Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Ya Allah lallai ni ina neman tsarinKa, daga munanan ɗabi'u da ayyuka da soye-soyen rayuka

عَن قُطْبَةَ بنِ مَالِكٍ رَضيَ اللهُ عنه قَالَ: كَانَ النَّبِيُّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: «اللَّهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ مِنْ مُنْكَرَاتِ الأَخْلاَقِ وَالأَعْمَالِ وَالأَهْوَاءِ».
Daga Ƙuɗbah ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana cewa: «Ya Allah lallai ni ina neman tsarinKa, daga munanan ɗabi'u da ayyuka da soye-soyen rayuka».
Tirmizi ne ya ruwaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Ya kasance daga cikin addu'ar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: (Ya Allah lallai ni ina neman tsari) ina fakewa (da Kai) banda waninKa, (daga munanan) abubuwan da Allah da ManzonSa suka hana su, (ɗabi'u) kamar ƙullata da hassada da girman kai, (da kuma) munanan (ayyuka) kamar zagi, (da) dukkanin (soye-soyen zuciya), waɗanda zuciya take son su alhali sun saɓawa shari'a.

Fa’idoji
  1. Falalar wannan addu'ar kuma an so a yi ta.
  2. Mumini yana kwaɗayi akan nisantar ɗabi'u ababen zargi da kuma munanan ayyuka, kuma yana kiyayewa daga bin son rai da kuma afkawa cikin sha'awowi.
  3. Rarrabuwar ɗabi'u da soye-soyen zuciya zuwa munana da kuma kyawawa.
Madogara

سنن الترمذي (5/ 544) (3591). فتح ذي الجلال والاكرام بشرح بلوغ المرام، لابن عثيمين (6/ 389). منحة العلام في شرح بلوغ المرام، لعبد الله الفوزان (10/ 248). توضِيحُ الأحكَامِ مِن بُلوُغ المَرَام، للبسام (7/ 436).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
ADDU'O'I DA AKA RUWAITO

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com