Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

ZIKIRAN SALLAH

Hadisai 17

Ya Allah ni ina neman tsarinka daga azabar kabari, da azabar wuta, da fitinar rayuwa da mutuwa, da fitinar Mai yawan yawo makaryaci (Jujal)

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: كَانَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَدْعُو وَيَقُولُ: «اللَّهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ مِنْ عَذَابِ القَبْرِ، وَمِنْ عَذَابِ النَّارِ، وَمِنْ فِتْنَةِ المَحْيَا وَالمَمَاتِ، وَمِنْ فِتْنَةِ المَسِيحِ الدَّجَّالِ». وفِي لَفْظٍ لِمُسْلِمٍ: «إِذَا فَرَغَ أَحَدُكُمْ مِنَ التَّشَهُّدِ الْآخِرِ، فَلْيَتَعَوَّذْ بِاللهِ مِنْ أَرْبَعٍ: مِنْ عَذَابِ جَهَنَّمَ، وَمِنْ عَذَابِ الْقَبْرِ، وَمِنْ فِتْنَةِ الْمَحْيَا وَالْمَمَاتِ، وَمِنْ شَرِّ الْمَسِيحِ الدَّجَّالِ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana yin addu'a yana cewa: "Ya Allah ni ina neman tsarinka daga azabar kabari, da azabar wuta, da fitinar rayuwa da mutuwa, da fitinar Mai yawan yawo makaryaci (Jujal)". A cikin wani lafazin na Muslim: "Idan dayanku ya gama tahiyar karshe, to ya nemi tsarin Allah daga abubuwa hudu: Daga azabar kabari, da fitinar rayuwa da mutuwa, da sharrin Mai yawan yawo makaryaci (Jujal).
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana neman tsarin Allah daga abubuwa hudu bayan tahiyar karshe kuma kafin sallama a sallah, ya kuma umarcemu mu nemi tsarin Allah daga garesu, Na farko: Daga azabar kabari. Na biyu: Daga azabar wuta hakan a ranar Alkiyama . Na uku: Daga fitinar rayuwa na sha'awowin duniya haramtattu da kuma shubuhohi masu batarwa, da kuma fitinar mutuwa, wato lokacin fitar rai, na karkacewa daga musulunci ko sunna, ko fitinar kabari kamar tambayar Mala'iku biyu. Na hudu: Fitinar mai yawan yawo makaryaci (Dajjal) wanda zai fito a karshen zamani, Allah zai jarrabi bayinSa da shi, ya kebance shi da ambato dan girman fitinarsa da batarwarsa.

Fa’idoji
  1. Wanan neman tsarin yana daga muhimman addu'o'i kuma gamammu, dan abinda suka kunsa na neman tsari daga sharrukan duniya da lahira.
  2. Tabbatar da azabar kabari kuma cewa ita gaskiya ce.
  3. Hadarin fitintinu da muhimmancin neman taimakon Allah da addu'a dan tsira daga garesu.
  4. Tabbatar da fitowar Dujal da girman fitinarsa.
  5. An so yin wannan addu'ar bayan tahiyar karshe.
  6. An so yin addu'a bayan aiki na gari.
Madogara

صحيح البخاري (2/ 99) (1377). صحيح مسلم (1/ 412) (588). الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري (1/ 172). تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، للبسام (ص212). خلاصة الكلام شرح عمدة الأحكام، لفيصل آل مبارك (ص96).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Ya Allah Ka nesanta tsakanina da kurakurai na kamar yadda Ka nesanta tsakanin mahudar rana da mafaɗarta

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: كَانَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، إِذَا كَبَّرَ فِي الصَّلَاةِ، سَكَتَ هُنَيَّةً قَبْلَ أَنْ يَقْرَأَ، فَقُلْتُ: يَا رَسُولَ اللهِ بِأَبِي أَنْتَ وَأُمِّي أَرَأَيْتَ سُكُوتَكَ بَيْنَ التَّكْبِيرِ وَالْقِرَاءَةِ، مَا تَقُولُ؟ قَالَ «أَقُولُ: اللهُمَّ بَاعِدْ بَيْنِي وَبَيْنَ خَطَايَايَ كَمَا بَاعَدْتَ بَيْنَ الْمَشْرِقِ وَالْمَغْرِبِ، اللهُمَّ نَقِّنِي مِنْ خَطَايَايَ كَمَا يُنَقَّى الثَّوْبُ الْأَبْيَضُ مِنَ الدَّنَسِ، اللهُمَّ اغْسِلْنِي مِنْ خَطَايَايَ بِالثَّلْجِ وَالْمَاءِ وَالْبَرَدِ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da aminci su tabbata a gare shi - ya kasance idan ya yi kabbara a sallah, sai ya yi shiru ɗan wani lokaci gabanin fara karatu, sai na ce: Ya manzon Allah, fansarka baba na da Baba ta, kana ganin shirun da kake yi tsakanin kabbara da karatu, me kake cewa? ya ce: Ina cewa: Ya Allah Ka nesanta tsakanina da kurakurai na kamar yadda Ka nesanta tsakanin mahudar rana da mafaɗarta, Ya Allah Ka tsaftace ni daga zunubaina kamar yadda ake tsaftace farar tufa daga datti. Ya Allah Ka wanke ni daga zunubai na da ruwan ƙanƙara kuma mai tsananin sanyi".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya yi kabbarar sallah yana yin shiru kaɗan kafin ya karanta fatiha, yana buɗe sallarsa da wasu daga addu'o'i a cikinta, daga abinda ya zo daga waɗannan addu'o'in faɗinsa: "Ya Allah Ka nesanta tsakanina da kurakurai na kamar yadda Ka nesanta tsakanin mahudar rana da mafaɗarta, Ya Allah Ka tsaftace ni daga kurakuraina kamar yadda ake tsaftace farar tufa daga datti, ya Allah Ka wanke ni daga zunubai na da ruwa da ƙanƙara da ruwa mai tsananin sanyi". Shi yana roƙon Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya nisantar da tsakaninsa da kurakurai da kada ya faɗa cikinsu, nisantarwa ta inda gamuwa ba zata ƙara faruwa tare da shi ba, kamar yadda babu haɗuwa tsakanin mahudar rana da mafaɗarta har abada, idan kuma ya faɗa cikinsu to Ya tsaftace su Ya kawar da su kamar yadda ake kawar da datti daga farin tufa, kuma Ya wanke shi daga kurakuransa Ya sanyaya horuwarsu da zafinsu, da waɗannan masu tsaftacewar masu sanyi: Ruwa, da kankara, da sanyi.

Fa’idoji
  1. Boye addu'ar buɗe sallah koda sallar ta kasance ta karatun bayyana ne.
  2. Kwaɗayin sahabbai - Allah Ya yarda da su - akan sanin halayen Manzo - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a motsinsa da shirunsa.
  3. Wasu sigogin daban sun zo na addu'ar buɗe sallah, abinda ya fi shi ne mutum ya bibiyi addu'o'in buɗe sallah da suka zo, kuma tabbatattu daga gare shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya zo da wannan wani lokaci, wani lokacin kuma ya zo da wannan.
Madogara

صحيح البخاري (1/ 149) (744). صحيح مسلم (1/ 419) (598). الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري (1/ 118). تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، للبسام (ص143). تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام، لابن عثيمين (2/ 186).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

bayan kowace sallah kada ka bar faɗin: Ya Allah Ka taimakeni akan ambatanKa da gode maKa da kyakkyawar ibadarKa

عَنْ مُعَاذِ بْنِ جَبَلٍ رضي الله عنه: أَنَّ رَسُولَ صَلَّى عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَخَذَ بِيَدِهِ، وَقَالَ: «يَا مُعَاذُ، وَاللَّهِ إِنِّي لَأُحِبُّكَ»، فَقَالَ: «أُوصِيكَ يَا مُعَاذُ لَا تَدَعَنَّ فِي دُبُرِ كُلِّ صَلَاةٍ تَقُولُ: اللَّهُمَّ أَعِنِّي عَلَى ذِكْرِكَ وَشُكْرِكَ وَحُسْنِ عِبَادَتِكَ».
Daga Mu'az Bin Jabal -Allah Ya yarda da shi -: Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya riƙe hannuna, sai ya ce: "Ya Mu'az, wallahi lallai ni ina sonka", sai ya ce: "Ina yi maka wasicci ya Mu'az bayan kowace sallah kada ka bar faɗin: Ya Allah Ka taimakeni akan ambatanKa da gode maKa da kyakkyawar ibadarKa".
Abu Dawud da Nasa'i haka Ahmad suka ruwaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya riƙe hannun Mu'aza - Allah Ya yarda da shi -, sai ya ce masa: Wallahi lallai ni ina sonka, kuma ina yi maka wasicci ya Mu'az a ƙarshen kowace sallah kada kabar faɗin: (Ya Allah Ka taimakeni akan ambatanKa) a kowace magana da aikin da zai kusanto da ni zuwa biyayya, (da godiyarKa) ta hanyar samun ni'imomi da tunkuɗe masifu, (da kyakkyawar bautarKa) ta hanyar yin ikhlasi ga Allah da bin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.

Fa’idoji
  1. Halaccin baiwa mutum labari da sonsa a lamarin Allah.
  2. An so yin wannan addu'ar a bayan kowace sallar farilla da nafila.
  3. A cikin yin addu'a da waɗannan lafuzan 'yan kaɗan (akwai) abbuwan nema a duniya da lahira.
  4. Daga fa'idojin soyayya a lamarin Allah yin wasicci da gaskiya da yi wa juna nasiha da taimakekeniya akan aikin alheri da tsoron Allah.
  5. Malam al-Ɗaibi ya ce: Ambatan Allah shi ne kan gaba a buɗewar ƙirji, godiyarSa kuma tsani ce na ni'imomi ababen amsawa, kyakkyawar ibada kuwa abar nema daga gare shi, shi ne nisantar abinda zai shagaltar da shi daga Allah - Maɗaukakin sarki -.
Madogara

سنن أبي داود (2/ 630) (1522). سنن النسائي (3/ 53) (1303). مسند أحمد (36/ 429) (22119). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 450). تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص259). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (3/ 264). كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (6/ 284). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 353).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Ya Allah ina neman tsari da yardarKa daga fushinKa, da kuma rangwaminKa daga uƙubarKa, kuma ina neman tsari da Kai daga gareKa ba zan iya ƙididdige yabo gareKa ba kamar yadda Ka yabi kanKa

عَنْ عَائِشَةَ رضي الله عنها قَالَتْ: فَقَدْتُ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ لَيْلَةً مِنَ الْفِرَاشِ فَالْتَمَسْتُهُ فَوَقَعَتْ يَدِي عَلَى بَطْنِ قَدَمَيْهِ وَهُوَ فِي الْمَسْجِدِ وَهُمَا مَنْصُوبَتَانِ، وَهُوَ يَقُولُ: «اللهُمَّ أَعُوذُ بِرِضَاكَ مِنْ سَخَطِكَ، وَبِمُعَافَاتِكَ مِنْ عُقُوبَتِكَ، وَأَعُوذُ بِكَ مِنْكَ لَا أُحْصِي ثَنَاءً عَلَيْكَ أَنْتَ كَمَا أَثْنَيْتَ عَلَى نَفْسِكَ».
Daga Nana Aisha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Na rasa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a wani dare a shinfiɗa sai na lalube shi sai hannuna ya faɗa akan cikin diga-digansa alhali shi yana cikin masallaci alhali su suna a kafe, alhali shi yana cewa: "Ya Allah ina neman tsari da yardarKa daga fushinKa, da kuma rangwaminKa daga uƙubarKa, kuma ina neman tsari da Kai daga gareKa ba zan iya ƙididdige yabo gareKa ba kamar yadda Ka yabi kanKa".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Na kasance ina barci a gefen Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai na rasashi da daddare, sai na laluba da hannayena gurin da ya kasance yake sallah a cikinsa a cikin ɗaki; sai gashi yana sujjada alhali diga-digansa suna a tsaye, sai gashi shi yana cewa: (Ina neman tsari) ina kamun ƙafa (da yardarKa daga fushinKa) akaina ko akan al'ummata, (kuma) ina neman tsari (da rangwaminKa) afuwarKa mai yawa (daga uƙubarKa), (Ina neman tsari daga gareKa) da siffofin kyawunKa daga siffofin ɗaukakarKa, inda ba mai fakewa daga gare Ka sai Kai, babu matserata kuma babu mafaka daga Allah sai dai zuwa gareShi, (Ba zan iya ƙididdige yabo a gareKa ba) ba zan iya kuma bazan kai ƙololuwa a lissafewa ba da kuma ƙirgawa ba saboda gajiyawata ba, ƙididdige ni'imarKa da kyautatawarKa kamar yadda Kake cancantarsa ba koda na yi ƙoƙari a hakan. (Kai kamar yadda Ka yabi kanKa) Kaine wanda Ka yi yabo akan zatinKa yabon da ya dace da Kai, waye yake da iko akan bada haƙƙin yabonKa?!

Fa’idoji
  1. An so waɗannan addu'o'in a cikin sujjada.
  2. Mirak ya ce: A cikin ɗaya daga riwayoyi al-Nasa'i: Ya kasance yana faɗin wannan addu'ar idan ya gama sallarsa ya koma makwancinsa.
  3. An so yabo ga Allah da siffofinSa da kuma roƙonSa da sunayenSa tabbatattu a cikin Littafi da Sunnah.
  4. A cikinsa akwai girmama Mahalicci a cikin ruku'u da sujjada.
  5. Halaccin neman tsari da siffofin Allah, kamar yadda neman tsari da zatinSa - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka - yake halatta.
  6. AlKhaɗɗabi ya ce: A cikin wannan maganar akwai ma’ana mai kyau, ita ce: Cewa shi haƙiƙa ya nemi tsarin Allah Ya tsare shi da yardarSa daga fushinSa, da kuma rangwaminSa daga uƙubarSa, yarda da fushi kishiyoyi ne masu fuskantar juna, haka nan rangwami da kamu da uƙuba, lokacin da ya zama zuwa anbatan abinda bask shi da kishiya Shi ne Allah - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka - ya nemi tsari da Shi daga gareShi bada waninSa ba, ma'anar haka: Istigfari domin kasawa wurin cika wajibi daga haƙƙin bayinSa, da yabo a gareShi. da faɗinSa: ba zan iya ƙididdige yabo a gareka ba: Wato ba zan iya shi ba, kuma ba zan iya kai matuka a cikinsa ba.
Madogara

صحيح مسلم (1/ 352) (486). تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص781). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (5/ 510). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين 2/ 979). طريق الهجرتين وباب السعادتين، لابن قيم الجوزية (ص136).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai taɓayin wata sallah ba bayan saukar: {Idan nasarar Allah ta zo da buɗi} [al-Nasr: 1] ta sauka gare shi sai ya ce a cikinta (sallar): "Tsarki ya tabbatar maKa Ubangijinmu da godiyarKa ya Allah Ka gafarta mini'

عَنْ عَائِشَةَ أُمِّ المُؤْمِنينَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهَا قَالَتْ: مَا صَلَّى النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ صَلاَةً بَعْدَ أَنْ نَزَلَتْ عَلَيْهِ: {إِذَا جَاءَ نَصْرُ اللَّهِ وَالفَتْحُ} [النصر: 1] إِلَّا يَقُولُ فِيهَا: «سُبْحَانَكَ رَبَّنَا وَبِحَمْدِكَ اللَّهُمَّ اغْفِرْ لِي». وعَنْها قَالَتْ: كَانَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يُكْثِرُ أَنْ يَقُولَ فِي رُكُوعِهِ وَسُجُودِهِ: «سُبْحَانَكَ اللهُمَّ رَبَّنَا وَبِحَمْدِكَ، اللهُمَّ اغْفِرْ لِي» يَتَأَوَّلُ الْقُرْآنَ.
Daga Nana Aisha Uwar Muminai - Allah ya yarda da ita - ta ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai taɓayin wata sallah ba bayan saukar: {Idan nasarar Allah ta zo da buɗi} [al-Nasr: 1] ta sauka gare shi sai ya ce a cikinta (sallar): "Tsarki ya tabbatar maKa Ubangijinmu da godiyarKa ya Allah Ka gafarta mini'. Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana yawan faɗa a cikin ruku'unsa da sujjadarsa: "Tsarki ya tabbatar maKa ya Allah Ubangijinmu da godiyarKa, ya Allah Ka gafarta mini" yana fassara alƙur'ani.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Uwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - tana bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - lokacin da aka saukar masa da: {Idan nasarar Allah ta zo da buɗi} ya fassara Alƙur'ani kuma ya yi gaggawa zuwa ruko da umarnin Allah - Maɗaukakin sarki - a cikin faɗinSa: {Ka yi tasbihi da godiyar Ubangijinka kuma ka nemi gafararSa}, to ya kasance yana yawaita faɗa a cikin halin ruku'insa da sujjadarsa a tsakiyar sallah: "Tsarki ya tabbatar maKa" da tsarkakewa gareKa daga dukkan tawaya daga abinda ba ya dacewa da Kai, "Ya Allah Ubangijinmu da godiyarKa" da yabo abin yabo gareKa dan cikar zatinka da siffofinKa da ayyukanKa, "Ya Allah Ka gafarta mini' Ka shafe mini zunubina Ka ƙetare daga gare shi .

Fa’idoji
  1. An so yawaita wannan addu'ar a cikin ruku'u da sujjada.
  2. Istigfari a ƙarshen rayuwa a cikinsa akwai faɗakarwa da cewa ka cika ibadu kamar haka - musamman ma sallah - da istigfari, dan ya riski abinda ya faru a cikinta na tawaya.
  3. Mafi kyan abinda ake tawassuli da shi zuwa ga Allah a cikin karɓar addu'a shi ne ambatan abubuwan yabonSa da tasbihinSa da tsarkake Shi daga tawaya da aibuka.
  4. Falalar istigfari, da kuma nemansa a kowane hali.
  5. Cikar ubudiyyar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da rukonsa da umarnin Allah.
Madogara

صحيح البخاري (6/ 178) (4968، 4967). صحيح مسلم (1/ 350-351) (484). تيسير العلام، للبسام (ص214). تنبيه الأفهام، للعثيمين (2/ 278). الإفهام في شرح عمدة الأحكام، لابن باز (ص263). الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري (1/ 176). خلاصة الكلام، فيصل المبارك (ص97).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Lallai cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya futo wurinmu, sai muka ce: Ya Manzon Allah, hakika mun san ya zamu yi maka sallama, to yaya zamu yi maka salati?

عَنْ عَبْدِ الرَّحْمَنِ بْنِ أَبِي لَيْلَى قَالَ: لَقِيَنِي كَعْبُ بْنُ عُجْرَةَ، فَقَالَ: أَلاَ أُهْدِي لَكَ هَدِيَّةً؟ إِنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ خَرَجَ عَلَيْنَا، فَقُلْنَا: يَا رَسُولَ اللَّهِ، قَدْ عَلِمْنَا كَيْفَ نُسَلِّمُ عَلَيْكَ، فَكَيْفَ نُصَلِّي عَلَيْكَ؟ قَالَ: «فَقُولُوا: اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ».
Daga Abdurrahman dan Abu Laila ya ce: Ka'abu dan Ujra ya hadu da ni, sai ya ce: Shin ba na baka wata kyauta ba? Lallai cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya futo wurinmu, sai muka ce: Ya Manzon Allah, hakika mun san ya zamu yi maka sallama, to yaya zamu yi maka salati? Ya ce: "Ku ce: Ya Allah ka yi salati ga (Annabi) Muhammad da alayen (Annabi) Muhammad, kamar yanda Ka yi salati ga (Annabi) Ibrahim da alayen (Annabi) Ibrahim, lallai cewa kai abin yabo ne kuma Mai girma. ya Allah Ka yi albarka ga (Annabi) Muhammad da alayen (Annabi) Muhammad, kamar yadda ka yi albarka ga (Annabi) Ibrahim da alayen (Annabi) Ibrahim, lallai kai abin yabo ne kuma Mai girma".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Sahabbai sun tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da siffar salati gare shi? bayan sun san siffar sallama gare shi a Tahiya: "Aminci ya tabbata agareka ya kai wannan Annabi da rahamar Allah da albarkarSa..."? Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya sanar da su siffar salati gare shi, ma'anarsa: "Ya Allah ka yi salati ga (Annabi) Muhammad da alayen (Annabi) Muhammad" Wato: Ka yi yabo gare shi da ambato mai kyau a cikin jama'a madaukaka, da mabiyansa a cikin AddininSa, da muminai daga makusantansa. "kamar yadda Ka yi salati ga (Annabi) Ibrahim" Kamar yadda ka yi baiwa ga iyalan (Annabi) Ibrahim - aminci ya tabbata agare shi - su ne (Annabi) Ibrahim, da (Annabi) Isma'il, da (Annabi) Ishak, da zuriyarsu da mabiyansu muminai, to ka riskar da falalararKa ga (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -. "Lallai kai abin yabo ne kuma Mai girma" Wato: Abin yabo a zatinKa da siffofinKa da ayyukanKa, Mayalwaci a girmanKa da sarautarKa da baiwarKa. "Ya Allah Ka yi albarka ga (Annabi) Muhammad da alayen (Annabi) Muhammad kamar yanda ka yi albarka ga Ibrahim" Wato: Ka ba shi alheri da girmamawa mafi girmasa Ka kara masa Ka tabbatar masa.

Fa’idoji
  1. Magabata sun kasance suna musayar kyautar mas'alolin ilimi.
  2. Wajabcin salati ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a Tahiyar karshe a sallah.
  3. Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya koyawa sahabbansa sallama da salati gare shi.
  4. Wannan sigar ita ce mafi cikar sigogi a salati ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
Madogara

صحيح البخاري (8/ 77) (6357). صحيح مسلم (1/ 305) (406). تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، لعبد الله البسام (ص208). تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام، لابن عثيمين (2/ 270). الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري (1/ 170).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana faɗinsu bayan kowacce sallah

عَنْ ‌أَبِي الزُّبَيْرِ قَالَ: كَانَ ‌ابْنُ الزُّبَيْرِ يَقُولُ فِي دُبُرِ كُلِّ صَلَاةٍ حِينَ يُسَلِّمُ: «لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ وَحْدَهُ لَا شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ، لَا حَوْلَ وَلَا قُوَّةَ إِلَّا بِاللهِ، لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ، ‌وَلَا ‌نَعْبُدُ ‌إِلَّا إِيَّاهُ، لَهُ النِّعْمَةُ وَلَهُ الْفَضْلُ وَلَهُ الثَّنَاءُ الْحَسَنُ، لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ وَلَوْ كَرِهَ الْكَافِرُونَ» وَقَالَ: «كَانَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يُهَلِّلُ بِهِنَّ دُبُرَ كُلِّ صَلَاةٍ».
Daga baban Zubair ya ce: Dan Zubair ya kasance yana cewa a bayan kowacce Sallah idan ya yi sallama: Babu abin bautawa da cancanta sai Allah, Shi kaɗai Ya ke ba shi da abokin tarayya, mulki na Sa ne, kuma godiya ta Sa ce, kuma Shi mai iko ne a kan komai. Ba dabara ba ƙarfi sai da Allah, babu abin bauta da gaskiya sai Allah, ba ma bautawa kowa sai Shi, Shi Ya ke da ni’ima da falala, Shi ke da kyawawan yabo, babu abin bautawa da cancanta sai Allah, muna masu tsarkake addini gare shi, ko da kafirai sun ƙi. Ya kuma ce: Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana faɗinsu bayan kowacce sallah.
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana HAILALA bayan ya sallame daga kowacce sallah ta farilla da wannan zikirin mai girma, Ma’anarsa ita ce: "Babu abin bautawa sai Allah"; Wato babu abin bauta da gaskiya sai Allah. "Shi kaɗai yake ba shi da abokin tarayya": Wato babu wanda yake tarayya da Shi a Allantaka [ cancantar bauta ] ko a rububiyya [ kasancewarSa Mahalicci, Mai azurtawa, Mai rayawa, Mai matarwa ] ko kuma a sunaye da siffofinSa. "Mulki na sa ne": Wato; Shi Ya ke da cikakken mulki wanda ya game komai, mulkin sammai da ƙassai da abin da ke tsakaninsu. "Godiya ta sa ce": Wato shi ne wanda ya siffantu da cikakkiyar cika, wanda ake yabonSa da cika saboda so da girmawa a kowanne lokaci, na farin ciki da na damuwa. "Shi mai iko ne a kan komai": IkonSa cikakken iko ne ta kowacce fuska, babu abin da yake gagararsa, babu wani al’amari da zai gagare shi. "Ba dabara ba ƙarfi sai da yin Allah": Wato babu canji daga wani hali zuwa wani halin, ko daga saɓon Allah zuwa ga baiyayyarSa, haka babu ƙarfi, sai da Allah wanda Shi ne Mai taimako, kuma Wanda ake dogara da Shi. "Babu abin bauta da gaskiya sai Allah, ba ma bautawa kowa sai Shi": karfafawa ce a kan ma’anar Allantaka da kuma kore shirka, da cewa babu wanda ya cancanci bauta in ba Shi ba. "Ni’ima ta Sa ce da falala": Shi ne wanda ya halicci ni’imomi kuma yake mallakarsu, yake kuma ba da su ga wanda Ya so cikin bayinSa. "Kyakkyawan yabo nasa ne": A bisa zatinSa da siffofinSa da ayyukanSa da Ni’imominSa a kowanne lokaci. "Babu abin bautawa da cancanta sai Allah, muna masu tsantsanta addini a gareShi": Wato, muna masu Tauhidi, babu riya, kuma babu jiyarwa a kan biyayya ga Allah. "Koda kafirai sun ƙi": Wato muna masu tabbatuwa a kan Tauhidi da bauta masa ko da kafirai sun ƙi.

Fa’idoji
  1. An so kulawada da wannan zikirin bayan kowacce sallah ta farilla.
  2. Musulmi yana ji da addininsa, kuma yana bayyana ayyukan addininsa, ko da kafirai sun ƙi.
  3. Idan a cikin Hadisi aka ce: "bayan sallah", to, idan abin da a ka ce a Hadisin zikiri ne, to, asali ana nufin bayan sallama, idan kuma addu’a ce, to, ana nufin kafin sallama.
Madogara

صحيح مسلم (1/ 415) (594). سبل السلام شرح بلوغ المرام، للصنعاني (1/ 293). كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (17/ 61). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمصطفى الخِن وغيره (2/ 973). بهجة الناظرين، لسليم الهلالي (2/ 499). مرقاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح، لعلي القاري (2/ 762). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (5/ 492).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Masu biyewa juna mai fadinsu ba ya tabewa - ko mai aikata su - a bayan kowacce sallar farilla, Tasbihi talatin da uku, da Tahmidi talatin da uku, da Kabbara talatin da hudu

عَنْ كَعْبِ بْنِ عُجْرَةَ رضي الله عنه عَنْ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «مُعَقِّبَاتٌ لَا يَخِيبُ قَائِلُهُنَّ -أَوْ فَاعِلُهُنَّ- دُبُرَ كُلِّ صَلَاةٍ مَكْتُوبَةٍ، ثَلَاثٌ وَثَلَاثُونَ تَسْبِيحَةً، وَثَلَاثٌ وَثَلَاثُونَ تَحْمِيدَةً، وَأَرْبَعٌ وَثَلَاثُونَ تَكْبِيرَةً».
Daga Ka'ab dan Ujrah - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Masu biyewa juna mai fadinsu ba ya tabewa - ko mai aikata su - a bayan kowacce sallar farilla, Tasbihi talatin da uku, da Tahmidi talatin da uku, da Kabbara talatin da hudu".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labari game da wasu zikiran da mai fadainsu ba ya asara kuma ba ya tabewa, kai yana da ladan wadannan kalmomin, kuma sashinsu yana zuwa bayan sashi, ana fadarsu a bayan sallolin farilla, su ne: "Tsarki ya tabbata ga Allah" sau talatin da uku, wato tsarkakeshi - Madaukakin sarki - daga dukkanin tawaya. "Godiya ta tabbata ga Allah" sau talatin da uku, ita ce siffanta Allah da cikakkiyar cika tare da soyayyarSa da girmamaShi. "Allah ne Mafi girma" sau talatin da hudu, Allah ne Mafi girmamawa Mafi buwaya daga dukkan komai.

Fa’idoji
  1. Falalar tasbihi da tahmidi da kabbara, su ne wanzajju nagartattu.
Madogara

صحيح مسلم (1/ 418) (596). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 501). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (2/ 976). مرقاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح، لعلي القاري (2/ 766). تيسير العلام، للبسام (ص227). فيض القدير شرح الجامع الصغير، لزين الدين المناوي (5/ 525).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
8 cikin 17
Hadisai 17
  1. Ya Allah ni ina neman tsarinka daga azabar kabari, da azabar wuta, da fitinar rayuwa da mutuwa, da fitinar Mai yawan yawo makaryaci (Jujal)
  2. Ya Allah Ka nesanta tsakanina da kurakurai na kamar yadda Ka nesanta tsakanin mahudar rana da mafaɗarta
  3. bayan kowace sallah kada ka bar faɗin: Ya Allah Ka taimakeni akan ambatanKa da gode maKa da kyakkyawar ibadarKa
  4. Ya Allah ina neman tsari da yardarKa daga fushinKa, da kuma rangwaminKa daga uƙubarKa, kuma ina neman tsari da Kai daga gareKa ba zan iya ƙididdige yabo gareKa ba kamar yadda Ka yabi kanKa
  5. Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai taɓayin wata sallah ba bayan saukar: {Idan nasarar Allah ta zo da buɗi} [al-Nasr: 1] ta sauka gare shi sai ya ce a cikinta (sallar): "Tsarki ya tabbatar maKa Ubangijinmu da godiyarKa ya Allah Ka gafarta mini'
  6. Lallai cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya futo wurinmu, sai muka ce: Ya Manzon Allah, hakika mun san ya zamu yi maka sallama, to yaya zamu yi maka salati?
  7. Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana faɗinsu bayan kowacce sallah
  8. Masu biyewa juna mai fadinsu ba ya tabewa - ko mai aikata su - a bayan kowacce sallar farilla, Tasbihi talatin da uku, da Tahmidi talatin da uku, da Kabbara talatin da hudu
  9. Ya Ubangijin jibrila da Mika'ila, da isarafilu, wanada ya halicci sammai da Qasa, wanda ya ke masanin gaibu da fili, kai ne wanda kake yin hukunci a tsakanin bayinka cikin abunda suka sabawa a cikinsa, ka shiryar da ni cikin abunda suka sava a cikinsa na gaskiya da ikonka, lallai kai ne Mai shiryar da wanda ka so zuwa tafarki madaidaici
  10. Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana faɗa a tsakanin sujjada biyu; "Ya Ubangiji ka gafarta min, ka yi min rahama, ka ba ni lafiya, ka shiryar da ni, ka azurta ni
  11. "Manzo tsira da amincin Alla su tabbata a gare shi ya koyar da ni tahiya.hannu na na cikin hannayensa, kamar yadda yake koyar da ni Surar daga Alqur'ani"
  12. Ya Ubangiji Kai ne aminci, kuma aminci daga gareka yake, Ka ɗaukaka ya ma’abocin girma da karamci
  13. Wanda ya tsarkake Allah a bayan kowacce sallah sau talatin da uku, kuma ya gode wa Allah sau talatin da uku, ya yi wa Allah Kabbara sau talatin da uku, wancan (lissafin) shi ne casa'in da tara kenan, kuma yace a cikon ɗarin: (Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kaɗai Yake ba Shi da abokin tarayya, mulki ya tabbata gareShi, godiya ta tabbata gareShi, kuma Shi mai iko ne a kan dukkan komai), za'a gafarta masa kurakuran sa, ko da sun kasance tamkar kumfar kogi
  14. Wanda ya karanta Ayatul kursiyyi a bayan kowacce sallar farilla to babu abinda zai hana shi shiga aljanna sai mutuwa
  15. Sunyi Gaskiya, lallai su ana yi musu Azaba Azabar da Dabbobi suke ji baki xayansu
  16. Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance idan ya ɗago bayansa daga ruku'u sai ya ce: "Allah Ya ji wanda ya gode maSa
  17. Lallai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana faɗa a bayan kowacce sallar farilla

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com