa na biyun ma matukar Al'ummarsa ta nisanci sabani da kuma rarrabuwa, da kuma gaba a n tsakaninta, kuma Annabi ya jiyewa Al'ummarsa tsoron Hadarin Batattun Shugabanni da kuma Malamai; domin Mutane da su suke koyi cikin batansu, kuma ya bada labari cewa Fitina zata afku da kuma Yaki to cewa hakan zai ci gaba har zuwa tashin Alkiyamakuma hakika hakan ya faru kamar yadda, to tunda fitinar ta faru kuma ita ce take ci gaba har yanzu, kuma ya bada labarin cewa wasu daga cikin Al'ummarsa zasu koma cikin kafirai can garuruwansu da Addininsu, kuma cewa wasu Jama'u daga cikin Al''umma zasu koma shirka kuma hakan ya faru kamar yadda ya bada labari, don an bautawa Kaburbura da Bishiyoyi da Duwatsu duk da faruwar wadan nan Masifi da hadura, kuma wannan Jama'a ta gaskiya duk da karancintabata cutu da kaidin Abokan gabarta ba da kuma wadanda suka saba mata.

Madogara

الملخص في شرح كتاب التوحيد، دار العاصمة الرياض، الطبعة: الأولى 1422هـ- 2001م. الجديد في شرح كتاب التوحيد، مكتبة السوادي، جدة، المملكة العربية السعودية، الطبعة: الخامسة، 1424هـ/2003م. صحيح مسلم، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي، نشر: دار إحياء التراث العربي – بيروت.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Lallai cewa mafi tsoron abinda nake jiye muku tsoro karamar shirka" suka ce : Mece ce karamar shirka ya Manzon Allah? ya ce: "Riya

عَنْ مَحْمُودِ بْنِ لَبِيدٍ رضي الله عنه أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «إِنَّ أَخْوَفَ مَا أَخَافُ عَلَيْكُمُ الشِّرْكُ الْأَصْغَرُ» قَالُوا: وَمَا الشِّرْكُ الْأَصْغَرُ يَا رَسُولَ اللهِ؟ قَالَ: «الرِّيَاءُ، يَقُولُ اللهُ عز وجل لَهُمْ يَوْمَ الْقِيَامَةِ إِذَا جُزِيَ النَّاسُ بِأَعْمَالِهِمْ: اذْهَبُوا إِلَى الَّذِينَ كُنْتُمْ تُرَاؤُونَ فِي الدُّنْيَا، فَانْظُرُوا هَلْ تَجِدُونَ عِنْدَهُمْ جَزَاءً؟».
Daga Mahmud Dan Labid - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Lallai cewa mafi tsoron abinda nake jiye muku tsoro karamar shirka" suka ce : Mece ce karamar shirka ya Manzon Allah? ya ce: "Riya, Allah - Mai girma da daukaka - Zai ce da su a ranar Alkiyama idan za’a yi wa mutane sakayyar ayyukansu: Ku tafi zuwa ga wadanda kuka kasance kuna nuna musu ayyukanku a duniya, sai ku duba shin zaku samu wani sakamako a wurin su?".
Ahmad ne ya rawaito shiDarajaHasan ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa mafi yawan abinda yake jin tsoronsa ga al'ummarsa: Karamar shirka ita ce: Riya; Ita ce ya yi aiki saboda mutane. Sannan ya bada labari game da ukubar masu riya a ranar Alkiyama za’a ce da su: Ku tafi zuwa ga wadanda kuka kasance kuna aiki saboda su, ku duba shin suna mallakar saka muku da baku lada akan wannan aikin?!

Fa’idoji
  1. Wajabcin tsarkake aiki saboda Allah - Mai girma da daukaka - da gargadarwa daga riya.
  2. Tsananin tausayinsa tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga al'ummarsa, da kwadayinsa akan shiriyarsu da kuma nasiharsa garesu.
  3. Idan wannan ya zama shi ne tsoronsa tsira da amincin Allah su tabbata agare shi alhali shi yana yiwa sahabbansa magana kuma su ne shugabannin salihai to tsoro akan wanda ke bayansu ya fi tsanani.
Madogara

مسند أحمد (39/ 39) (23630). الجديد في شرح كتاب التوحيد، لمحمد القرعاوي (ص57). الملخص في شرح كتاب التوحيد، لصالح الفوزان (ص45).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Ananbi tsira da amincin Allah ya yi dare bai fito sallar Issha'i ba, sai Umar ya fito yace: salla ya Manzon Allah mata da yara sun yi bacci, sai Manzo ya fito kansa yana digar da ruwa yana cewa: ba don kar in takurawa al'ummata ba, da na umarce su da yin wannan sallar a irin wannan lokacin.

عن عَبْد اللَّهِ بْنِ عَبَّاسٍ رضي الله عنهما قال: «أّعْتَمَ النَبِيُّ -صلَّى الله عليه وسلَّم- بِالعِشَاء، فَخَرَج عُمَر فقال: الصَّلاةَ يا رسول الله، رَقَد النِسَاءُ والصِّبيَان. فَخَرَجَ ورَأسُهُ يَقطُر يقول: لَولاَ أن أَشُقَّ عَلَى أُمَّتِي -أو على النَّاس- لَأَمَرتُهُم بهذه الصَّلاة هذه السَّاعَة».
Daga Abdullahi Dan Abbas -Allah ya yarda da su- zuwa ga Annabi: "Annabi tsira da amincin Allah ya yi dare bai fito sallar Issha'i ba,siai Umar ya fito yace: salla ya Manzon Allah mata da yara sun yi bacci,sai Manzo ya fito kansa yana digar da ruwa yana cewa: ba don kar in takurawa al'ummata ba, da na umarce su da yin wannan sallar a irin wannan lokaci
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi ya jinkirta fitowa zuwa ga sallar issha'i har dare yayi ,mata da yara sun kwanta bacci,wanda basu da jumurin jira mai tsawo,sai Umar Dan Khaddab ya zo wajensa yace: sallah,mata da yara sun yi bacci. sai Manzo tsira da aminci ya fito daga gidansa zuwa masallaci kansa yana digar da ruwan wanka yana bayyana cewa mafi kyawun liokacin sallar issha'i shine a jinkirta ta.ba don gudun wahalar jiran lokacin ba:ba don kan in matsawa al'umma ta ba da na umarce su da wannan sallar a irin wannan lokacin

Madogara

الإلمام بشرح عمدة الأحكام لإسماعيل الأنصاري، ط1، دار الفكر، دمشق، 1381هـ تيسير العلام شرح عمدة الأحكام للبسام، حققه وعلق عليه وخرج أحاديثه وصنع فهارسه: محمد صبحي بن حسن حلاق، ط10، مكتبة الصحابة، الإمارات - مكتبة التابعين، القاهرة، 1426 هـ تنبيه الأفهام شرح عمدة لأحكام لابن عثيمين، ط1، مكتبة الصحابة، الإمارات، 1426هـ عمدة الأحكام من كلام خير الأنام صلى الله عليه وسلم لعبد الغني المقدسي، دراسة وتحقيق: محمود الأرناؤوط، مراجعة وتقديم: عبد القادر الأرناؤوط، ط2، دار الثقافة العربية، دمشق ، بيروت، مؤسسة قرطبة، 1408 هـ صحيح البخاري، تحقيق: محمد زهير بن ناصر الناصر، ط1، دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم: محمد فؤاد عبد الباقي)، 1422هـ. صحيح مسلم، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي، دار إحياء التراث العربي، بيروت، 1423 هـ.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Idan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - zai bar aiki, kuma zai so yin aiki da shi; Tsoron mutane su yi aiki da shi, to, za a ɗora musu.

عن أم المؤمنين عائشة رضي الله عنها قالت: إِنْ كَانَ رسولُ اللهِ صلى الله عليه وسلم لَيَدَعُ العَمَلَ، وهو يُحِبُّ أَنْ يَعْمَلَ بِهِ؛ خَشْيَةَ أَنْ يَعْمَلَ بِهِ النَّاسُ فَيُفْرَضَ عَلَيْهِمْ.
A kan Uwar Muminai, A’isha, Allah Ya yarda da ita, wacce ta ce: Idan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - zai bar aiki, kuma zai so yin aiki da shi; Tsoron mutane su yi aiki da shi, to, za a ɗora musu.
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi -SAW- ya kasance yana barin aiki alhali yana son aikata shi, don kada mutane su yi aiki a kansa, ta yadda zai zama dalilin dora su a kansu, don haka ya haifar musu da wahalhalu da yawa kuma shi - tsira da aminci su tabbata a gare shi - ya tsani sanya musu kunci.

Madogara

نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، نشر: مؤسسة الرسالة، الطبعة: الرابعة عشر، 1407هـ - 1987م. شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين، نشر: دار الوطن للنشر، الرياض، الطبعة: 1426هـ. بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، للهلالي، نشر: دار ابن الجوزي -الطبعة الأولى 1418هـ. صحيح البخاري، نشر: دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم ترقيم محمد فؤاد عبد الباقي)، الطبعة: الأولى، 1422هـ. صحيح مسلم، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي، نشر: دار إحياء التراث العربي، بيروت.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Ba na zuwa sallah, kuma ina so in tsawaita, saboda haka na ji yaron yana kuka, don haka sai na wuce cikin addu'ata na ƙi jinin mahaifiyarsa

عن أبي قتادة وأنس بن مالك رضي الله عنهما مرفوعاً: «إني لأقوم إلى الصلاة، وأريد أن أُطَوِّلَ فيها، فأسمع بكاء الصبي فأَتَجَوَّزُ في صلاتي كراهيةَ أن أَشُقَّ على أمه».
Daga Abu Qatada da Anas bin Malik - Allah ya yarda da su - a cikin marfoo: "Na tashi zuwa ga salla, kuma ina so in tsawaita, don haka sai na ji yaron yana kuka, don haka na sanya shi ya halatta a cikin addu'ata in ki son mai tsananin uwarsa".
Buhari ne ya rawaito shi - Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Cewa Annabi -SAW- ya shiga cikin salla a cikin jam’i a matsayin limami kuma yana son tsawaita shi, don haka idan ya ji kukan yaron, sai ya saukake masa saboda tsoron kar tsawaitawa ya yi wa mahaifiyarsa wahala. Domin zuciyarta tana shagaltuwa da ɗanta.

Madogara

دليل الفالحين لطرق رياض الصالحين، لابن علان، نشر دار الكتاب العربي. نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، نشر: مؤسسة الرسالة، الطبعة الرابعة عشر، 1407ه - 1987م. شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين، نشر: دار الوطن للنشر، الرياض، الطبعة: 1426ه. بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، للهلالي، نشر: دار ابن الجوزي.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Kwatankwacinku da kwatankwacinku kamar na mutumin da ya kunna wuta ne, sai ya sa ciyawa da shimfiɗar ciki suka fado a ciki, yayin da yake ƙona su daga gare ku, ni kuwa na karɓi namanku daga gare ku.

عن جابر بن عبد الله وأبو هريرة رضي الله عنهم مرفوعاً: «مثلي ومثلُكم كمثل رجلٍ أَوْقَدَ نارًا فجعل الجنادِبُ والفَرَاشُ يَقَعْنَ فيها، وهو يَذُبُّهُنَّ عنها، وأنا آخذٌ بحُجَزِكُم عن النار، وأنتم تَفَلَّتُون من يَدَيَّ».
Daga Jabir bin Abdullah da Abu Huraira - Allah ya yarda da su - a cikin isnadi: “Misãna da misãlinku kamar misãlin mutum ne wanda ya hura wuta, kuma ya sanya ciyawa da shimfiɗar shimfiɗa a ciki, alhãli kuwa yanã nisantar da su daga gare ta, alhãli kuwa ina ɗauke ku daga wutã,” kuna tserewa.
Muslim ne ya rawaito shi - Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara

رياض الصالحين، للنووي، نشر: دار ابن كثير للطباعة والنشر والتوزيع، دمشق – بيروت، تحقيق: ماهر ياسين الفحل، الطبعة: الأولى، 1428هـ - 2007م. دليل الفالحين لطرق رياض الصالحين، لابن علان، نشر دار الكتاب العربي. نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، نشر: مؤسسة الرسالة، الطبعة: الرابعة عشر، 1407ه 1987م. شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين، نشر: دار الوطن للنشر، الرياض، الطبعة: 1426ه. كنوز رياض الصالحين، نشر: دار كنوز إشبيليا، الطبعة: الأولى، 1430ه 2009م. بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، للهلالي، نشر: دار ابن الجوزي. صحيح البخاري، نشر: دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم ترقيم محمد فؤاد عبد الباقي)، الطبعة: الأولى، 1422ه. صحيح مسلم، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي، نشر: دار إحياء التراث العربي – بيروت.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
8 cikin 11
Hadisai 11
  1. Shin bana ba ku labari ba game da Jujal, wanda babu wani annabi da ya zantar da mutanensa shi ? lallai shi mai ido ɗaya ne, kuma shi zai zo a tare da shi akwai kwatankwacin aljanna da wuta,
  2. Lallai cewa Annabi ya kasance yana Sallah kuma ya na dauke da Umama Yar Zainab Yar Annabi
  3. Lallai cewa Allah Maigirma da Daukaka ya nade mun kasa, sai da nagano daga bangon gabas zuwa bangon yamma , ku ma cewa lallai Al'umma ta Mulkinta zai kai inda aka nunamun, kuma anbani Taskoki biyu Ja da fara.
  4. Lallai cewa mafi tsoron abinda nake jiye muku tsoro karamar shirka" suka ce : Mece ce karamar shirka ya Manzon Allah? ya ce: "Riya
  5. Ananbi tsira da amincin Allah ya yi dare bai fito sallar Issha'i ba, sai Umar ya fito yace: salla ya Manzon Allah mata da yara sun yi bacci, sai Manzo ya fito kansa yana digar da ruwa yana cewa: ba don kar in takurawa al'ummata ba, da na umarce su da yin wannan sallar a irin wannan lokacin.
  6. Idan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - zai bar aiki, kuma zai so yin aiki da shi; Tsoron mutane su yi aiki da shi, to, za a ɗora musu.
  7. Ba na zuwa sallah, kuma ina so in tsawaita, saboda haka na ji yaron yana kuka, don haka sai na wuce cikin addu'ata na ƙi jinin mahaifiyarsa
  8. Kwatankwacinku da kwatankwacinku kamar na mutumin da ya kunna wuta ne, sai ya sa ciyawa da shimfiɗar ciki suka fado a ciki, yayin da yake ƙona su daga gare ku, ni kuwa na karɓi namanku daga gare ku.
  9. Wanda ba ya jin kai ba ba za'a ji kansa ba
  10. Ya Jibrilu, je wurin Muhammad ka ce: Za mu faranta maka a cikin alummarka ba matan ka ba
  11. Manzon Allah SAW ya shafi Hannunsa a fuskarsa kuma yayi mun Addu'a , sai ya rayu shekara xari da Ashirin kuma babu komai a kansa sai 'Yan gasuka kaxan farare

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com