Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Lallai daga cikin alamomin tashin Alkiyama, za’a dauke ilimi, jahilci zai yi yawa, zina zata yawaita, za’a yawaita shan giya, maza za su yi karanci, mata za su yi yawa, har sai ya kasance mata hamsin mutum daya ne yake kula da su

عَنْ أَنَسٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، قَالَ: لَأُحَدِّثَنَّكُمْ حَدِيثًا سَمِعْتُهُ مِنْ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ لاَ يُحَدِّثُكُمْ بِهِ أَحَدٌ غَيْرِي: سَمِعْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: «إِنَّ مِنْ أَشْرَاطِ السَّاعَةِ أَنْ يُرْفَعَ العِلْمُ، وَيَكْثُرَ الجَهْلُ، وَيَكْثُرَ الزِّنَا، وَيَكْثُرَ شُرْبُ الخَمْرِ، وَيَقِلَّ الرِّجَالُ، وَيَكْثُرَ النِّسَاءُ حَتَّى يَكُونَ لِخَمْسِينَ امْرَأَةً القَيِّمُ الوَاحِدُ».
Daga Anas - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Wallahi zan zantar daku wani hadisin da na ji shi daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - wanina ba zai zantar daku shi ba: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Lallai daga cikin alamomin tashin Alkiyama, za’a dauke ilimi, jahilci zai yi yawa, zina zata yawaita, za’a yawaita shan giya, maza za su yi karanci, mata za su yi yawa, har sai ya kasance mata hamsin mutum daya ne yake kula da su".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa daga alamomin kusantowar tashin Alkiyama dauke ilimi na shari'a, wannan kuwa ta hanyar mutuwar malamai ne. Sakamakon hakan jahilci zai yawaita ya yadu, zina da alfasha zasu yadu, shan giya zai yawaita, adadin maza zai karanta , adadin mata zai karu; har yakasance namiji daya zai tsayawa mata hamsin ga al'amuransu kuma zai jibinci maslahohinsu.

Fa’idoji
  1. Bayanin wasu daga cikin alamomin Alkiyama.
  2. Sanin lokacin Alkiyama yana daga al'amuran gaibu wadanda Allah ne kadai ya san su.
  3. Kwadaitarwa akan neman ilimin shari'a kafin a rasa shi..
Madogara

صحيح البخاري (7/ 37) (5231)، صحيح مسلم (4/ 2056) (2671)، فتح الباري لابن حجر (9/ 330)، عمدة القاري شرح صحيح البخاري (20/ 213).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
RAYUWAR BARZAHU

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com