Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

KUNYARSA TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARESHI

Hadisai 1

Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance mafi tsananin kunya daga budurwar dake cikin budircinta, idan ya ga wani abinda yake kinsa muna gane hakan a fuskarsa

عَنْ أَبِي سَعِيدٍ الخُدْرِيِّ رضي الله عنه قَالَ: كَانَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَشَدَّ حَيَاءً مِنَ العَذْرَاءِ فِي خِدْرِهَا، فَإِذَا رَأَى شَيْئًا يَكْرَهُهُ عَرَفْنَاهُ فِي وَجْهِهِ.
Daga Abu Sa'id al-Kudri - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance mafi tsananin kunya daga budurwar dake cikin budircinta, idan ya ga wani abinda yake kinsa muna gane hakan a fuskarsa.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Abu Sa'idul Khudr - Allah Ya yarda da shi - yana bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance mafi tsananin kunya daga yarinya budurwa wacce bata yi aure ba, ba ta yi mu'amala da maza ba wacce ke suturce a cikin gidanta, yana daga tsananin kunyarsa cewa shi idan ya ki wani abu fuskarsa tana canjawa kuma ba ya magana, kai sahabbansa suna fahimtar kinsa ga hakan a fuskarsa.

Fa’idoji
  1. Bayanin abinda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kunsa akansa na kunya, ita ce ɗabi'u masu girma.
  2. Kunyar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - muddin dai ba'a keta alfarmomin Allah, idan an keta su; to shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana fushi yana umartar sahabbansa kuma yana hanasu.
  3. Kwaɗaitarwa akan ɗabi'antuwa da kunya; domin ita tana sawa rai aiki mai kyau da barin mummuna.
Madogara

صحيح البخاري (8/ 26) (6102). صحيح مسلم (4/ 1809) (2320). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 11). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (4/ 32). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 562).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com