Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Mafi yawan addu'ar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ta kasance: "Ya Allah Ubangijinmu Ka bamu kyakkyawa a duniya, a lahira ma kyakkyawa, kuma ka karemu azabar wuta

عَنْ أَنَسٍ رضي الله عنه قَالَ: كَانَ أَكْثَرُ دُعَاءِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «اللَّهُمَّ رَبَّنَا آتِنَا فِي الدُّنْيَا حَسَنَةً، وَفِي الآخِرَةِ حَسَنَةً، وَقِنَا عَذَابَ النَّارِ».
Daga Anas - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Mafi yawan addu'ar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ta kasance: "Ya Allah Ubangijinmu Ka bamu kyakkyawa a duniya, a lahira ma kyakkyawa, kuma ka karemu azabar wuta".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana yawaita addu'a da addu'a gamammiya, daga cikinsu: "Ya Allah Ubangijinmu Ka bamu kyakkyawa a duniya, a lahira ma kyakkyawa, kuma Ka tsaremu azabar wuta", Ita ta tattaro kyau a duniya na arziki mai dadi, mayalwaci na halal, da mace ta gari, da da wanda ido zai yi farin ciki da shi, da hutu, da ilimi mai amfani, da makamancin hakan na abububuwan da ake so na halal, kyakkyawa a lahira na kubuta daga ukubobin kabari da tsayuwa da wuta, da samuwar yardar Allah, da rabauta da ni'ima madawwamiya, da kusanci ga Ubangiji Mai jin kai a lahira.

Fa’idoji
  1. An so addu'a da addu'o'i masu tattarowa, dan koyi da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
  2. Mafi cika mutum ya hada tsakanin alherin duniya da lahira a addu'arsa.
Madogara

صحيح البخاري (8/ 83) (6389). صحيح مسلم (4/ 2070) (2690). توضيح الأحكام من بلوغ المرام، للبسام (7/ 578). منحة العلام في شرح بلوغ المرام، لعبد الله الفوزان (10/ 463). فتح ذي الجلال والإكرام، لابن عثيمين (6/ 504). سبل السلام بشرح بلوغ المرام، للصنعاني (2/ 714).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
ADDU'O'I DA AKA RUWAITO

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com