Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Ya Allah ni ina neman tsarinka daga azabar kabari, da azabar wuta, da fitinar rayuwa da mutuwa, da fitinar Mai yawan yawo makaryaci (Jujal)

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: كَانَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَدْعُو وَيَقُولُ: «اللَّهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ مِنْ عَذَابِ القَبْرِ، وَمِنْ عَذَابِ النَّارِ، وَمِنْ فِتْنَةِ المَحْيَا وَالمَمَاتِ، وَمِنْ فِتْنَةِ المَسِيحِ الدَّجَّالِ». وفِي لَفْظٍ لِمُسْلِمٍ: «إِذَا فَرَغَ أَحَدُكُمْ مِنَ التَّشَهُّدِ الْآخِرِ، فَلْيَتَعَوَّذْ بِاللهِ مِنْ أَرْبَعٍ: مِنْ عَذَابِ جَهَنَّمَ، وَمِنْ عَذَابِ الْقَبْرِ، وَمِنْ فِتْنَةِ الْمَحْيَا وَالْمَمَاتِ، وَمِنْ شَرِّ الْمَسِيحِ الدَّجَّالِ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana yin addu'a yana cewa: "Ya Allah ni ina neman tsarinka daga azabar kabari, da azabar wuta, da fitinar rayuwa da mutuwa, da fitinar Mai yawan yawo makaryaci (Jujal)". A cikin wani lafazin na Muslim: "Idan dayanku ya gama tahiyar karshe, to ya nemi tsarin Allah daga abubuwa hudu: Daga azabar kabari, da fitinar rayuwa da mutuwa, da sharrin Mai yawan yawo makaryaci (Jujal).
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana neman tsarin Allah daga abubuwa hudu bayan tahiyar karshe kuma kafin sallama a sallah, ya kuma umarcemu mu nemi tsarin Allah daga garesu, Na farko: Daga azabar kabari. Na biyu: Daga azabar wuta hakan a ranar Alkiyama . Na uku: Daga fitinar rayuwa na sha'awowin duniya haramtattu da kuma shubuhohi masu batarwa, da kuma fitinar mutuwa, wato lokacin fitar rai, na karkacewa daga musulunci ko sunna, ko fitinar kabari kamar tambayar Mala'iku biyu. Na hudu: Fitinar mai yawan yawo makaryaci (Dajjal) wanda zai fito a karshen zamani, Allah zai jarrabi bayinSa da shi, ya kebance shi da ambato dan girman fitinarsa da batarwarsa.

Fa’idoji
  1. Wanan neman tsarin yana daga muhimman addu'o'i kuma gamammu, dan abinda suka kunsa na neman tsari daga sharrukan duniya da lahira.
  2. Tabbatar da azabar kabari kuma cewa ita gaskiya ce.
  3. Hadarin fitintinu da muhimmancin neman taimakon Allah da addu'a dan tsira daga garesu.
  4. Tabbatar da fitowar Dujal da girman fitinarsa.
  5. An so yin wannan addu'ar bayan tahiyar karshe.
  6. An so yin addu'a bayan aiki na gari.
Madogara

صحيح البخاري (2/ 99) (1377). صحيح مسلم (1/ 412) (588). الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري (1/ 172). تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، للبسام (ص212). خلاصة الكلام شرح عمدة الأحكام، لفيصل آل مبارك (ص96).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
ZIKIRAN SALLAH

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com