عَنْ أَبِي سَعِيدٍ الْخُدْرِيِّ قَالَ: خَرَجَ مُعَاوِيَةُ عَلَى حَلْقَةٍ فِي الْمَسْجِدِ، فَقَالَ: مَا أَجْلَسَكُمْ؟ قَالُوا: جَلَسْنَا نَذْكُرُ اللهَ، قَالَ آللَّهِ مَا أَجْلَسَكُمْ إِلَّا ذَاكَ؟ قَالُوا: وَاللهِ مَا أَجْلَسَنَا إِلَّا ذَاكَ، قَالَ: أَمَا إِنِّي لَمْ أَسْتَحْلِفْكُمْ تُهْمَةً لَكُمْ، وَمَا كَانَ أَحَدٌ بِمَنْزِلَتِي مِنْ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَقَلَّ عَنْهُ حَدِيثًا مِنِّي: وَإِنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ خَرَجَ عَلَى حَلْقَةٍ مِنْ أَصْحَابِهِ، فَقَالَ: «مَا أَجْلَسَكُمْ؟» قَالُوا: جَلَسْنَا نَذْكُرُ اللهَ وَنَحْمَدُهُ عَلَى مَا هَدَانَا لِلْإِسْلَامِ، وَمَنَّ بِهِ عَلَيْنَا، قَالَ: «آللَّهِ مَا أَجْلَسَكُمْ إِلَّا ذَاكَ؟» قَالُوا: وَاللهِ مَا أَجْلَسَنَا إِلَّا ذَاكَ، قَالَ: «أَمَا إِنِّي لَمْ أَسْتَحْلِفْكُمْ تُهْمَةً لَكُمْ، وَلَكِنَّهُ أَتَانِي جِبْرِيلُ فَأَخْبَرَنِي أَنَّ اللهَ عَزَّ وَجَلَّ يُبَاهِي بِكُمُ الْمَلَائِكَةَ».
Daga Abu Sa'id AlKudri ya ce: Mu'awiya ya fito ga wata halƙa a cikin masallaci, sai ya ce: Me ya zaunar da ku? suka ce: Mun zauna muna ambatan Allah, ya ce kun rantse da Allah babu abinda ya zaunar da ku sai hakan? suka ce: Wallahi babu abinda ya zaunar da mu sai hakan, ya ce: Amma ni ban rantsar da ku ba dan tuhuma gareku, kuma babu wani a matsayina daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - mafi ƙarancin hadisi daga gareni: Lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya fito ga wata halƙa daga sahabbansa, sai ya ce; "Me ya zaunar da ku?" suka ce: Mun zauna muna ambatan Allah muna gode masa akan abinda ya shiryar da mu na musulunci, kuma ya yi baiwa da shi garemu, ya ce: "Kun rantse da Allah babu abinda ya zaunar da ku sai hakan? suka ce: Wallahi babu abinda ya zaunar da mu sai hakan, ya ce: "Amma ni ban rantsar da ku ba dan tuhuma gareku, sai dai cewa (Mala'ika) Jibril ya zo min sai ya ba ni labarin cewa Allah - mai girma da ɗaukaka - Yana yi wa mala'iku alfahari da ku".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Mu'awiya Dan Abu Sufyan - Allah Ya yarda da su - ya fito ga wata halƙa a cikin Masallaci, sai ya tambayesu akan wanne abu ne suka taru? sai suka ce: Muna ambatan Allah, sai ya sa suka rantse, Allah Ya yarda da shi - cewa su ba su yi nufin komai da taruwarsu ba sai zikiri, sai suka rantse masa, Sannan ya ce da su: Lallai ni ban rantsar da ku ba dan tuhuma gareku da kuma kokwanto a gaskiyarku ba, sannan ya bada labari game da matsayinsa ga annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kuma cewa shi babu wani mutum dake da matsayin kusancin sa daga gare shi; dan kasancewar Ummu Habiba 'yar uwarsa ce kuma matar annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ce-, dan kuma kasancewarsa daga marubutan wahayi, tare da hakan to shi mai ƙarancin riwaya ne ga hadisai. Sai ya zantar da su cewa annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya fito wata rana daga gidansa, sai ya samesu a zaune a cikin masallaci, suna anbaton Allah suna gode masa akan shiryar da su da ya yi , ya kuma ni’imta su da shi, sai - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tambaye su ya kuma rantsar da su da irin abinda Mu'awiya - Allah Ya yarda da shi - ya aikata tare sahabban sa. Sannan annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya faɗa musu sababin tambayar sa gare su da kuma rantsar da su da ya yi: Cewa mala'ika Jibrilu - aminci ya tabbata a gare shi - ya zo masa sai ya ba shi labarin cewa Allah - mai girma da ɗaukaka - Yana yi wa mala'iku alfahari da ku, kuma yana bayyanar da falalarku gare su, kuma yana nuna musu kyakkyawan ayyukanku, Yana yabon ku a gurin su.
Fa’idoji
- Falalar Mu'awiya - Allah Ya yarda da shi - da kwaɗayin sa akan koyi da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a isar da ilimi.
- Halaccin sa a rantse ba tare da tuhuma ba dan faɗakarwa akan muhimmancin alheri.
- Falalar majalisan zikiri da ilimi kuma cewa Allah Yana son su kuma Yana yi wa mala'iku alfahari da su.
Madogara
صحيح مسلم (4/ 2075) (2701).
نزهة المتقين (2/ 993).
بهجة الناظرين، لسليم الهلالي (2/ 522).
كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (17/ 271).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن أنس بن مالك رضي الله عنه قال: كان أخوانِ على عهد النبي صلى الله عليه وسلم وكان أحدُهما يأتي النبي صلى الله عليه وسلم والآخر يَحتَرِف، فَشَكَا الُمحتَرِف أَخَاه للنبي صلى الله عليه وسلم فقال: «لعَلَّك تُرزَقُ بِهِ».
Daga Anas bn Malik - Allah ya yarda da shi - ya ce: Akwai ‘yan’uwa maza biyu a zamanin Annabi -SAW- kuma dayansu zai zo wurin Annabi -SAW- dayan kuma kwararre ne. da shi ".
Al-Tirmithi Ya Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Anas, Allah ya yarda da shi, ya ce: Akwai wasu 'yan'uwa maza biyu a lokacin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - kuma wani daga taron zai zo taron Annabi - kuma don Allah - me - Kuma - me yasa - kuma ya raka shi ya karba daga abokan hulda kuma ya karba daga maganganun da zaiyi, yayin da dayan zaiyi aiki mai girma kuma ya himmatu wajen neman. Kwararren ya koka da dan uwansa game da barin aikin ga Annabi - Allah, ya albarkace shi ya kuma ba ni - sannan me ya sa - sannan shi - shi a gare ni da ni da kuma dalilin da ya sa - ya nishadantar da shi: Wata ƙila yin al'amuransa dalili ne na sau manyan maganganun azabar azar . Domin Allah yana taimakon bawan, bawan ba zai taimaki ɗan'uwansa ba.
Madogara
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين لسليم الهلالي، ط1، دار ابن الجوزي، الدمام، 1415هـ.
تطريز رياض الصالحين للشيخ فيصل المبارك، ط1، تحقيق: عبد العزيز بن عبد الله آل حمد، دار العاصمة، الرياض، 1423هـ.
جامع الترمذي، تحقيق وتعليق: أحمد محمد شاكر وآخرون، ط2، شركة مكتبة ومطبعة مصطفى البابي الحلبي، مصر، 1395هـ.
دليل الفالحين لطرق رياض الصالحين، لمحمد علي بن محمد بن علان، ط4، اعتنى بها: خليل مأمون شيحا، دار المعرفة، بيروت، 1425هـ.
صحيح الجامع الصغير وزياداته، للألباني، نشر: المكتب الإسلامي.
رياض الصالحين للنووي، ط1، تحقيق: ماهر ياسين الفحل، دار ابن كثير، دمشق، بيروت، 1428هـ.
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين، ط14، مؤسسة الرسالة، 1407هـ.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن أنس رضي الله عنه مرفوعاً: «من خَرج في طلب العلم فهو في سَبِيلِ الله حتى يرجع».
Daga Anas - Allah ya yarda da shi - da isnadi: "Duk wanda ya fita neman ilimi to zai kasance a kan tafarkin Allah har sai ya dawo."
Al-Tirmithi Ya Rawaito shiDarajaHasan ne
Sharhi
Ma'anar hadisin: Wanda ya fita daga gidansa ko kasarsa Don neman ilimin shari'a, yana zuwa karkashin hukuncin wanda ya fita zuwa jihadi saboda Allah Madaukaki, don haka zai koma ga danginsa. Domin kamar mai gwagwarmaya ne wajen rayar da addini, da wulakanta Iblis, da wahalar da kai.
Madogara
جامع الترمذي، تحقيق وتعليق:أحمد محمد شاكر وآخرون، مكتبة ومطبعة مصطفى البابي الحلبي، ط2، مصر، 1395هـ.
دليل الفالحين لطرق رياض الصالحين، لمحمد علي بن محمد بن علان، ط4، اعتنى بها: خليل مأمون شيحا، دار المعرفة، بيروت، 1425ه.
رياض الصالحين للنووي، ط1، تحقيق: ماهر ياسين الفحل، دار ابن كثير، دمشق، بيروت، 1428هـ.
رياض الصالحين، ط4، تحقيق: عصام هادي، وزارة الأوقاف والشؤون الإسلامية القطرية، دار الريان، بيروت، 1428هـ.
صحيح الترغيب والترهيب، للألباني، ط5، مكتبة المعارف – الرياض.
مرعاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح، للمباركفوري، الطبعة الثالثة، إدارة البحوث العلمية والدعوة والإفتاء، الجامعة السلفية - بنارس الهند، 1404هـ.
مرقاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح، للقاري، ط1، دار الفكر، بيروت، 1422هـ.
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين، ط14، مؤسسة الرسالة، 1407هـ.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ أَبِي مُوسَى رَضيَ اللهُ عنه عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «مَثَلُ مَا بَعَثَنِي اللَّهُ بِهِ مِنَ الهُدَى وَالعِلْمِ كَمَثَلِ الغَيْثِ الكَثِيرِ أَصَابَ أَرْضًا، فَكَانَ مِنْهَا نَقِيَّةٌ، قَبِلَتِ المَاءَ، فَأَنْبَتَتِ الكَلَأَ وَالعُشْبَ الكَثِيرَ، وَكَانَتْ مِنْهَا أَجَادِبُ، أَمْسَكَتِ المَاءَ، فَنَفَعَ اللَّهُ بِهَا النَّاسَ، فَشَرِبُوا وَسَقَوْا وَزَرَعُوا، وَأَصَابَتْ مِنْهَا طَائِفَةً أُخْرَى، إِنَّمَا هِيَ قِيعَانٌ لاَ تُمْسِكُ مَاءً وَلاَ تُنْبِتُ كَلَأً، فَذَلِكَ مَثَلُ مَنْ فَقُهَ فِي دِينِ اللَّهِ وَنَفَعَهُ مَا بَعَثَنِي اللَّهُ بِهِ، فَعَلِمَ وَعَلَّمَ، وَمَثَلُ مَنْ لَمْ يَرْفَعْ بِذَلِكَ رَأْسًا، وَلَمْ يَقْبَلْ هُدَى اللَّهِ الَّذِي أُرْسِلْتُ بِهِ».
Daga Abu Musa - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Kwatankwacin abinda Allah Ya aikoni da shi, na shiriya da ilimi kamar kwatankwacin girgije ne mai yawa da ya zuba a wata ƙasa, daga cikinta akwai tsarkakakkiya, ta karɓi ruwa, sai ta tsirar da ciyawa mai yawa, kuma daga cikinta akwai mai fari, ta riƙe ruwan, sai Allah Ya amfani mutane da ita, sai suka sha suka shayar, kuma suka yi shuka, kuma ruwan ya samu wani ɓangare daban, wanda shi kawai faƙo ne ba ya riƙe ruwan kuma ba ya tsirar da ciyawa, to hakan kwatankwacin wanda ya fahimci Addinin Allah ne kuma Ya amfanar da shi da abinda Allah Ya aikoni da shi, sai ya sani ya kuma sanar, da kwatankwacin wanda bai ɗaga kai ba da hakan, kuma bai karɓi shiriyar Allah ba wacce aka aikoni da ita ba».
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kamanta yana mai ban ammaki wanda yake anfanuwa da abinda ya zo da shi na hujjoji da kuma hanyar da zata kai zuwa ga abin da ake nema, da kuma ilimi na shari'a da ƙasar da ruwa mai yawa yake sauka a ita; sai ta zama ta kasu kaso uku: Na farkonsu: Tsarkakakkiyar ƙasa mai tsarki, wacce take karɓar ruwan sama, sai ta tsirar da tsirrai mai yawa ɗanye da busasshe, sai mutane suka amfana da ita. Na biyunsu: Ƙasar da take riƙe ruwa, saidai ba ta tsirar da shuka, ita tana kiyaye ruwa dan mutane su amfana da shi; sai su sha su shayar da dabbobinsu da kuma shukarsu. Na ukunsu: Ƙasa madaidaiciya mai santsi wacce ba ta riƙe ruwa kuma ba ta tsirar da shuka, ita akan kanta ba ta amfana da ruwan da hakan ba, haka kuma mutane basu amfana da ruwan ba. Haka nan masu jin abinda aka aiko Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da shi na ilimi da kuma shiriya. Na farko: Malami wanda ya fahimci Addinin Allah, mai aiki da iliminsa, mai sanar da waninsa; shi a matsayin ƙasa ce mai tsarki wacce ta sha ruwa sai ta amfana ita akan kanta, kuma ta tsirar sai ta amfani waninta. Na biyu: Mai haddace ilmi sai dai ba shi da fahimta da kuma istinbaɗi, shi ya tara ilimi, ya dilmiyar da lokacinsa a cikin hakan, sai dai cewa shi bai yi aiki da nafilfilinsa ba, ko bai fahimci abinda ya tara ba; to shi ala ce ga waninsa, kuma a matsayin ƙasa ce wacce ruwa ba ya tabbata a cikinta ballantana mutane su amfana da shi. Na uku: Wanda yake jin ilimi ba ya haddace shi, ba kuma ya aiki da shi, kuma ba ya ciratarsa ga waninsa; to shi a matsayin ƙasar gishiri ce ko ƙasa mai santsi wacce babu tsirrai a cikinta kuma ba ta karɓar ruwa ko tana ɓata shi ga waninta.
Fa’idoji
- Bayanin falalar neman ilimi da sanar da shi, da gargaɗarwa daga bijira daga garesu.
- Buga misalai dan kusanto da ma'anoni ga mutane.
- AlƘurɗubi ya ce: Kamar yadda cewa girgije yana raya mataccen gari haka nan ilimummukan Addini suna raya matacciyar zuciya, sannan ya kamanta masu jinsa da ƙasa mai banbancin abinda girgijen yake saukar wa na ruwa a kanta.
- Mutane matakai ne a karɓar ilimin shari'a.
Madogara
صحيح البخاري (1/ 27) (79).
صحيح مسلم (4/ 1787) (2282).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 464).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (2/ 294).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (2/ 950).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «مَنْ نَفَّسَ عَنْ مُؤْمِنٍ كُرْبَةً مِنْ كُرَبِ الدُّنْيَا نَفَّسَ اللهُ عَنْهُ كُرْبَةً مِنْ كُرَبِ يَوْمِ الْقِيَامَةِ، وَمَنْ يَسَّرَ عَلَى مُعْسِرٍ يَسَّرَ اللهُ عَلَيْهِ فِي الدُّنْيَا وَالْآخِرَةِ، وَمَنْ سَتَرَ مُسْلِمًا سَتَرَهُ اللهُ فِي الدُّنْيَا وَالْآخِرَةِ، وَاللهُ فِي عَوْنِ الْعَبْدِ مَا كَانَ الْعَبْدُ فِي عَوْنِ أَخِيهِ، وَمَنْ سَلَكَ طَرِيقًا يَلْتَمِسُ فِيهِ عِلْمًا سَهَّلَ اللهُ لَهُ بِهِ طَرِيقًا إِلَى الْجَنَّةِ، وَمَا اجْتَمَعَ قَوْمٌ فِي بَيْتٍ مِنْ بُيُوتِ اللهِ يَتْلُونَ كِتَابَ اللهِ وَيَتَدَارَسُونَهُ بَيْنَهُمْ إِلَّا نَزَلَتْ عَلَيْهِمِ السَّكِينَةُ، وَغَشِيَتْهُمُ الرَّحْمَةُ، وَحَفَّتْهُمُ الْمَلَائِكَةُ، وَذَكَرَهُمُ اللهُ فِيمَنْ عِنْدَهُ، وَمَنْ بَطَّأَ بِهِ عَمَلُهُ لَمْ يُسْرِعْ بِهِ نَسَبُهُ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya yayewa wani mumini wani baƙin ciki daga baƙin cikin duniya Allah Zai yaye masa wani baƙin ciki daga baƙin cikin ranar alƙiyama, wanda ya yalwatawa wanda yake cikin matsuwa to Allah Zai yalwata masa a duniya da lahira, wanda ya suturta wani musulmi Allah Zai suturta shi a duniya da lahira, Allah Yana cikin taimakon bawa matuƙar bawan yana cikin taimakon ɗan'uwansa, wanda ya bi wata hanya yana neman Ilimi a cikinta to Allah Zai sawwaƙe masa hanyar shiga aljanna da ita, kuma wasu mutane basu taru ba a wani ɗaki daga cikin ɗakunan Allah suna karanta littafin Allah kuma suna dirasarsa a tsakaninsu sai nutsuwa ta saukar musu, kuma rahama ta lullubesu, mala'iku sun kewayesu, kuma Allah Ya ambacesu a cikin wadanda ke tare da shi, wanda aikinsa ya jinkirtar da shi to nasabarsa bazata gaggauto da shi ba".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa sakamakon musulmi a wurin Allah yana daga jinsin abinda musulmi yake aikata shi ne tare da musulmai; wanda ya yaye ya gusar ya yayewa wani mumini wani baƙin ciki da tsanani daga baƙƙan cikin duniya, Allah Zai yi masa sakayya da cewa Zai Yaye masa wani baƙin ciki daga baƙƙan cikin ranar alƙiyama. Wanda ya yalwatawa wanda ke ciki matsi ya kuma sawwaƙa masa ya gusar da matsinsa, Allah Zai yalwata masa a duniya da lahira. Wanda ya suturta wani musulmi kamar idan ya tsinkaya daga gare shi akan abinda bayyanar da shi ba ya kamata na tuntuɓe da kurakurai, Allah Zai suturta shi a duniya da lahira. Allah Yana kasancewa Mai taimako ga bawanSa, muddin dai bawan ya kasance mai tafiya ne akan taimakon ɗan uwansa a maslahohinsa na Addini da duniya, taimako yana kasancewa ne da addu'a da jiki da dukiya da kuma wanin hakan. Wanda ya yi tafiya zuwa tabbatar da wani ilimi na shari'a, yana mai nufin fuskar Allah - Maɗaukakin sarki - da shi; to Allah Zai sawwaƙa masa hanya zuwa aljanna da shi. Wasu mutane ba su taba taruwaba a wani ɗaki daga cikin ɗakunan Allah (Msallatai), suna karanta littafin Allah kuma suna mudarasarsa a tsakaninsu, sai nutsuwa ta saukar musu, rahamar Allah ta gamesu ta lulluɓesu, kuma mala'iku sun kewayesu, Allah Ya yi yabo a garesu a cikin makusantan dake wajenSa, kuma ambatan Allah ga bawa a cikin jama'a maɗaukaka ya isa ɗaukaka. Wanda aikinsa ya kasance tauyayye ne, ba zai riskar da shi da darajar ma'abota ayyuka ba, to yana kamata kada ya dogara akan matsayin danganta da falalar iyayeba, ya taƙaita a aiki.
Fa’idoji
- Ibnu Daƙiƙi Eid ya ce: Wannan hadisi ne mai girma, mai tattarowa ne ga nau’ukan ilimummuka da ƙa'idoji da ladubba, a cikinsa a kwai falalar biyan buƙatun musulmai da anfanar da su da abinda ya sawwaƙa, na ilimi, ko dukiya, ko taimako, ko nuni da wata maslaha, ko nasiha, ko wanin haka.
- Kwaɗaitarwa a cikin yalwatawa wanda ke cikin matsi.
- Kwaɗaitarwa akan taimakon bawa musulmi, kuma Allah - Maɗaukakin sarki - Yana taimakon mai taimako gwargwadan taimakonsa ga ɗan uwansa.
- Yana daga cikin suturta musulmi: Rashin bibiyar al'aurarsa, haƙiƙa an ruwaito daga sashin magabata ya ce: Na riski wasu mutane basu da wasu aibuka, sai suka ambaci aibukan mutane, sai mutane suka ambata musu aibukansu, kuma na riski wasu mutane sun kasance suna da aibuka, sai suka kame daga aibukan mutane, sai aka manta da aibukansu.
- Barin munkari da rashin canja shi bai zama daga lazimtar suturta mutane ba, domin in ya canja ya suturta, wannan a cikin haƙƙin wanda ba’a san shi da ɓarna ba da kuma zarcewa a cikin shisshigi ba, wanda aka san shi da hakan to shi ba'a son suturta shi, kai za'a kai al'amarinsa zuwa ga hukuma, idan bai ji tsoron ɓarna ba daga hakan; hakan domin suturta shi zai ruɗar da shi akan ɓarnar, kuma zai sa shi ƙarfin hali akan cutar da bayin Allah, kuma zai sa waninsa ma ƙarfin hali daga ma'abota sharri da tsaurin kai.
- Kwaɗaitarwa akan neman ilimi da karatun alƙur'ani da mudararsa.
- Nawawi ya ce: A cikin wannan akwai dalilin taruwa akan karatun alƙur'ani a cikin masallatai... an riskar da masallaci a tabbatar da wannan falalar, taruwa a cikin wata makaranta ko zaman dako da makancin su in Allah - Maɗaukakin sarki - Ya so.
- Sakayya kawai Allah Ya jeranta ne akan ayyuka ba'a kan dangantaka ba.
Madogara
صحيح مسلم (4/ 2074) (2699).
التحفة الربانية، لإسماعيل الأنصاري (ص82).
الأحاديث الأربعون النووية وعليها الشرح الموجز المفيد، لعبد الله المحسن (ص69).
شرح الأربعين النووية ، لابن عثيمين (ص355).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن معاوية رضي الله عنه قال: سمعت النبي صلى الله عليه وسلم يقول: «مَنْ يُرِدِ اللهُ بِهِ خَيْرًا يُفَقِّهْهُ فِي الدِّينِ، وَإِنَّمَا أَنَا قَاسِمٌ، وَاللهُ يُعْطِي، وَلَنْ تَزَالَ هَذِهِ الْأُمَّةُ قَائِمَةً عَلَى أَمْرِ اللهِ، لَا يَضُرُّهُمْ مَنْ خَالَفَهُمْ، حَتَّى يَأْتِيَ أَمْرُ اللهِ».
Daga Mu’awiya - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa; Wanda Allah yake nufin shi da alheri sai ya fahimtar da shi addini to, Ni dai mai rabawa ne, Allah ne Yake bayarwa, wannan al’ummar ba za ta gushe ba tana tsaye akan al’amarin Allah, wanda ya saɓa musu ba zai cutar da su ba, har al’amarin Allah ya zo.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agare shi yana ba da labarin cewa wanda Allah Ya nufe shi da alheri, to, sai ya azurta shi da fahimta a addininSa tsarki ya tabbata a gare shi. Kuma shi [Annabi] tsira da aminci su tabbata a agare shi Mai rabawa ne, yana raba abin da Allah Ya ba shi na arziki da ilimi da wanin haka, Kuma hakikanin wanda yake bayarwar shi ne Allah, amma duk wanda ba shi ba, to, su sabubba ne, ba sa anfanarwa sai da izinin Allah, Kuma lalle wannan al’ummar ba za ta gushe a kan al’amarin Allah ba, wanda ya saɓa musu ba zai taba cutar da su ba , har ƙiyama ta tashi.
Fa’idoji
- Girma da falalar ilimin addini, da koyon shi da kuma kwaɗaitarwa a kansa.
- Tsayuwa a kan gaskiya tabbace yake a cikin wannan al’ummar, idan wata jama'a ta kauce sai wata ta ɗauka.
- Fahimtar addini yana daga cikin nufatar Allah maɗaukaki na alheri ga bawansa.
- Annabi tsara da amincin Allah su tabbata a gare shi kawai yana bayarwa ne da umarnin Allah da ganin damarSa, shi ba ya mallakar komai.
Madogara
صحيح البخاري (1/ 25) (71).
صحيح مسلم (2/ 718) (1037).
توضيح الأحكام من بلوغ المرام، للبسام (7/ 485).
منحة العلام في شرح بلوغ المرام، لعبد الله الفوزان (10/ 324).
فتح ذي الجلال والإكرام، لابن عثيمين (6/ 424).
سبل السلام بشرح بلوغ المرام، للصنعاني (2/ 688).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ أَبِي أُمَامَةَ البَاهِلِيِّ رَضيَ اللهُ عنه قَالَ: ذُكِرَ لِرَسُولِ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ رَجُلاَنِ أَحَدُهُمَا عَابِدٌ وَالآخَرُ عَالِمٌ، فَقَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «فَضْلُ العَالِمِ عَلَى العَابِدِ كَفَضْلِي عَلَى أَدْنَاكُمْ»، ثُمَّ قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «إِنَّ اللَّهَ وَمَلاَئِكَتَهُ وَأَهْلَ السَّمَوَاتِ وَالأَرَضِينَ حَتَّى النَّمْلَةَ فِي جُحْرِهَا وَحَتَّى الحُوتَ لَيُصَلُّونَ عَلَى مُعَلِّمِ النَّاسِ الخَيْرَ».
Daga Abu Umama al-Bahili - Allah Ya yarda da shi - ya ce: An ambatawa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - wasu mutane biyu ɗayansu mai ibada ne ɗayan kuma malami ne, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: «Falalar malami akan mai ibada kamar falalata ne akan wanda ke ƙasanku», sannan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Lallai Allah da mala'ikunSa da waɗanda ke sammai da ƙassai har tururuwa a cikin raminta kai har kifi suna addu'a ta alheri ga wanda yake koyar da mutane alheri».
Tirmizi ne ya ruwaito shiDarajaHasan ne da wani Sanadin
Sharhi
An ambatawa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - wasu mutane biyu ɗayansu mai ibada ne, ɗayan kuma malamai ne, wanene yafi a cikinsu?
Sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Falalar masanain ilimummukan shari'a mai yin aiki da su kuma mai koyar da su akan mai yin ibada wanda ya kaɗaita ga ibada tare da da cewa ya san abinda ya wajaba akansa na ilimi kamar falalarsa ne - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da kuma ɗaukakarsa akan mafi koma baya daga cikin sahabbai Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya bayyana sababin hakan da cewa Allah - tsarki ya tabbatar maSa -, da mala'ikunSa cikin maɗauka al'arshi, da waɗanda ke cikin sammai na sauran mala'iku, da ma'abota ƙasa na aljanu da mutane da dukkanin dabbobi, har tururuwa a gidanta a cikin ƙasa, har kifin da ke cikin kogi; dan ya haɗa dabbobin sarari (tudu) da kogi, dukkanin waɗannan sunayin addu'a ta alheri ga wanda yake koyar da mutane ilimummukan Addinin da a cikinsu akwai tsiran mutane da kuma rabautarsu.
Fa’idoji
- Daga cikin usuluban kira zuwa ga Allah akwai kwaɗaitarwa da kuma buga misalai.
- Girman ɗaukakar malaman da suka koyi ilimi kuma suka tsaya da haƙƙinsa na aiki da kuma da'awa.
- Kwaɗaitarwa akan girmama malamai da ɗaliban ilimi da kuma yi musu addu'a.
- Kwaɗaitarwa akan koyar da mutane alheri; domin shi ne sababin tsirarsu da kuma azirtarsu.
Madogara
سنن الترمذي (4/ 416) (2685).
كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (16/ 481).
مرقاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح، لعلي القاري (1/ 298).
فيض القدير شرح الجامع الصغير، للمناوي (4/ 432).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 469).
تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص758).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (2/ 954).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن أبي هريرة رضي الله عنه عن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: «النَّاسُ مَعَادِن كَمَعَادِن الذَّهَب وَالفِضَّة، خِيَارُهُم فِي الجَاهِلِيَّة خِيَارُهُم فِي الإِسْلاَم إِذَا فَقُهُوا، والأَرْوَاحُ جُنُودٌ مُجَنَّدَة، فَمَا تَعَارَفَ مِنْهَا ائتَلَفَ، وَمَا تَنَاكَرَ مِنْهَا اخْتَلَفَ».
وعن أبي هريرة رضي الله عنه قال: قال رسول الله -صلى الله عليه وسلم:
«تَجِدُون النَّاسَ مَعَادِن: خِيَارُهُم فِي الجَاهِليَّة خِيَارُهُم فِي الإِسْلاَم إِذَا فَقِهُوا، وَتَجِدُون خِيَار النَّاس فِي هَذَا الشَّأْن أَشَدُّهُم كَرَاهِيَة لَه، وَتَجِدُون شَرَّ النَّاس ذَا الوَجْهَين، الَّذِي يَأْتِي هَؤُلاَء بِوَجه، وَهَؤُلاَء بِوَجْه».
Daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- daga Manzon Allah SAW ya ce: "Mutane Kamar Ma'adanan Zinare da Azurfa ne, Mafifitanku a Jahiliyya sune Mafifitanku a musulunci idan Sukai Ilimi, Kuma Rayuka Kamar Rundunar yaki ce, duk wanda suka San juna sai su Saba, wanda kuma suka saba kuma sai suki jituwa" kuma an rawaito daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- Manzon Allah ya ce: "Zaku samu Mutane Kamar ne, Mafifitanku a Jahiliyya sune Mafifitanku a musulunci idan Sukai Ilimi, Kumazaku samu zababbu a cikin Mutane a wannan Al-amari su ne Mafiya tsananin kinsa, kuma zaku samu Mafi Sharrin Mutane Masu fuska biyu, wanda zai zowa wadan nan da wata fuska kuma wadan nan da wata Fuskar daban"
Buhari da Muslim suka rawaito shi da ruwayoyin saDarajaIngantacce ne duka Riwayoyin nasa guda biyun
Madogara
- صحيح البخاري، للإمام محمد بن إسماعيل البخاري، تحقيق محمد الناصر، دار طوق النجاة.
- صحيح مسلم، للإمام مسلم بن الحجاج، تحقيق محمد فؤاد عبد الباقي، دار إحياء التراث العربي.
- بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين؛ تأليف سليم الهلالي، دار ابن الجوزي- الطبعة الأولى1418ه
- نزهة المتقين شرح رياض الصالحين؛ تأليف د. مصطفى الخِن وغيره، مؤسسة الرسالة-بيروت، الطبعة الرابعة عشر، 1407هـ.
- شرح رياض الصالحين؛ للشيخ محمد بن صالح العثيمين، مدار الوطن، الرياض، 1426هـ.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comKowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com