عَنِ العَبَّاسِ بْنِ عَبْدِ الْمُطَّلِبِ رَضيَ اللهُ عنهُ قَالَ: قُلْتُ: يَا رَسُولَ اللهِ، عَلِّمْنِي شَيْئًا أَسْأَلُهُ اللَّهَ عَزَّ وَجَلَّ. قَالَ: «سَلِ اللَّهَ العَافِيَةَ»، فَمَكَثْتُ أَيَّامًا ثُمَّ جِئْتُ فَقُلْتُ: يَا رَسُولَ اللهِ، عَلِّمْنِي شَيْئًا أَسْأَلُهُ اللَّهَ. فَقَالَ لِي: «يَا عَبَّاسُ، يَا عَمَّ رَسُولِ اللهِ، سَلِ اللَّهَ العَافِيَةَ فِي الدُّنْيَا وَالآخِرَةِ».
Daga Abbas ɗan AbdulMuɗɗalib - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ce: Ya Manzon Allah, ka sanar dani wani abu in roƙi Allah, Allah - Mai girma da ɗaukaka -shi. Ya ce: "Ka roƙi Allah lafiya", sai na zauna wasu kwanuka sannan na zo sai na ce: Ya Manzon Allah, ka sanar dani wani abu in roƙi Allah shi. Sai ya ce dani: "Ya Abbas, ya baffan Manzon Allah, ka roƙi Allah lafiya a duniya da lahira".
Tirmizi da Ahmad sun rawaito shiDarajaIngantacce ne ta wani bangaren
Sharhi
Baffan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - Abbas ɗan Abdulmuɗɗalib - Allah Ya yarda da shi - ya nema daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya sanar da shi addu'ar da zai roƙi Allah ita, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya sanar da shi cewa ya roƙi Allah lafiya da kuɓuta daga illoli da aibuka a addini da duniya da lahira, Abbas ya ce: Bayan wasu kwanuka sai na dawo zuwa gare shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - karo na gaba ina tambayarsa ya sanar dani addu'ar da zan nemeta daga Allah, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce masa yana mai nuna masa kauna: Ya Abbas, ya baffan Manzon Allah, ka roki Allah lafiya dan tunkude kowace cuta da jawo kowane alheri da anfani a duniya da lahira.
Fa’idoji
- Maimaitawar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ita kanta addu'ar ga Abbas lokacin da ya tambaye shi karo na biyu yana nuni akan cewa lafiya ita ce mafi alherin abinda bawa zai roƙi UbangijinSa.
- Bayanin falalar lafiya, kuma a cikinta akwai tattarowar alherin duniya da lahira.
- Kwaɗayin sahabbai - Allah Ya yarda da su - akan neman ƙari na ilimi da alheri.
Madogara
سنن الترمذي (5/ 491) (3514).
مسند أحمد (3/ 303) (1783).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين (2/ 1014).
كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (17/ 468).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 566).
تطريز رياض الصالحين، لفيصل المبارك (ص815).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (6/ 40).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ رَضيَ اللهُ عنهما أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَانَ يَقُولُ: «اللهُمَّ لَكَ أَسْلَمْتُ، وَبِكَ آمَنْتُ، وَعَلَيْكَ تَوَكَّلْتُ، وَإِلَيْكَ أَنَبْتُ، وَبِكَ خَاصَمْتُ، اللهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِعِزَّتِكَ، لَا إِلَهَ إِلَّا أَنْتَ أَنْ تُضِلَّنِي، أَنْتَ الْحَيُّ الَّذِي لَا يَمُوتُ، وَالْجِنُّ وَالْإِنْسُ يَمُوتُونَ».
Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana cewa: "Ya Allah gareKa na miƙa wuya, kuma da Kai ne na yi imani, gareka ne na dogara, gareKa ne na dawo, saboda Kai ne na yi husuma, Ya Allah lallai ni ina neman tsari da buwayarKa, babu abin bautawa da gaskiya sai Kai (kada) Ka ɓatar da ni, Kaine Rayayye wanda ba zai mutu ba, aljanu da mutane kuwa zasu mutu"
Bukhari da Muslim ne suka ruwaito, wannan lafazin na Muslim ne, amma Bukhari ya rawaito shi a taƙaiceDarajaIngantacce ne
Sharhi
Ya kasance daga addu'ar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa shi ya kasance yana cewa: (Ya Allah gareKa ne na miƙa wuya) kuma na jawu, (da Kai ne na yi imani) na gasgata kuma na yi iƙrari, (kuma gareKa ne na dogara) na fawwala na kuma dogara, (gareKa ne na koma) na koma na fuskanta, (saboda Kai ne na yi husuma) na yi jayayya da maƙiyanKa, (Ya Allah ni ina neman tsarinKa) ina fakewa (da buwayarKa) da hanawarKa da kuma rinjayenKa, (babu abin bautawa da gaskiya sai Kai) kuma babu wani abin bautawa da gaskiya inba Kai ba, (da Ka ɓatar da ni) daga shiriya da dacewa da yardarKa, (Kai ne Rayayye wanda ba zai mutu ba) kuma ba zai ƙareba, (aljanu da mutane kuwa zasu mutu).
Fa’idoji
- Halaccin gabatar da yabo (ga Allah) a yayin roƙon kowane abin nema.
- Wajabcin dogara ga Allah - Maɗaukakin sarki - Shi kaɗai da neman kiyayewa daga gareShi; domin cewa Shi Mai siffantuwa ne da siffofin cika, kuma Shi kaɗaine wanda ake dogara da Shi, halittu dukkaninsu gajiyayyu ne kuma masu tiƙewa ne zuwa ga mutuwa, su basu cancanci dogara a kansu ba.
- Koyi da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikin addu'a da waɗannan kalmomi masu tattarowa komai ya shiga, waɗanda suke bayyanar da gaskiyar imani da kuma matuƙar sakankancewa.
- Sindi ya ce: Faɗinsa (Kai ne Rayayye) wato: Kai ne wanda ya kamata a nemi tsari da Shi ba waninKa ba.
Madogara
صحيح البخاري (9/ 117) (7383).
صحيح مسلم (4/ 2086) (2717).
تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص72).
فتح رب البرية بتلخيص الحموية، لابن عثيمين (ص79).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 109).
مرعاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح، عبيد الله المباركفوري (8/ 223).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ أَنَسٍ رضي الله عنه قَالَ: كَانَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يُكْثِرُ أَنْ يَقُولَ: «يَا مُقَلِّبَ القُلُوبِ ثَبِّتْ قَلْبِي عَلَى دِينِكَ»، فَقُلْتُ: يَا رَسُولَ اللهِ، آمَنَّا بِكَ وَبِمَا جِئْتَ بِهِ فَهَلْ تَخَافُ عَلَيْنَا؟ قَالَ: «نَعَمْ، إِنَّ القُلُوبَ بَيْنَ أُصْبُعَيْنِ مِنْ أَصَابِعِ اللهِ يُقَلِّبُهَا كَيْفَ يَشَاءُ».
Daga Anas - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana yawaita faɗin: "Ya mai jujjuya zukata Ka tabbatar da zuciyata akan addininKa" sai na ce: Ya Manzon Allah, mun yi imani da kai da kuma abinda ka zo da shi, shin kana jin tsoro akanmu ne? ya ce: "Eh, lallai zukata suna tsakanin yatsu biyu daga yatsun Allah Yana jujjuyasu yadda Ya ga dama".
Tirmizi da Ahmad sun rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Mafi yawan addu'ar Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ta kasance rokon Allah ne tabbata akan addini da biyayya, da nisanta daga karkata da kuma bata, Sai Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya yi mamakin yawaitawar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - akan wannan addu'ar, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ba shi labarin cewa zukata suna tsakanin yatsu biyu daga yatsun Allah Yana juyasu yadda Ya ga dama, Zuciya ita ce gurin imani da kafirci, hakika an anbaci zuciya (Kalbu) saboda yawan jujjuawarta; ita ce mafi tsananin jujjuyawa daga tukunya idan ta tafarfasa, wanda Allah Ya so Zai tsaida zuciyarsa akan shiriya, ya tabbatar da shi akan addini, wanda Allah Ya ga dama kuma Zai juyar da zuciyarsa daga shiriya zuwa karkata da bata.
Fa’idoji
- Kankan da kan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga Ubangijinsa da kankar dakai gareShi, da nunawa al'umma rokon hakan.
- Muhimmancin tsayuwa akan gaskiya da tabbata akan addini, kuma izina da karshe ne.
- Bawa ba ya wadatuwa daga Allah Ya tabbatarwa shi akan musulunci koda kiftawar ido.
- Kwadaitarwa akan yawaita wannan addu'ar dan koyi da Annabi - tsira da aminci su tabbata agare shi -.
- Tabbata akan musulunci shi ne ni'ima mafi girma wacce yake kamata ga bawa ya yi kokari gareta kuma ya godewa Ubangijinsa akanta.
Madogara
سنن الترمذي (4/ 19) (2140).
مسند أحمد (19/ 160) (12107).
كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (17/ 476).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 567).
نزهة المتقين، لمجموعة من الباحثين (2/ 1014).
تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص808).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (6/ 41).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن أنس رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رسُولُ الله صلى الله عليه وسلم : «ألِظُّوا بـ (يَاذا الجَلاَلِ والإكْرامِ)».
Daga Anas Dan Malik - Allah ya yarda da shi - ya ce Manzon Allah -tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Ku kama kafa da fadin Ya Ma'abocin Girma da Daukaka"r"
Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Al-Nasa'i Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara
- رياض الصالحين من كلام سيد المرسلين، للإمام أبي زكريا النووي، تحقيق د. ماهر الفحل، دار ابن كثير، دمشق، الطبعة الأولى، 1428ه.
- نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، تأليف د. مصطفى الخِن وغيره، مؤسسة الرسالة، بيروت، الطبعة الرابعة عشر، 1407هـ.
- كنوز رياض الصالحين، لحمد بن ناصر العمار، دار كنوز إشبيليا - الطبعة الأولى، 1430ه.
سنن الترمذي - محمد بن عيسى الترمذي، تحقيق وتعليق: أحمد محمد شاكر ومحمد فؤاد عبد الباقي وإبراهيم عطوة عوض - شركة مكتبة ومطبعة مصطفى البابي الحلبي - مصر، الطبعة: الثانية، 1395هـ - 1975م.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ عَبْدِ اللهِ بْنِ مَسْعُودٍ رَضيَ اللهُ عنهُ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَنَّهُ كَانَ يَقُولُ: «اللهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ الْهُدَى وَالتُّقَى، وَالْعَفَافَ وَالْغِنَى».
Daga Abdullahi ɗan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa shi ya kasance yana cewa: «Ya Ubangiji ina roƙonKa shiriya da tsoron Allah, da kamewa, da wadata».
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Ya kasance daga addu'ar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: «Ya Allah ni ina roƙonKa shiriya» hanya madaidaiciya na sanin gaskiya da aiki da ita.
«Da tsoron Allah», ruko da umarni da nisantar hane-hane. «Da kamewa» kamewa daga abinda ba ya halatta kuma ba shi da kyau na magana ne ko aiki.
«Da wadatuwa» daga halitta, inda ba zai yi buƙatuwa ba zuwa ga wani inba Uabngijinsa - Mai girma da ɗaukaka ba -.
Fa’idoji
- Ɗaukakar waɗannan ɗabi'un: Shiriya da tsoron Allah da kamewa da wadata, da kwaɗaitarwa akan ɗabi'antuwa da su.
- Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ba ya mallakawa kansa wani amfani ko cutarwa, wanda yake mallakar hakan Shi ne Allah - Maɗaukakin sarki -.
- Wanda yake mallakar amfani da cutarwa da shiryar da halitta Shi ne Allah Shi kaɗai, ba wani mala'ika makusanci ba kuma ba wani Annabi abin aikowa ko waninsu ba.
Madogara
صحيح مسلم (4/ 2087) (2721).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 146).
تطريز رياض الصالحين، لفيصل المبارك (ص68).
كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (2/ 183).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (1/ 528).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، مجموعة من الباحثين (1/ 104).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن ابن عباس رضي الله عنهما أن رسول الله صلى الله عليه وسلم كان يقول: «اللَّهُمَّ لك أَسْلَمْتُ، وبِكَ آمَنتُ، وعَلَيكَ تَوَكَّلْت، وإِلَيكَ أَنَبْتُ، وبك خَاصَمْتُ، اللهم أعُوذ بِعزَّتك؛ لا إله إلا أنت أن تُضلَّني، أنت الحَيُّ الذي لا تموت، والجِنُّ والإنْسُ يَمُوتُونَ».
Dangane da Ibn Abbas, Allah ya yarda da su duka biyu, cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana cewa: “Ya Allah, na rungume ka, kuma da kai na yi imani, kuma a kan ka na dogara, kuma a gare ka na tuba, kuma na yi rigima da kai, Allah ina neman tsarinka; Babu wani abin bauta sai kai ka batar da ni, kai rayayye ne da ba ya mutuwa, aljannu da mutane za su mutu. ”
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Dangane da Ibn Abbas - Allah ya yarda da su duka - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana cewa: (Ya Allah, ka musulunta) wato mika wuya ga bayyane, ba ga wasu ba, (kuma tare da ku kun yi imani) wannan shi ne: yarda a ciki, (kuma dole ne ku dogara) wato: Na rungumi dukkan lamurana Don sarrafa shi, don ba ni da wani amfani ko cutarwa, (kuma a gare ku ya girma) wannan shi ne: Na dawo daga rashin biyayya ga biyayya ko daga gafala zuwa zikiri, (da kuma a kanku) tare da taimakonku (Na yi husuma) wato: Na yi yaƙi da maƙiyanku, (Ya Allah, ina neman tsari a cikin ɗaukakarka) wato: tare da nasararku, ɗaukaka ga Allah Duk. (Babu wani abin bauta sai kai) Babu wani abu na bautar gumaka sai kai, kuma babu wata tambaya face daga gare ka, kuma babu wata mafaka sai ta hanyarka. (Don batar da ni) Wato ina neman tsarinku kada ku batar da ni bayan kun shiryar da ni kuma kun yarda da ni a bayyane da mika wuya a cikin hukunce-hukuncenku da hukuncinku, in wakilta a bangarenku, ku yi fada da makiyanku, kuma ku nemi duk wata daukaka da nasararku, (Kai ne rayayyun da ba su mutuwa, kuma aljannu da mutane suna mutuwa).
Madogara
- صحيح البخاري -الجامع الصحيح-؛ للإمام أبي عبد الله محمد بن إسماعيل البخاري، عناية محمد زهير الناصر، دار طوق النجاة، الطبعة الأولى، 1422هـ.
- صحيح مسلم؛ للإمام مسلم بن الحجاج، حققه ورقمه محمد فؤاد عبد الباقي، دار عالم الكتب-الرياض، الطبعة الأولى، 1417هـ.
- كنوز رياض الصالحين، لحمد بن ناصر العمار، دار كنوز إشبيليا- الطبعة الأولى1430ه.
- شرح رياض الصالحين؛ للشيخ محمد بن صالح العثيمين، مدار الوطن، الرياض، 1426هـ.
- دليل الفالحين لطرق رياض الصالحين؛ لمحمد بن علان الشافعي، تحقيق خليل مأمون شيحا-دار المعرفة-بيروت-الطبعة الرابعة1425ه.
- بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين؛ تأليف سليم الهلالي، دار ابن الجوزي- الطبعة الأولى1418ه.
- نزهة المتقين شرح رياض الصالحين؛ تأليف د. مصطفى الخِن وغيره، مؤسسة الرسالة-بيروت، الطبعة الرابعة عشرة، 1407هـ.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَن قُطْبَةَ بنِ مَالِكٍ رَضيَ اللهُ عنه قَالَ: كَانَ النَّبِيُّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: «اللَّهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ مِنْ مُنْكَرَاتِ الأَخْلاَقِ وَالأَعْمَالِ وَالأَهْوَاءِ».
Daga Ƙuɗbah ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana cewa: «Ya Allah lallai ni ina neman tsarinKa, daga munanan ɗabi'u da ayyuka da soye-soyen rayuka».
Tirmizi ne ya ruwaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Ya kasance daga cikin addu'ar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: (Ya Allah lallai ni ina neman tsari) ina fakewa (da Kai) banda waninKa, (daga munanan) abubuwan da Allah da ManzonSa suka hana su, (ɗabi'u) kamar ƙullata da hassada da girman kai, (da kuma) munanan (ayyuka) kamar zagi, (da) dukkanin (soye-soyen zuciya), waɗanda zuciya take son su alhali sun saɓawa shari'a.
Fa’idoji
- Falalar wannan addu'ar kuma an so a yi ta.
- Mumini yana kwaɗayi akan nisantar ɗabi'u ababen zargi da kuma munanan ayyuka, kuma yana kiyayewa daga bin son rai da kuma afkawa cikin sha'awowi.
- Rarrabuwar ɗabi'u da soye-soyen zuciya zuwa munana da kuma kyawawa.
Madogara
سنن الترمذي (5/ 544) (3591).
فتح ذي الجلال والاكرام بشرح بلوغ المرام، لابن عثيمين (6/ 389).
منحة العلام في شرح بلوغ المرام، لعبد الله الفوزان (10/ 248).
توضِيحُ الأحكَامِ مِن بُلوُغ المَرَام، للبسام (7/ 436).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن سعد بن أبي وقاص رضي الله عنه قَال: عَادَنِي رسول الله صلى الله عليه وسلم فقال: «اللَّهُمَّ اشْفِ سَعْداً، اللَّهُمَّ اشْفِ سَعْداً، اللَّهُمَّ اشْفِ سَعْداً».
Daga Saad bin Abi Waqas - yardar Allah ta tabbata a gare shi - ya ce: Manzon Allah - SAW- ya tursasa ni ya ce: "Ya Allah, ka warkar da farin ciki, ya Allah, ka warkar da farin ciki, ya Allah, ka warkar da Sa'adi".
Bukhari da Muslim Suka Rawaito shi amma lafazin na Muslim neDarajaIngantacce ne
Madogara
صحيح مسلم, ترقيم محمد فؤاد عبد الباقي, دار إحياء التراث العربي, بيروت.
دليل الفالحين لطرق رياض الصالحين لمحمد بن علان الصديقي, دار الكتاب العربي.
شرح رياض الصالحين لابن عثيمين , دار الوطن للنشر، الرياض, الطبعة: 1426 هـ.
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين لسليم الهلالي, دار ابن الجوزي.
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين لمجموعة من الباحثين, مؤسسة الرسالة, الطبعة الرابعة عشر, 1407ه.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comKowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com