Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

‌Falalar malami akan mai ibada kamar falalata ne akan wanda ke ƙasanku

عَنْ أَبِي أُمَامَةَ البَاهِلِيِّ رَضيَ اللهُ عنه قَالَ: ذُكِرَ لِرَسُولِ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ رَجُلاَنِ أَحَدُهُمَا عَابِدٌ وَالآخَرُ عَالِمٌ، فَقَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «فَضْلُ العَالِمِ عَلَى العَابِدِ كَفَضْلِي عَلَى أَدْنَاكُمْ»، ثُمَّ قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «إِنَّ اللَّهَ وَمَلاَئِكَتَهُ وَأَهْلَ السَّمَوَاتِ وَالأَرَضِينَ حَتَّى النَّمْلَةَ فِي جُحْرِهَا وَحَتَّى الحُوتَ لَيُصَلُّونَ عَلَى مُعَلِّمِ النَّاسِ الخَيْرَ».
Daga Abu Umama al-Bahili - Allah Ya yarda da shi - ya ce: An ambatawa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - wasu mutane biyu ɗayansu mai ibada ne ɗayan kuma malami ne, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: «‌Falalar malami akan mai ibada kamar falalata ne akan wanda ke ƙasanku», sannan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «‌Lallai Allah da mala'ikunSa da waɗanda ke sammai da ƙassai har tururuwa a cikin raminta kai har kifi suna addu'a ta alheri ga wanda yake koyar da mutane alheri».
Tirmizi ne ya ruwaito shiDarajaHasan ne da wani Sanadin
Sharhi

An ambatawa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - wasu mutane biyu ɗayansu mai ibada ne, ɗayan kuma malamai ne, wanene yafi a cikinsu? Sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Falalar masanain ilimummukan shari'a mai yin aiki da su kuma mai koyar da su akan mai yin ibada wanda ya kaɗaita ga ibada tare da da cewa ya san abinda ya wajaba akansa na ilimi kamar falalarsa ne - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da kuma ɗaukakarsa akan mafi koma baya daga cikin sahabbai Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya bayyana sababin hakan da cewa Allah - tsarki ya tabbatar maSa -, da mala'ikunSa cikin maɗauka al'arshi, da waɗanda ke cikin sammai na sauran mala'iku, da ma'abota ƙasa na aljanu da mutane da dukkanin dabbobi, har tururuwa a gidanta a cikin ƙasa, har kifin da ke cikin kogi; dan ya haɗa dabbobin sarari (tudu) da kogi, dukkanin waɗannan sunayin addu'a ta alheri ga wanda yake koyar da mutane ilimummukan Addinin da a cikinsu akwai tsiran mutane da kuma rabautarsu.

Fa’idoji
  1. Daga cikin usuluban kira zuwa ga Allah akwai kwaɗaitarwa da kuma buga misalai.
  2. Girman ɗaukakar malaman da suka koyi ilimi kuma suka tsaya da haƙƙinsa na aiki da kuma da'awa.
  3. Kwaɗaitarwa akan girmama malamai da ɗaliban ilimi da kuma yi musu addu'a.
  4. Kwaɗaitarwa akan koyar da mutane alheri; domin shi ne sababin tsirarsu da kuma azirtarsu.
Madogara

سنن الترمذي (4/ 416) (2685). كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (16/ 481). مرقاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح، لعلي القاري (1/ 298). فيض القدير شرح الجامع الصغير، للمناوي (4/ 432). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 469). تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص758). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (2/ 954).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
FALALAR ILIMI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com