Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

JURIYARSA TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARESHI

Hadisai 2

"Ku rabu da shi ku zuba Bokitin Ruwa, ko Gugan Ruwa, Saboda an turo ku ne Masu saukakakawa ba'a turoku masu tsanantawa ba"

عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: بال أعرابي في المسجد، فقام الناس إليه لِيَقَعُوا فيه، فقال النبي صلى الله عليه وسلم : «دعوه وأريقوا على بوله سَجْلاً من ماء، أو ذَنُوبًا من ماء، فإنما بُعِثْتُمْ مُيَسِّرِينَ، ولم تُبْعَثُوا مُعَسِّرِينَ».
An rawaito daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- ya ce: wani Balaraben Kauye a Masallaci, sai Muatane sukai ca kansa don su taba shi, sai Annabi -Amincin Allah a gare shi- ya ce: "Ku rabu da shi ku zuba Bokitin Ruwa, ko Gugan Ruwa, Saboda an turo ku ne Masu saukakakawa ba'a turoku masu tsanantawa ba"
Bukhari da Muslim Suka Rawaito shi amma lafazin na Bukhari neDarajaIngantacce ne
Madogara

الجامع المسند الصحيح (صحيح البخاري), تأليف: محمد بن إسماعيل البخاري, تحقيق: محمد زهير بن ناصر الناصر, دار طوق النجاة ترقيم محمد فؤاد عبدالباقي, ط 1422. رياض الصالحين-النووي-تعليق وتحقيق: الدكتور ماهر ياسين الفحل الناشر: دار ابن كثير للطباعة والنشر والتوزيع، دمشق - بيروت-الطبعة: الأولى، 1428 هـ - 2007 م. بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين, تأليف: سليم بن عيد الهلالي, دار ابن الجوزي. إرشاد الساري لشرح صحيح البخاري, تأليف: أبو العباس أحمد بن محمد القسطلاني, الناشر: المطبعة الكبرى الأميرية, ط7 عام 1323.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Ba'a taɓa ba wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - zabi ba tsakanin abubuwa biyu face sai ya zaɓi mafi sauƙinsu, matuƙar bai kasance saɓo ba, idan ya kasance saɓo ne to ya kasance ya fi kowa nisantar shi

عَنْ عَائِشَةَ أُمِّ المُؤْمِنينَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهَا أَنَّهَا قَالَتْ: مَا خُيِّرَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ بَيْنَ أَمْرَيْنِ إِلَّا أَخَذَ أَيْسَرَهُمَا، مَا لَمْ يَكُنْ إِثْمًا، فَإِنْ كَانَ إِثْمًا كَانَ أَبْعَدَ النَّاسِ مِنْهُ، وَمَا انْتَقَمَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ لِنَفْسِهِ إِلَّا أَنْ تُنْتَهَكَ حُرْمَةُ اللَّهِ، فَيَنْتَقِمَ لِلَّهِ بِهَا.
Daga Nana Aisha Uwar Muminai - Allah Ya yarda da ita - cewa ita ta ce: Ba'a taɓa ba wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - zabi ba tsakanin abubuwa biyu face sai ya zaɓi mafi sauƙinsu, matuƙar bai kasance saɓo ba, idan ya kasance saɓo ne to ya kasance ya fi kowa nisantar shi, kuma Annabi bai bai taɓa ramuwar gayya ga kansa ba ko sau ɗaya, sai dai idan an keta hurumin Allah, sai ya yi hukunci saboda Allah da ita.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Uwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta bada labari game da wasu daga ɗabi'un Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, daga abinda ta ambata: Cewa shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ba'a taɓa ba shi zaɓi ba tsakanin al'amura biyu sai ya ɗauki mafi sauƙinsu muddin dai mafi sauƙin ba mai kaiwa zuwa zunubi ba ne, to cewa shi zai kasance mafi nisantar mutane ga wannan zunubin kuma zai zaɓi mafi tsanani a lokacin. Kuma (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi bai taɓa ramuwa ba ga kansa a keɓance ba, kai ya kasance yana kau da kai kuma yana afuwa daga haƙƙinsa sai dai idan keta alfarmomin Allah aka yi sai ya zama ya yi hukunci saboda Allah, kuma ya kasance mafi tsananin mutane a fushi saboda Allah.

Fa’idoji
  1. An so riƙo da sauƙi a cikin al'amura matuƙar dai babu saɓo a cikinsa.
  2. Sauƙin Musulunci.
  3. Halaccin fushi saboda Allah - Maɗaukakin sarki -.
  4. Abinda (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi yake akansa na juriya da haƙuri da tsayuwa da haƙƙi a cikin tsaida iyakokin Allah - Maɗaukakin sarki -.
  5. Ibnu Hajar ya ce: A cikinsa akwai barin riƙo da abu mai wahala, da wadatuwa da sassauƙa, da barin nacewa a cikin abinda ba'a buƙatuwa zuwa gare shi .
  6. Kwaɗaitarwa akan afuwa sai dai a cikin haƙƙoƙin Allah - Maɗaukakin sarki -.
Madogara

صحيح البخاري (4/ 189) (3560). صحيح مسلم (4/ 1813) (2327). فتح الباري لابن حجر (575/6). شرح صحيح مسلم (83/15). كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (601/9). شرح رياض الصالحين لابن عثيمين (587/3).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com