Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Manzon Allah SAW ya shafi Hannunsa a fuskarsa kuma yayi mun Addu'a , sai ya rayu shekara xari da Ashirin kuma babu komai a kansa sai 'Yan gasuka kaxan farare

عن أبي زيد بن أخْطَب رضي الله عنه قال: «مَسَح رسول الله صلى الله عليه وسلم يده على وجْهِي ودَعا لي» قال عَزْرَةُ: إنه عاش مائة وعشرين سنَة وليس في رأسه إلا شُعيْرات بِيض.
Daga Abu Zaid Bn Akhxab -Allah ya yarda da shi- ya ce: "Manzon Allah SAW ya shafi Hannunsa a fuskarsa kuma yayi mun Addu'a , sai ya rayu shekara xari da Ashirin kuma babu komai a kansa sai 'Yan gasuka kaxan farare"
Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Manzon Allah SAW ya shafa hannunsa akan fuskar Abu zaid Bn Akhxab Al-ansari -Allah ya yarda da shi- kuma yayi Masa Addua a wata riwayar kuma ta hadisin cewa shi yayi masa Addu'a da wannan Addu'ar "Allah ka ka Qawata shi, kuma ka tabbatar da Kyawunsa" ai ka sanya shi kyakkyawa Kuma ka Sanya Kyawunsa Dawwamamme tare da shi tsawo rayuwarsa, Azara xaya daga cikin waxanda suka rawaito Hadisin yana cewa: lallai Abu Zaid Al-ansari ya rayu shekara Xari da Ashirin kuma babu Furfura akansa sa yan silalan gashi farare, kuma a cikin wata riwayar: cewa shi ya kasance ne Mai sakin Fuska kuma bashi da Mokaxar fata ko kuma nannaxewa, kuma haka ya zauna har ya Mutu, kuma wannan duk saboda Al-barkar Addu'ar Manzon Allah SAW da kuma Shafar da yayi Masa a Fuskarsa.

Madogara

- سنن الترمذي، نشر: شركة مكتبة ومطبعة مصطفى البابي الحلبي – مصر، الطبعة: الثانية، 1395هـ - 1975م. - مسند الإمام أحمد بن حنبل، تحقيق: شعيب الأرنؤوط - عادل مرشد، وآخرون، نشر: مؤسسة الرسالة، الطبعة: الأولى، 1421هـ - 2001م. - صحيح وضعيف سنن الترمذي, محمد ناصر الدين الألباني، برنامج منظومة التحقيقات الحديثية، من إنتاج مركز نور الإسلام لأبحاث القرآن والسنة بالإسكندرية. - تحفة الأحوذي بشرح جامع الترمذي, أبو العلا محمد عبد الرحمن بن عبد الرحيم المباركفورى, دار الكتب العلمية – بيروت. - الفتح الرباني لترتيب مسند الإمام أحمد بن حنبل الشيباني ومعه بلوغ الأماني من أسرار الفتح الرباني, أحمد بن عبد الرحمن بن محمد البنا الساعاتي, دار إحياء التراث العربي, الطبعة: الثانية.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
JINƘANSA TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARESHI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com