Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

ka ce Ya Allah Ka shiryar dani Ka datar dani, ka ambaci shiriya (irin) shiriyarka ta hanya, da dacewa (irin) dacewar kibiya

عَنْ عَلِيٍّ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ لِي رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «قُلِ اللهُمَّ اهْدِنِي وَسَدِّدْنِي، وَاذْكُرْ بِالْهُدَى هِدَايَتَكَ الطَّرِيقَ، وَالسَّدَادِ سَدَادَ السَّهْمِ».
Daga Ali - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce da ni: "ka ce Ya Allah Ka shiryar dani Ka datar dani, ka ambaci shiriya (irin) shiriyarka ta hanya, da dacewa (irin) dacewar kibiya
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya umarci Ali ɗan Abu Ɗalib - Allah Ya yarda da shi - ya roƙi Allah ya tambaye shi sai ya ce: (Ya Allah Ka shiryar da ni) Ka shiryar da ni Ka nuna mini (Ka datar da ni) Ka yi mini gam da katar, Ka sanya ni madaidaici a dukkan al'amurana. Shiriya: Ita ce sanin gaskiya a fayyace kuma a dunƙule, da dacewa ga binta a zahiri da baɗini. Dacewa kuwa: Ita ce dacewa da daidaita a dukkanin al'amura da abinda zai zama daidai akan gaskiya, shi ne hanya madaidaiciya a magana da aiki da ƙudiri. Kuma cewa umarni na ma'ana yana bayyana da abin ji; ka tina alhali kai kana yin wannan addu'ar cewa: (Shiriya: Shiriyarka (irin ta) hanya) ka halarto zuciyarka alhali kai kana roƙon shiriya kamar shiriyar wanda ya yi tafiya, cewa shi baya kaucewa akan hanya dama da hagu; hakan dan ya kuɓuta daga ɓata (makuwa), da haka ne zai samu kuɓuta, ya kai zuwa manufarsa a gaggauce. (Daidaita: (irin) daidaitar kibiya) kai kana lura a lokacin da kake daidaita kibiya a gaggawar saduwarta da samunta ga inda aka harbata, mai harbi idan ya harbi inda yake so sai ya daidaita kibiya wajen inda zai harba, to haka nan zaka roƙi Allah - Maɗaukakin sarki - cewa abinda ka yi niyyarsa na daidai yana kan yanayin kibiya; sai ka zama a roƙonka mai neman matuƙar shiriya, da ƙarshen daidaita. Ka halarto wannan ma'anar a zuciyarka har sai ka roƙi Allah daidai dan abinda ka yi niyyarsa daga hakan ya zama akan yanayin abinda kake anfani da shi na harbi.

Fa’idoji
  1. Mai addu'a ya kamata ya yi kwaɗayi akan daidaita aikinsa da daidaita shi ta hanyar lazimtar sunna da tsarkake niyya.
  2. An so yin addu'a da waɗannan kalmomin mai tattarowa ga dacewa da daidaita.
  3. Ya kamata ga bawa ya nemi taimakon Allah - Maɗaukakin sarki - a dukkan al'amuransa.
  4. Buga misali a lokacin koyarwa.
  5. Haɗawa tsakanin neman shiriya da gyaruwar hali, da tafiya akansa da rashin karkata daga gare shi koda ƙiftawar ido da gyaruwar makoma, faɗinsa: "Ka shiryar da ni" shi ne ya zama mai tafiya akan hanyar shiriya, da faɗinsa: "Ka datar da ni": Na dacewa da rashin karkacewa a lokacin shiriyar da ya riƙeta.
  6. Mai Addu'a ya kamata gare shi ya himmantu da addu'arsa, ya halarto ma'anonin addu'arsa a cikin zuciyarsa; to wannan ya fi kusa ga karɓuwa.
Madogara

صحيح مسلم (4/ 2090) (2725). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 546). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (2/ 1006). كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (17/ 383).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
ADDU'O'I DA AKA RUWAITO

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com