Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Wanda ya karanta Ayatul kursiyyi a bayan kowacce sallar farilla to babu abinda zai hana shi shiga aljanna sai mutuwa

عَنْ أَبِي أُمَامَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «مَنْ قَرَأَ آيَةَ الْكُرْسِيِّ فِي دُبُرِ كُلِّ صَلَاةٍ مَكْتُوبَةٍ لَمْ يَمْنَعْهُ مِنْ دُخُولِ الْجَنَّةِ إِلَّا أَنْ يَمُوتَ».
Daga Abu Umamah - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya karanta Ayatul kursiyyi a bayan kowacce sallar farilla to babu abinda zai hana shi shiga aljanna sai mutuwa".
Nasa'i ne ya rawaito shi a cikin Al-KubraDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wanda ya karanta Ayatul Kursi bayan ƙare sallar farilla babu abinda zai hana shi shiga aljanna sai mutuwa; ita tana cikin Suratul Baƙara, faɗinSa - Maɗaukakin sarki -: {Allah, bãbu wani Ubangiji fãce Shi, Rãyayye, Wanda komai ya tsayu da Shi, gyangyaɗi bã ya kãma Shi, kuma barci bã ya kãma Shi, Shi ne da abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasa. Wanene wanda yake yin cẽto a wurinSa, fãce da izninSa? Yana sanin abin da yake a gaba gare su da abin da yake a bãyansu. Kuma bã su kẽwayẽwa da kõme daga ilminSa, fãce da abin da Ya so. KursiyyunSa ya yalwaci sammai da ƙasa. Kuma tsare su bã ya gajiyar da Shi, Kuma Shi ne Maɗaukaki, Mai girma} [al-Baƙara: 255].

Fa’idoji
  1. Falalar wannan ayar mai girma; dan abinda ta ƙunsa na kyawawan sunaye, da siffofi Maɗaukaka.
  2. An so karanta wannan ayar mai girma bayan kowacce sallar farilla.
  3. Ayyuka na gari sababi ne na shiga aljanna.
Madogara

المعجم الكبير، للطبراني السنن الكبرى، للنسائي (9/ 44) (9848). توضِيحُ الأحكَامِ مِن بُلوُغ المَرَام، للبسام (2/ 313). منحة العلام في شرح بلوغ المرام، لعبد الله الفوزان (3/ 197).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
ZIKIRAN SALLAH

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com