عَنْ زِيَادِ بْنِ لَبِيدٍ رضي الله عنه قَالَ: ذَكَرَ النَّبِيُّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ شَيْئًا، فَقَالَ: «ذَاكَ عِنْدَ أَوَانِ ذَهَابِ الْعِلْمِ» قُلْتُ: يَا رَسُولَ اللَّهِ، وَكَيْفَ يَذْهَبُ الْعِلْمُ، وَنَحْنُ نَقْرَأُ الْقُرْآنَ وَنُقْرِئُهُ أَبْنَاءَنَا وَيُقْرِئُهُ أَبْنَاؤُنَا أَبْنَاءَهُمْ إِلَى يَوْمِ الْقِيَامَةِ؟ قَالَ: «ثَكِلَتْكَ أُمُّكَ زِيَادُ، إِنْ كُنْتُ لَأُرَاكَ مِنْ أَفْقَهِ رَجُلٍ بِالْمَدِينَةِ، أَوَلَيْسَ هَذِهِ الْيَهُودُ وَالنَّصَارَى يَقْرَؤونَ التَّوْرَاةَ وَالْإِنْجِيلَ، لَا يَعْمَلُونَ بِشَيْءٍ مِمَّا فِيهِمَا؟!».
Daga Ziyad Dan Labid - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ambaci wani abu, sai ya ce: "Wannan a lokacin tafiyar ilimi kenan" Na ce: Ya Manzon Allah, ta yaya ilimi zai tafi, alhali mu muna karanta Alkur’ani kuma, muna karantar da 'ya'yanmu shi, kuma 'ya'yanmu suna karantar da 'ya'yansu har zuwa ranar Alkiyama ? Ya ce: "Mahaifiyarka ta yi wabinka Ziyad, na kasance ina ganinka daga mafi fahimtar mutane a Madina, shin wadannan Yahudawan da Nasaran ba sa karanta Attaura da Injila, ba sa aiki da wani abinda ke cikinsu?!".
Ibnu Majah ne ya ruwaito shiDarajaIngantacce ne ta wani bangaren
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agar shi - ya kasance a zaune tsakanin sahabbansa, sai ya ce:: Wannan lokacin da za'a dauke a zare ilimi ne daga mutane. Sai Ziyad Dan Labid Al-Ansary - Allah Ya yarda da shi - ya yi mamaki kuma ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, Sai ya ce; Ta yaya za'a dauke ilimi a sarayar da shi daga garemu?! Alhali mun karanta Alkur’ani mun haddaceshi; na rantse da Allah sai mun karantashi, kuma mun karantar da matanmu da 'ya'yanmu shi, da 'ya'yan 'ya'yanmu, Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce yana mai mamaki: Mahaifiyarka ta rasaka ya Ziyad! na kasance ina lissafaka daga malaman mutanen Madina! Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya bayyana masa: Cewa rasa ilimi bai zamo da rasa Alkur’ani ba; saidai rasa ilimi (yana kasancewa ne) da rashin aiki da shi, Wannan Attaurar da Injilar dake wajen Yahudawa da Nasara; a tare da haka ba ta anfanesu ba, kuma ba su anfana da manufarsu ba; shi ne aiki da abinda suka sani.
Fa’idoji
- Samun kwafin Alkur’ani da littattafai a hannun mutane ba ya anfani ba tare da aiki da su ba.
- Dauke ilimi yana kasancewa da wasu al'amura, daga cikin su (akwai): Mutuwar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, da mutuwar malamai, da barin aiki da ilimi.
- Daga alamomin Alkiyama (akwai) tafiyar ilimi da barin aiki da shi.
- Kwadaitarwa akan aiki da ilimi domin shi ne abin nufi.
Madogara
سنن ابن ماجه (5/ 172) (4048)، سنن الترمذي (4/ 328) (2653)، مسند أحمد (39/ 417) (23990)، الكاشف عن حقائق السُّنن (2/721)، المفهم (6/705)، مشارق الأنوار الوهاجة (2/146)، مرشد ذوي الحجا والحاجة إلى سنن ابن ماجه والقول المكتفى على سنن المصطفى (24/ 274).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ جَابِرِ بْنِ عَبْدِ اللَّهِ رضي الله عنهما أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «لَا تَعَلَّمُوا الْعِلْمَ لِتُبَاهُوا بِهِ الْعُلَمَاءَ، وَلَا لِتُمَارُوا بِهِ السُّفَهَاءَ، وَلَا تَخَيَّرُوا بِهِ الْمَجَالِسَ، فَمَنْ فَعَلَ ذَلِكَ، فَالنَّارُ النَّارُ».
Daga Jabir Dan Abdullahi - Allah Ya yarda da su - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Kada ku nemi ilimi dan ku yi wa malamai alfahari da shi, ko ku yi musu da wawaye da shi, kuma kada ku nufi bijiro da shi a zababbun majalisai, wanda ya aikata haka to wuta wuta".
Ibnu Majah ne ya ruwaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya gargadar da wanda ya nemi ilimi dan yi wa malamai alfahari, da bayyanar da cewa ni malami ne irinku, ko dan su yi magana da jayayya da wawaye masu karancin hankali, ko a nemi ilimi dan a bijiro a majalisai, a gabatar da shi akan waninsa a cikinsu. Wanda ya aikata haka; to cewa shi ya cancanci wuta da riyarsa da rashin tsarkake niyyarsa a cikin neman ilimi saboda Allah.
Fa’idoji
- Narko mai tsanani da wuta ga wanda ya nemi ilimi dan ya yi alfahari da shi ko ya yi jayayya da shi ko ya bijirowa majalisai da shi, da makamancin haka.
- Muhimmancin tsarkake niyya ga wanda ya nemi ilimi ya kuma sanar da shi.
- Niyya ita ce tushen ayyuka, kuma akanta ne sakamakon ayyuka yake kasancewa.
Madogara
سنن ابن ماجه (1/ 170) (254)، مرشد ذوي الحجا والحاجة (2/378)، مشارق الأنوار الوهاجة ومطالع الأسرار البهاجة في شرح سنن الإمام ابن ماجه (4/ 482).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه أَنَّ رَسُولَ اللهِ صلى الله عليه وسلم قَالَ: «إِذَا مَاتَ الْإِنْسَانُ انْقَطَعَ عَنْهُ عَمَلُهُ إِلَّا مِنْ ثَلَاثَةٍ: إِلَّا مِنْ صَدَقَةٍ جَارِيَةٍ، أَوْ عِلْمٍ يُنْتَفَعُ بِهِ، أَوْ وَلَدٍ صَالِحٍ يَدْعُو لَهُ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -: Lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Idan mutum ya rasu akin sa ya yanke sai dai daga abu uku: Sadaka mai gudana, ko wani ilimin da ake anfanuwa da shi, ko ɗa na gari da ya ke masa addu'a".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa aikin mamaci yana yankewa da rasuwarsa,, kyawawan ayyuka basa samunsa bayan mutuwnrsa sai a waɗannan ukun; dan kasancewarsa ya zama sababinsu:
Na farko: Sadakar da ladanta yake gudana kuma yake dawwama, ba mai yankewa ba, kamar waƙafi, da gina masallatai, da haƙa rijiyoyi, da wanin hakan.
Na biyu: Ilimin da mutane suke anfanuwa da shi, kamar wallafa littattafan ilimi, ko kamar ya koyar da wani mutum, sai wannan mutumin ya yaɗa wannan ilimin bayan mutuwarsa.
Na uku: Ɗa na gari mumini da zai yi masa addu'a.
Fa’idoji
- Ma'abota ilimi sun haɗu akan cewa daga abinda yake riskar mutum bayan mutuwarsa na lada: Sadaka mai gudana, da ilimin da ake anfanuwa da shi, da addu'a, kuma ya zo a cikin wasu Hadisan daban: Hajji kuma.
- An keɓanci waɗannan ukun da ambato a cikin wannan Hadisin; domin sune tushen alheri, kuma mafi rinjayar abinda ma'abota falala suke nufin wanzuwarsa bayansu.
- Dukkan ilimin da ake anfanuwa da shi to shi lada yana samuwa gare shi, sai dai ƙololuwarsu shi ne ilimi na shari'a da ilimummuka masu ƙarfafarsa.
- Ilimi mafi anfani shi ne waɗannan ukun; domin ilimi mutumin da yake neman saninsa yana anfanuwa da shi, akwai kiyaye shari'a a cikin ilimi, akwai anfanar halitta a gamewa, shi ne mafi ƙunsa kuma mafi gamewa; domin shi yana neman iliminka samamme a cikin rayuwarka kuma samamme bayan mutuwarka.
- Kwaɗaitarwa akan tarbiyyar yara salihai; su ne waɗanda suke anfanar iyayensu a lahira, daga anfanar su suna yi musu addu'a.
- Kwaɗaitarwa akan kyautatawa mahaifa bayan mutuwarsu, shima yana daga aikin alherin ɗa zai anfana da shi.
- Addu'a tana anfanar mamaci koda daga wanin ɗa ne, sai dai ankeɓanci ɗa da ambato; domin shi ne wanda yake ci gaba a addu'a ga mutum a galibi har zuwa mutuwarsa.
Madogara
صحيح مسلم (3/ 1255) (1631)، البحر المحيط الثجاج في شرح صحيح الإمام مسلم بن الحجاج (28/ 413).
Wannan hadisi a HadeethEnc.com