Abu Sa'idul Khudr - Allah Ya yarda da shi - yana bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance mafi tsananin kunya daga yarinya budurwa wacce bata yi aure ba, ba ta yi mu'amala da maza ba wacce ke suturce a cikin gidanta, yana daga tsananin kunyarsa cewa shi idan ya ki wani abu fuskarsa tana canjawa kuma ba ya magana, kai sahabbansa suna fahimtar kinsa ga hakan a fuskarsa.
- Bayanin abinda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kunsa akansa na kunya, ita ce ɗabi'u masu girma.
- Kunyar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - muddin dai ba'a keta alfarmomin Allah, idan an keta su; to shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana fushi yana umartar sahabbansa kuma yana hanasu.
- Kwaɗaitarwa akan ɗabi'antuwa da kunya; domin ita tana sawa rai aiki mai kyau da barin mummuna.
صحيح البخاري (8/ 26) (6102). صحيح مسلم (4/ 1809) (2320). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 11). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (4/ 32). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 562).