Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

bayan kowace sallah kada ka bar faɗin: Ya Allah Ka taimakeni akan ambatanKa da gode maKa da kyakkyawar ibadarKa

عَنْ مُعَاذِ بْنِ جَبَلٍ رضي الله عنه: أَنَّ رَسُولَ صَلَّى عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَخَذَ بِيَدِهِ، وَقَالَ: «يَا مُعَاذُ، وَاللَّهِ إِنِّي لَأُحِبُّكَ»، فَقَالَ: «أُوصِيكَ يَا مُعَاذُ لَا تَدَعَنَّ فِي دُبُرِ كُلِّ صَلَاةٍ تَقُولُ: اللَّهُمَّ أَعِنِّي عَلَى ذِكْرِكَ وَشُكْرِكَ وَحُسْنِ عِبَادَتِكَ».
Daga Mu'az Bin Jabal -Allah Ya yarda da shi -: Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya riƙe hannuna, sai ya ce: "Ya Mu'az, wallahi lallai ni ina sonka", sai ya ce: "Ina yi maka wasicci ya Mu'az bayan kowace sallah kada ka bar faɗin: Ya Allah Ka taimakeni akan ambatanKa da gode maKa da kyakkyawar ibadarKa".
Abu Dawud da Nasa'i haka Ahmad suka ruwaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya riƙe hannun Mu'aza - Allah Ya yarda da shi -, sai ya ce masa: Wallahi lallai ni ina sonka, kuma ina yi maka wasicci ya Mu'az a ƙarshen kowace sallah kada kabar faɗin: (Ya Allah Ka taimakeni akan ambatanKa) a kowace magana da aikin da zai kusanto da ni zuwa biyayya, (da godiyarKa) ta hanyar samun ni'imomi da tunkuɗe masifu, (da kyakkyawar bautarKa) ta hanyar yin ikhlasi ga Allah da bin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.

Fa’idoji
  1. Halaccin baiwa mutum labari da sonsa a lamarin Allah.
  2. An so yin wannan addu'ar a bayan kowace sallar farilla da nafila.
  3. A cikin yin addu'a da waɗannan lafuzan 'yan kaɗan (akwai) abbuwan nema a duniya da lahira.
  4. Daga fa'idojin soyayya a lamarin Allah yin wasicci da gaskiya da yi wa juna nasiha da taimakekeniya akan aikin alheri da tsoron Allah.
  5. Malam al-Ɗaibi ya ce: Ambatan Allah shi ne kan gaba a buɗewar ƙirji, godiyarSa kuma tsani ce na ni'imomi ababen amsawa, kyakkyawar ibada kuwa abar nema daga gare shi, shi ne nisantar abinda zai shagaltar da shi daga Allah - Maɗaukakin sarki -.
Madogara

سنن أبي داود (2/ 630) (1522). سنن النسائي (3/ 53) (1303). مسند أحمد (36/ 429) (22119). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 450). تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص259). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (3/ 264). كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (6/ 284). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 353).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
ZIKIRAN SALLAH

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com