Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana cewa idan ya kammala sallarsa; Ina neman gafar Allah, Ina neman gafarar Allah, Ina neman gafarar Allah. Sannan sai ya girmama Ubangijinsa, ya ce: "Ya Ubangiji Kai ne aminci, kuma aminci daga gareKa yake, Ka girmama ya ma’abocin girma da karamci". Shi Allah tsarkakke ne, kuma cikakke ne a siffofinsa, kuma Ya tsarkaka daga barin kowanne aibu da tawaya, kuma ka nemi waraka daga dukkan sharri duniya da lahira daga wajenSa ba daga wani ba, Shi Allah alheranSa sun yawaita a duniya da lahira, Ma’abocin girma da kyautatawa ne.
- Ana son neman gafara bayan kammala sallah, da kuma dawwama a kan hakan.
- Ana son neman gafara domin cike tawaya a ibada, da ɗori na kasawa a ibadar.
صحيح مسلم (1/ 414) (591). مرعاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح، لعبيد الله المباركفوري (3/ 317). سبل السلام، للصنعاني (1/ 294). توضيح الأحكام مِن بلوغ المرام، لعبد الله البسام (2/ 301).