Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Wanda Allah yake nufin shi da alheri sai ya fahimtar da shi addini

عن معاوية رضي الله عنه قال: سمعت النبي صلى الله عليه وسلم يقول: «مَنْ يُرِدِ اللهُ بِهِ خَيْرًا يُفَقِّهْهُ فِي الدِّينِ، وَإِنَّمَا أَنَا قَاسِمٌ، وَاللهُ يُعْطِي، وَلَنْ تَزَالَ هَذِهِ الْأُمَّةُ قَائِمَةً عَلَى أَمْرِ اللهِ، لَا يَضُرُّهُمْ مَنْ خَالَفَهُمْ، حَتَّى يَأْتِيَ أَمْرُ اللهِ».
Daga Mu’awiya - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa; Wanda Allah yake nufin shi da alheri sai ya fahimtar da shi addini to, Ni dai mai rabawa ne, Allah ne Yake bayarwa, wannan al’ummar ba za ta gushe ba tana tsaye akan al’amarin Allah, wanda ya saɓa musu ba zai cutar da su ba, har al’amarin Allah ya zo.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agare shi yana ba da labarin cewa wanda Allah Ya nufe shi da alheri, to, sai ya azurta shi da fahimta a addininSa tsarki ya tabbata a gare shi. Kuma shi [Annabi] tsira da aminci su tabbata a agare shi Mai rabawa ne, yana raba abin da Allah Ya ba shi na arziki da ilimi da wanin haka, Kuma hakikanin wanda yake bayarwar shi ne Allah, amma duk wanda ba shi ba, to, su sabubba ne, ba sa anfanarwa sai da izinin Allah, Kuma lalle wannan al’ummar ba za ta gushe a kan al’amarin Allah ba, wanda ya saɓa musu ba zai taba cutar da su ba , har ƙiyama ta tashi.

Fa’idoji
  1. Girma da falalar ilimin addini, da koyon shi da kuma kwaɗaitarwa a kansa.
  2. Tsayuwa a kan gaskiya tabbace yake a cikin wannan al’ummar, idan wata jama'a ta kauce sai wata ta ɗauka.
  3. Fahimtar addini yana daga cikin nufatar Allah maɗaukaki na alheri ga bawansa.
  4. Annabi tsara da amincin Allah su tabbata a gare shi kawai yana bayarwa ne da umarnin Allah da ganin damarSa, shi ba ya mallakar komai.
Madogara

صحيح البخاري (1/ 25) (71). صحيح مسلم (2/ 718) (1037). توضيح الأحكام من بلوغ المرام، للبسام (7/ 485). منحة العلام في شرح بلوغ المرام، لعبد الله الفوزان (10/ 324). فتح ذي الجلال والإكرام، لابن عثيمين (6/ 424). سبل السلام بشرح بلوغ المرام، للصنعاني (2/ 688).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
FALALAR ILIMI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com