Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai taɓayin wata sallah ba bayan saukar:
{Idan nasarar Allah ta zo da buɗi} [al-Nasr: 1] ta sauka gare shi sai ya ce a cikinta (sallar):
"Tsarki ya tabbatar maKa Ubangijinmu da godiyarKa ya Allah Ka gafarta mini'
Daga Nana Aisha Uwar Muminai - Allah ya yarda da ita - ta ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai taɓayin wata sallah ba bayan saukar:
{Idan nasarar Allah ta zo da buɗi} [al-Nasr: 1] ta sauka gare shi sai ya ce a cikinta (sallar):
"Tsarki ya tabbatar maKa Ubangijinmu da godiyarKa ya Allah Ka gafarta mini'. Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana yawan faɗa a cikin ruku'unsa da sujjadarsa: "Tsarki ya tabbatar maKa ya Allah Ubangijinmu da godiyarKa, ya Allah Ka gafarta mini" yana fassara alƙur'ani.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Uwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - tana bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - lokacin da aka saukar masa da: {Idan nasarar Allah ta zo da buɗi} ya fassara Alƙur'ani kuma ya yi gaggawa zuwa ruko da umarnin Allah - Maɗaukakin sarki - a cikin faɗinSa: {Ka yi tasbihi da godiyar Ubangijinka kuma ka nemi gafararSa}, to ya kasance yana yawaita faɗa a cikin halin ruku'insa da sujjadarsa a tsakiyar sallah: "Tsarki ya tabbatar maKa" da tsarkakewa gareKa daga dukkan tawaya daga abinda ba ya dacewa da Kai, "Ya Allah Ubangijinmu da godiyarKa" da yabo abin yabo gareKa dan cikar zatinka da siffofinKa da ayyukanKa, "Ya Allah Ka gafarta mini' Ka shafe mini zunubina Ka ƙetare daga gare shi .
Fa’idoji
An so yawaita wannan addu'ar a cikin ruku'u da sujjada.
Istigfari a ƙarshen rayuwa a cikinsa akwai faɗakarwa da cewa ka cika ibadu kamar haka - musamman ma sallah - da istigfari, dan ya riski abinda ya faru a cikinta na tawaya.
Mafi kyan abinda ake tawassuli da shi zuwa ga Allah a cikin karɓar addu'a shi ne ambatan abubuwan yabonSa da tasbihinSa da tsarkake Shi daga tawaya da aibuka.
Falalar istigfari, da kuma nemansa a kowane hali.
Cikar ubudiyyar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da rukonsa da umarnin Allah.
Madogara
صحيح البخاري (6/ 178) (4968، 4967).
صحيح مسلم (1/ 350-351) (484).
تيسير العلام، للبسام (ص214).
تنبيه الأفهام، للعثيمين (2/ 278).
الإفهام في شرح عمدة الأحكام، لابن باز (ص263).
الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري (1/ 176).
خلاصة الكلام، فيصل المبارك (ص97).
Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com