عَنِ ابْنِ عُمَرَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا قَالَ: حَفِظْتُ مِنَ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَشْرَ رَكَعَاتٍ: رَكْعَتَيْنِ قَبْلَ الظُّهْرِ، وَرَكْعَتَيْنِ بَعْدَهَا، وَرَكْعَتَيْنِ بَعْدَ المَغْرِبِ فِي بَيْتِهِ، وَرَكْعَتَيْنِ بَعْدَ العِشَاءِ فِي بَيْتِهِ، وَرَكْعَتَيْنِ قَبْلَ صَلاَةِ الصُّبْحِ، وَكَانَتْ سَاعَةً لاَ يُدْخَلُ عَلَى النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فِيهَا، حَدَّثَتْنِي حَفْصَةُ أَنَّهُ كَانَ إِذَا أَذَّنَ المُؤَذِّنُ وَطَلَعَ الفَجْرُ صَلَّى رَكْعَتَيْنِ، وَفِي لَفْظٍ: أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَانَ يُصَلِّي بَعْدَ الْجُمُعَةِ رَكْعَتَيْنِ.
Daga Dan Umar - Allah ya yarda da su - ya ce: Na kiyaye raka'o'i goma daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Raka'a biyu kafin Azahar, da raka'a biyu a bayan azahar, da raka'a biyu bayan Magariba a gidansa, da raka'a biyu bayan Issha' a gidansa, da raka'a biyu kafin sallar Asuba, wani lokaci ne ba'a shiga wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikinsa, Nana Hafsat ta zantar da ni cewa idan ladani ya yi kiran sallah, alfijir ya bullo zai yi sallah raka'a biyu, a wani lafazin: Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana sallah bayan Juma'a raka'a biyu.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi da dukkan ruwayoyin saDarajaIngantacce ne
Sharhi
Abdullahi Dan Umar - Allah Ya yarda da su - yana bayyana: Cewa daga nafilfilin da ya haddacesu daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - raka'o'i goma ana ambatansu sunnoni ratibai, raka'a biyu kafin Azahar, da raka'a biyu a bayan azahar, da raka'a biyu bayan Magariba a gidansa, da raka'a biyu bayan Isha'i a gidansa, da raka'a biyu kafin Asuba, raka'o'i goma sun cika kenan. Amma sallar Juma'a yana yin sallah raka'a biyu a bayanta.
Fa’idoji
- An so yin wadannan nafilfilin da lazimta a kansu.
- Halaciin yin sunna a gida.
Madogara
صحيح البخاري (2/ 58-59) (1180، 1181).
صحيح مسلم (2/ 601) (882).
تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، للبسام (ص112).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ زَيْنَبَ بِنْتِ جَحْشٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْها أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ دَخَلَ عَلَيْهَا فَزِعًا يَقُولُ: «لاَ إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ، وَيْلٌ لِلْعَرَبِ مِنْ شَرٍّ قَدِ اقْتَرَبَ، فُتِحَ اليَوْمَ مِنْ رَدْمِ يَأْجُوجَ وَمَأْجُوجَ مِثْلُ هَذِهِ» وَحَلَّقَ بِإِصْبَعِهِ الإِبْهَامِ وَالَّتِي تَلِيهَا، قَالَتْ زَيْنَبُ بِنْتُ جَحْشٍ فَقُلْتُ يَا رَسُولَ اللَّهِ: أَنَهْلِكُ وَفِينَا الصَّالِحُونَ؟ قَالَ: «نَعَمْ إِذَا كَثُرَ الخَبَثُ».
Daga Zainab 'yar Jahsh - Allah Ya yarda da ita - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shiga gurinta a firgice yana cewa; "Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, azaba ta tabbata ga larabawa daga sharrin da ya kusanto, a yau an buɗe katangar Yajuju da Majuju kwatankwacin hakan" sai ya kewaye ɗan yatsansa babba da wanda yake biye da shi.
Zainab 'yar Jahsh ta ce : Sai na ce ya Manzon Allah: Shin zamu halaka alhali a cikinmu akwai salihai? ya ce: "Eh, idan barna ta yi yawa".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shiga gurin Zainab 'yar Jahsh - Allah Ya yarda da ita - a firgice a tsorace, alhali shi yana cewa: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, dan sanarwa da tinanin afkuwar wani al'amari abin ki da zai faru, kuma babu tsira daga gare shi sai fakewa ga Allah - tsarki ya tabbatar maSa -, sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Kaico ya tabbata ga Larabawa daga wani sharrin da afkuwarsa ya kusanto, yau an buɗe katangar Yajuju da Majuju, shi ne katangar da Zulkarnaini ya ginata, misalin wannan; sai ya kewaye ɗan yatsansa babba da wanda ke biye da shi. Sai Zainab - Allah Ya yarda da ita - ta ce : Yaya Allah Zai halakar da mu alhali a cikinmu akwai muminai na gari? Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce mata: Idan barna ta yi yawa da fasikanci da fajirci da sabo, da zina, da giya, da wasunsu, to halaka zata game kowa da kowa.
Fa’idoji
- Firgici ba ya shagaltar da mumini daga ambatan Allah a lokacin tsoro; domin da ambatan Allah ne zukata suke nutsuwa.
- Kwaɗaitarwa akan hana sabo da hana afkuwarsa.
- Halaka mai gamewa tana faruwa saboda sababin yawan sabo da yaɗuwarsa da rashin hanawa koda mutanen kirki sun yawaita.
- Masifu suna game mutane baki ɗaya salihai da batattu, saidai za’a tashe su ne akan niyyoyinsu.
- Ya kebanci Larabawa a cikin faɗinsa: "Kaico ya tabbata ga Larabawa daga wani sharrin da ya kusanto"; domin su ne mafi yawan waɗanada suka musulunta lokacin da ya faɗi hakan.
Madogara
صحيح البخاري (4/ 138) (3346).
صحيح مسلم (4/ 2208) (2880).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 280).
كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (4/ 54).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (2/ 437).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 212).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ عَائِشَةَ أُمِّ المُؤمنينَ رضي الله عنها قَالَتْ: كُنْتُ أَغْتَسِلُ أَنَا وَالنَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ مِنْ إِنَاءٍ وَاحِدٍ كِلاَنَا جُنُبٌ، وَكَانَ يَأْمُرُنِي، فَأَتَّزِرُ، فَيُبَاشِرُنِي وَأَنَا حَائِضٌ، وَكَانَ يُخْرِجُ رَأْسَهُ إِلَيَّ وَهُوَ مُعْتَكِفٌ فَأَغْسِلُهُ وَأَنَا حَائِضٌ.
Daga Nana Aisha Uwar Muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce : Na kasance ina wanka ni da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - daga kwarya (abin wanka) daya mu duka biyun muna da janaba, ya kasance yana umartata, sai insa gwafso, sai ya rungumeni alhali ni ina al’ada, ya kasance yana fito min da kansa alhali shi yana i'itikafi sai in wanke masa shi alhali ina al’ada.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Nana A'isha uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - ta bada labari game da sashin halayenta na musamman tare da shi tsira da amincin Allah su tabbata agare shi, daga hakan: Ta kasance tana wankan janaba tare da shi tsira da amincin Allah su tabbata agare shi- daga kwarya daya sai su dinga diban ruwan tare. Kuma cewa shi tsira da amincin Allah su tabbata agare shi idan ya yi nufin zuwa mata alhali tana al’ada sai ya umarceta ta rufe jikinta daga cibiya zuwa gwiwa, sai ya rungumeta da abinda ke koma bayan jima'i. Kuma cewa shi tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya kasance yana i'itikafi a cikin masallaci sai ya fitar da kansa ga Nana A'isha alhali tana cikin dakinta tana al’ada.
Fa’idoji
- Halaccin wankan mutum da matarsa a kwarya daya.
- Halaccin rungumar mai al’ada a abinda ke kasa da farji, kuma cewa jikinta mai tsarki ne.
- An so sanyawarta gwafso a lokacin rungumemeniya.
- Rikon sabubba masu hana afkawa cikin haram.
- Hana mai al’ada zama a cikin masallaci.
- Halaccin tabawarta abubuwa danyu da busassu, daga hakan (akwai) wanke gashi da tsefe shi.
- Kyakkyawan mu'amalar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga iyalansa.
Madogara
صحيح البخاري (1/ 67) (299 - 301).
صحيح مسلم (1/ 244) (297)، (1/ 255) (319).
الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري (1/ 66).
تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، للبسام (ص79).
تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام، لابن عثيمين (1/ 76).
Wannan hadisi a HadeethEnc.com