Daga Abdullahi ɗan Amr ɗan al-Aas - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana Addu’a da waɗannan kalomin: "Ya Allah ni ina neman tsarinKa daga rinjayar bashi, da rinjayar maƙiyi, da dariyar maƙiya".
Nasa'i ne ya ruwaito shi da AhmadDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya nemi tsari daga wasu al'amra:
Na farko: (Ya Allah ni ina neman tsari) ina fakewa ina dogara (da Kai) bada wanin Ka ba, (daga rinjayar bashi) da rinjayarsa da baƙin cikinsa da takaicin sa, ina roƙonKa taimako akan biyansa da warware shi.
Na biyu: (Rinjayar maƙiyi) da rinjayansa da ɗora shi akaina, ina roƙon Ka kame cutarsa, da nasararsa a kansa.
Na uku: (Dariyar maƙiya) da farin cikin makiya akan abinda yake samun musulmai na bala'i da musiba.
Fa’idoji
Kwaɗaitarwa akan neman tsari daga dukkasn abinda yake shagaltarwa daga ɗa'a kuma yake jawo baƙƙan ciki kamar bashi.
Cin bashi kai tsaye babu laifi a cikinsa, kawai damuwa ga wanda ba shi da da abinda zai biya bashin, wannan shi ne bashi mai rinjaye.
Mutum ya wajaba akansa ya nisanci al'amuran da za yi masa dariya da su kuma a aibata shi a kansu.
Bayanin ƙiyayyar kafirai ga muminai da dariyar ƙetarsu garesu a lokacin aukawar masifu.
Maƙiya su bayyanar da farin cikinsu ga musifar mutum yana tsananta bala'in akan mutum.
Madogara
سنن النسائي (8/ 265) (5475).
مسند أحمد (11/ 189) (6618).
توضيح الأحكام من بلوغ المرام، لعبد الله البسام (7/ 569).
منحة العلام في شرح بلوغ المرام، لعبد الله الفوزان (10/ 450).
فتح ذي الجلال والإكرام، لابن عثيمين (6/ 497).
Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com