Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Ya Allah ina neman tsarinKa daga gushewar ni'imarKa, da juyawar lafiyarKa, da shammatar azabarKa, da dukkan fushinKa

عَنْ عَبْدِ اللهِ بْنِ عُمَرَ رضي الله عنهما قَالَ: كَانَ مِنْ دُعَاءِ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «اللهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ مِنْ زَوَالِ نِعْمَتِكَ، وَتَحَوُّلِ عَافِيَتِكَ، وَفُجَاءَةِ نِقْمَتِكَ، وَجَمِيعِ سَخَطِكَ».
Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Ya kasance daga addu'ar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi -: "Ya Allah ina neman tsarinKa daga gushewar ni'imarKa, da juyawar lafiyarKa, da shammatar azabarKa, da dukkan fushinKa".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya nemi tsari daga abubuwa huɗu: Na farko: (Ya Allah ni ina neman tsarinKa daga gushewar ni'imarKa) ta Addini da duniya kuma in tabbata akan Musulunci, in nisanci faɗawa cikin saɓon da yake gusar da ni'imomi. Na biyu: (Da juyawar lafiyarKa) da canjata zuwa bala'i; to ina roƙonKa dawwamar lafiya, da kuɓuta daga radaɗi da cututtuka. Na uku: (Da shammatar azabarKa) daga bala'i ko saɓo, azaba da uƙuba idan suka zo fuj'a bagtatan, to babu wani lokaci a wannan dan tuba da riska, wanda aka shafa da su zai zama mafi girma kuma mafi tsanani. Na huɗu: (Da dukkan fushinKa) da sabubban da suke wajabta fushinKa; domin wanda Ka yi fushi da shi to haƙiƙa ya taɓe kuma ya yi asara. Haƙiƙa tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya zo da lafazin jam'i; dan ya ƙunshi sabubban fushinSa - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka - daga maganganu da ayyuka da ƙudirce-ƙudierce.

Fa’idoji
  1. Buƙatuwar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - zuwa ga Allah - Maɗaukakin sarki -.
  2. Waɗannan neman tsarin masu albarka sun ƙunshi: Dacewa ga godewar ni'imomi, da kiyayewa daga afkawa cikin saɓo; domin cewa su suna gusar da ni'imomi.
  3. Kwaɗayi daga barin nisanta daga guraren fushin Allah - Maɗaukakin sarki -.
  4. (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya nemi tsari daga shammatar azabar Allah - Maɗaukakin sarki -; domin cewa Shi idan Ya yi wa bawa azaba to haƙiƙa Ya saukar masa da bala'in da ba zai iya tunkuɗeshi ba, kuma ba zai nemi kariyar ragowar halittu ba, koda sun taru gaba ɗaya.
  5. (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya nemi tsari daga juyawar lafiyarSa - tsarki ya tabbatar maSa -; domin cewa shi idan Allah ya kasance ya keɓance shi da lafiyarSa to haƙiƙa ya rabauta da alherin duniya da lahira, idan ta juya daga gare shi to haƙiƙa an taɓa shi da sharrin duniya da lahira, domin cewa lafiya da ita ce gyaruwar Addini da duniya (suke).
Madogara

صحيح مسلم (4/ 2097) (2739). توضيح الأحكام من بلوغ المرام، لعبد الله البسام (7/ 568). منحة العلام في شرح بلوغ المرام، لعبد الله الفوزان (10/ 447). فتح ذي الجلال والإكرام، لابن عثيمين (6/ 495). سبل السلام بشرح بلوغ المرام، لمحمد الصنعاني (2/ 711 ).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
ADDU'O'I DA AKA RUWAITO

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com

Ya Allah ina neman tsarinKa daga gushewar ni'imarKa, da juyawar lafiyarKa, da shammatar azabarKa, da dukkan fushinKa · Hadisai tare da sharhi · Sabīl