عَنْ حُمْرَانَ مَوْلَى عُثْمَانَ بْنِ عَفَّانَ رضي الله عنه: أَنَّهُ رَأَى عُثْمَانَ بْنَ عَفَّانَ دَعَا بِوَضُوءٍ، فَأَفْرَغَ عَلَى يَدَيْهِ مِنْ إِنَائِهِ، فَغَسَلَهُمَا ثَلَاثَ مَرَّاتٍ، ثُمَّ أَدْخَلَ يَمِينَهُ فِي الْوَضُوءِ، ثُمَّ تَمَضْمَضَ وَاسْتَنْشَقَ وَاسْتَنْثَرَ، ثُمَّ غَسَلَ وَجْهَهُ ثَلَاثًا، وَيَدَيْهِ إِلَى الْمِرْفَقَيْنِ ثَلَاثًا، ثُمَّ مَسَحَ بِرَأْسِهِ، ثُمَّ غَسَلَ كُلَّ رِجْلٍ ثَلَاثًا، ثُمَّ قَالَ: رَأَيْتُ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَتَوَضَّأُ نَحْوَ وُضُوئِي هَذَا، وَقَالَ: «مَنْ تَوَضَّأَ نَحْوَ وُضُوئِي هَذَا ثُمَّ صَلَّى رَكْعَتَيْنِ لَا يُحَدِّثُ فِيهِمَا نَفْسَهُ غَفَرَ اللهُ لَهُ مَا تَقَدَّمَ مِنْ ذَنْبِهِ».
Daga Humran bararran bawa na Usman Dan Affan cewa ya ga Usman Dan Affan ya nemi da akawo masa ruwan alwala, sai ya karkato da kwaryar (butar Alwala), sai ya wankesu sau uku, sannan ya shigar da (hannunsa na) dama a ruwan alwalar, sannan ya kuskure baki ya shaƙa ruwa ya face, sannan ya wanke fuskarsa sau uku, da hannayensa zuwa gwiwar hannaye sau uku, sannan ya shafi kansa, sannan ya wanke kowacce ƙafa sau uku, sannan ya ce: Na ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a greshi - ya yi alwala irin wannan alwalar tawa, sai ya ce: "Wanda ya yi alwala irin wannan alwalar tawa sannan ya yi sallah raka'a biyu bai zantar da ransa a cikinsu ba, to, Allah Zai gafarta masa abin da ya gabata daga zunubinsa".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Sayyidina Usman - Allah Ya yarda da shi - ya karantar da siffar alwalar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a aikace; don ya zama mafi fitowa ɓaro-ɓaro, sai ya nemi ruwa a ƙwarya, sai ya zuba a hannayensa sau uku, bayan haka ya shigar da hannunsa na dama a cikin ƙwaryar, sai ya ɗebo ruwa daga cikinta sai ya kurkura shi a bakinsa, sannan ya fitar da shi, sannan ya shaki ruwan da numfashinsa zuwa cikin hancinsa, sannan ya fitar da shi ya face, sannan ya wanke fuskarsa sau uku, sannan ya wanke hannayensa tare da gwiwar hannaye sau uku, sannan ya shuɗar da hannunsa a kan kansa suna masu damshi da ruwa sau ɗaya, sannan ya wanke ƙafafuwansa tare da idon sawu sau uku.
Lokacin da ya gama - Allah Ya yarda da shi - sai ya ba su labarin cewa shi ya ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya yi alwala irin wannan alwalar, kuma [Annabi] - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi musu albishir da cewa wanda ya yi irin wannan alwalar, ya yi sallah raka'a biyu, yana mai khushu'i yana mai halarto da zuciyarsa a gaban Ubangijinsa - mai girma da ɗaukaka - a cikinsu, to, Allah Zai yi masa sakayya a kan wannan alwalar cikakkiya da wannan sallar tsarkakiyya da gafarta abin da ya gabata daga zunubansa.
Fa’idoji
- An so wanke hannaye kafin shigar da su a cikin ƙwarya (butar Alwala) a farkon alwala, ko da bai kasance ya taso daga barci ba, idan ya farka daga barcin dare ne, to, ya wajaba a wankesu.
- Ya kamata ga mai koyarwa ya bi hanya mafi kusa ga fahimta da tabbatar da ilimi ga mai koyo, daga hakan akwai koyarwa a aikace.
- Ya kamata ga mai sallah ya tunkuɗe duk wasu tunani dake rataye da shagulgulan duniya, cikar sallah da kamalarta (yana tabbata ne) a halartowar zuciya a cikinta, in ba haka ba fa, to, kuɓuta daga tunani iri daban daban yana da wahala [a sallah], ya wajaba a kansa ya yaƙi ransa kada ya yi sako-sako a hakan.
- An so damantawa a alwala.
- Shar’antuwar jerantawa a tsakanin kuskurar baki da shaƙa ruwa da facewa.
- An so wanke fuska da hannaye da ƙafafuwa sau uku, amma wajibi (shi ne) sau ɗaya.
- Gafarar Allah ga abin da ya gabata daga zunubai ya jerantu ga al'amura biyu: Alwala, da sallah raka'a biyu, a kan siffar da aka ambata a hadisin.
- A kwai iyaka ga kowacce gaɓa daga gaɓɓan alwala: Iyakar fuska: Tun daga matsirar gashin kai na al'ada, zuwa abin da ya sauka zuwa gemu da haɓa a tsawo, a faɗi kuma daga kunne zuwa kunne. Iyakar hannu: Tun daga gefen 'yan yatsu zuwa gwiwar hannu, shi ne mararraba tsakanin sangalalin hannu da damtse. Iyakar kai kuma: tun daga matsirar gashi na al'ada daga sasannin fuska zuwa saman wuya, shafar kunnuwa suna cikin kai. Iyakar ƙafa: Dudduge gabaɗayansa tare da mararraba tsakaninsa da ƙwauri.
Madogara
صحيح البخاري (1/ 44) (164).
صحيح مسلم (1/ 204) (226).
الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري (1/ 16).
تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، للبسام (ص26).
تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام، لابن عثيمين (1/ 24).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ يحيى بنِ عُمَارةَ المَازِنِيِّ قَالَ: شَهِدْتُ عَمْرَو بْنَ أَبِي حَسَنٍ سَأَلَ عَبْدَ اللَّهِ بْنَ زَيْدٍ، عَنْ وُضُوءِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَدَعَا بِتَوْرٍ مِنْ مَاءٍ، فَتَوَضَّأَ لَهُمْ وُضُوءَ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَأَكْفَأَ عَلَى يَدِهِ مِنَ التَّوْرِ، فَغَسَلَ يَدَيْهِ ثَلاَثًا، ثُمَّ أَدْخَلَ يَدَهُ فِي التَّوْرِ، فَمَضْمَضَ وَاسْتَنْشَقَ وَاسْتَنْثَرَ، ثَلاَثَ غَرَفَاتٍ، ثُمَّ أَدْخَلَ يَدَهُ فَغَسَلَ وَجْهَهُ ثَلاَثًا، ثُمَّ غَسَلَ يَدَيْهِ مَرَّتَيْنِ إِلَى المِرْفَقَيْنِ، ثُمَّ أَدْخَلَ يَدَهُ فَمَسَحَ رَأْسَهُ، فَأَقْبَلَ بِهِمَا وَأَدْبَرَ مَرَّةً وَاحِدَةً، ثُمَّ غَسَلَ رِجْلَيْهِ إِلَى الكَعْبَيْنِ.
Daga Yahaya dan Umara AlMazinu ya ce: Na halarci Amr dan Abu Hassan ya tambayi Abdullahi dan Zaid game da alwalar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce a kawo masa kwarya ta ruwa, sai ya yi musu alwala irin alwalar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya sanya hannunsa akwaryar, sai ya wanke hannayensa sau uku, sannan ya shigar da hannunsa a cikin kwaryar, sai ya kuskure baki ya shaka ruwa ya face, kanfata uku, sannan ya shigar da hannunsa sai ya wanke fuskarsa sau uku, sannan ya wanke hannayensa sau biyu zuwa gwiwar hannu, sannan ya shigar da hannunsa sai ya shafi kansa, sai ya yi gaba da su ya yi baya sau daya, sannan ya wanke kafafuwansa zuwa idan sawu.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Abdullahi Dan Zaid - Allah Ya yarda da shi - yana bayyana siffar alwalar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi a aikace, sai ya nemi karamar kwarya (buta) ta ruwa, a farko sai ya fara da wanke tafukansa, sannan ya karkatar da kwaryar ya zuba ruwa sai ya wankesu sau uku a wajen kwaryar, sannan ya shigar da hannunsa a cikin kwaryar ya kanfato daga gareta kanfata uku yana kuskurar baki a kowacce kanfata yana shaka ruwa yana facewa, sannan ya kanfato daga kwaryar (butar) sai ya wanke fuskarsa sau uku, sannan ya kanfato daga gareta sai ya wanke hannayensa zuwa gwiwoyin hannaye sau biyu-biyu, sannan ya shigar da hannayensa cikin kwaryar, ya shafi kansa da hannayensa ya fara da magabacin kansa har ya kai zuwa keyarsa saman wuya, sannan ya dawo da su har ya kai gurin da ya fara daga gare shi, sannan ya wanke kafafuwansa tare da idan sawu.
Fa’idoji
- yanayin malami shi ne mafi kusancin hanyoyi zuwa fahimta da tabbatar da ilimi, daga hakan koyarwa a aikace.
- halaccin maimaitawa sau uku a wasu daga gabobin alwala da yi sau biyu a sashinsu, wajibi (shi ne) sau daya.
- Wajabcin jerantawa tsakanin gabban alwala kamar yadda ya zo a cikin hadisin.
- Iyakar fuska daga matsirar gashin kai na al'ada zuwa abinda ya sauka daga gemu da haba a tsawo, daga kunne zuwa kunne a fadi.
Madogara
صحيح البخاري (1/ 48) (186).
صحيح مسلم (1/ 210) (235).
الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري (1/ 18).
الإفهام في شرح عمدة الأحكام، لابن باز (ص72).
تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، لعبد الله البسام (ص29).
تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام، لابن عثيمين (1/ 27).
شرح العمدة للسعدي (ص 50).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن عبْدِ خيْرٍقال: أتانا علي رضي الله عنه وقد صلَّى فدعا بطَهور، فقلنا ما يصنع بالطَّهور وقد صلَّى ما يُريد، إلا ليعلِّمَنا، فأُتِي بإناء فيه ماء وطَسْت، فأفْرَغَ من الإناء على يمينه، فغسل يديه ثلاثا، ثم تَمَضْمَضَ واسْتَنْثَر ثلاثا، فمَضْمَض ونَثَرَ من الكفِّ الذي يأخُذ فِيه، ثم غسل وجهه ثلاثا، ثم غسل يده اليمنى ثلاثا، وغسل يده الشِّمال ثلاثا، ثم جعل يده في الإناء فمسَحَ بِرأسه مرَّة واحدة، ثم غسل رجله اليمنى ثلاثا، ورِجْلَه الشمال ثلاثا. ثم قال: «مَنْ سرَّه أن يعْلَم وُضُوء رسول الله صلى الله عليه وسلم فهو هذا».
A kan Abdul Khair, ya ce: Ali - Allah ya yarda da shi - ya zo wurinmu sai ya yi salla ya yi salla tare da tsarkakewa.Ya watsa dabinon da yake karba, sannan ya wanke fuskarsa sau uku, sannan ya wanke damansa hannu uku, kuma ya wanke hannunsa na hagu sau uku, sa’an nan ya sa hannunsa a cikin kwano ya goge kansa sau daya, sannan ya wanke kafarsa ta dama sau uku, da ta hagu sau uku. Sannan ya ce: "Duk wanda ya faranta masa rai ya san alwalar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - wannan shi ne."
Ibnu Majah ne ya Rawaito shi - Al-Nasa'i Ya Rawaito shi - Abu Daud Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Wannan hadisin, tare da tsayinsa tsakanin sifa da alwalar Annabi - Salati da amincin Allah su tabbata a gare shi-, a ciki Abd Khair ya ambaci cewa Ali - Allah ya yarda da shi - ya zo gare su bayan ya yi salla, don haka ya sun yi kira ga ruwa. Kuma suka kawo masa ruwa a cikin kwano, sai ya zuba daga kwandon daga hannun dama, sai ya wanke hannayensa sau uku, sa'annan ya kurkure bakinsa ya kurkure sau uku, ya kurkure bakinsa kuma ya kurkuta daga dabino guda wanda yake daukar ruwan, sannan ya wanke fuskarsa sau uku, da kan iyakan fuskar daga asalin gashin kai na yau da kullun Zuwa cuwa-cuwa tare da bayan gemu, kuma daga kunne zuwa kunne, sannan ya wanke damansa hannu zuwa gwiwar hannu sau uku, sannan hagu ma, kuma guiwar hannu suna cikin wankin, sannan ya shafa kansa sau ɗaya, sa'annan ya wanke ƙafarsa ta dama sau uku, sannan ƙafarsa ta hagu sau uku, sannan ya ambata Cewa wannan alwalar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.
Madogara
سنن أبي داود, المحقق: محمد محيي الدين عبد الحميد, المكتبة العصرية، صيدا – بيروت.
السنن الصغرى للنسائي "المجتبى"، تحقيق: عبد الفتاح أبو غدة، نشر: مكتب المطبوعات الإسلامية – حلب، الطبعة: الثانية، 1406ه – 1986م.
مسند الإمام أحمد بن حنبل، تحقيق: شعيب الأرنؤوط - عادل مرشد، وآخرون، نشر: مؤسسة الرسالة، الطبعة: الأولى، 1421هـ - 2001م.
سنن ابن ماجه, تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي, الناشر: دار إحياء الكتب العربية - فيصل عيسى البابي الحلبي.
معجم اللغة العربية المعاصرة، للدكتور أحمد مختار عبد الحميد عمر بمساعدة فريق عمل، الناشر: عالم الكتب، الطبعة: الأولى، 1429 هـ - 2008 م.
تاج العروس من جواهر القاموس, محمّد بن محمّد الحسيني، الملقّب بمرتضى الزَّبيدي, مجموعة من المحققين, الناشر: دار الهداية.
توضيح الأحكام مِن بلوغ المرام، تأليف: عبد الله بن عبد الرحمن بن صالح البسام، الناشر: مكتبة الأسدي، مكة المكرّمة الطبعة: الخامِسَة، 1423 هـ - 2003 م
فتح ذي الجلال والإكرام شرح بلوغ المرام لمحمد بن صالح بن محمد العثيمين، تحقيق: صبحي بن محمد رمضان، وأُم إسراء بنت عرفة، ط1، المكتبة الإسلامية، مصر، 1427ه.
منحة العلام في شرح بلوغ المرام، تأليف : عبد الله بن صالح الفوزان، الناشر : دار ابن الجوزي الطبعة : الأولى ، 1427 هـ، 1431 هـ.
تسهيل الإلمام بفقه الأحاديث من بلوغ المرام، تأليف: صالح بن فوزان بن عبد الله الفوزان، الطبعة: الأولى، 1427، 2006 م.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «إِذَا اسْتَيْقَظَ أَحَدُكُمْ مِنْ مَنَامِهِ فَلْيَسْتَنْثِرْ ثَلَاثَ مَرَّاتٍ، فَإِنَّ الشَّيْطَانَ يَبِيتُ عَلَى خَيَاشِيمِهِ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Idan ɗayanku ya farka daga baccinsa to ya face hancinsa sau uku, domin cewa Shaiɗan yana kwana akan karan hancinsa".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana kwaɗaitar da wanda ya farka daga baccinsa cewa ya face hancinsa sau uku; facewa ita ce fitar da ruwa daga hanci bayan shigar da shi, hakan domin cewa Shaiɗan yana kwana akan karan hanci - shi ne hancin gaba ɗayansa -.
Fa’idoji
- An shar'antawa dukkan wanda ya farka daga bacci ya face hanci dan gusar da gurbin Shaiɗan daga hancinsa, idan ya kasance zai yi alwala, to umarnin ya fi ƙarfafuwa a lokacin.
- Face hanci yana daga cikar fa'idar shaƙa ruwa; domin shaƙa ruwa tsarkake cikin hanci ne, facewa kuma hakan yana fitar da datti tare da ruwan.
- Ƙayyade shi da baccin dare, dan yin riƙo daga lafazin "yana kwana"; domin kwana ba ya kasancewa sai daga baccin dare, kuma cewa shi ne lokacin zatan tsawaitawa da zirfafawa.
- A cikin hadisin akwai dalili akan cakuɗuwar Shaiɗan ga mutum alhali shi ba ya jin hakan.
Madogara
صحيح البخاري (4/ 126) (3295).
صحيح مسلم (1/ 212) (238).
توضيح الأحكام، للشيخ للبسام (1/ 211).
سُبل السلام، للصنعاني (1/ 64).
فتح ذي الجلال والإكرام بشرح بلوغ المرام، لابن عثيمين (1/ 179).
منحة العلَّام، لعبد الله الفوزان (1/ 166).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن عبد الله بن زيد رضي الله عنه مرفوعاً: «أن النبي صلى الله عليه وسلم أُتِيَ بِثُلُثَيْ مُدٍّ فجعل يَدْلُكُ ذِرَاعَه».
Daga Abdullahi Dan Umar - Allah ya yarda da shi - zuwa ga Annabi : "Lallai cewa Annabi SAW ya zo da xaya bisa Ukun Mudu sai yake shafawa a Dantsensa"
Ibn Khuzaimah ya rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara
مسند الإمام أحمد، تأليف: أحمد بن محمد بن حنبل، تحقيق: شعيب الأرناؤوط وغيره، الناشر: الناشر: مؤسسة الرسالة ، الطبعة: الأولى، 1421 هـ.
صحيح ابن خزيمة، تأليف: أبو بكر محمد بن إسحاق بن خزيمة ، المحقق: د. محمد مصطفى الأعظمي، الناشر: المكتب الإسلامي، بيروت.
توضيح الأحكام مِن بلوغ المرام، تأليف: عبد الله بن عبد الرحمن بن صالح البسام، الناشر: مكتبة الأسدي، مكة المكرّمة الطبعة: الخامِسَة، 1423 هـ - 2003 م.
التعليقات الحسان على صحيح ابن حبان وتمييز سقيمه من صحيحه، وشاذه من محفوظه، محمد ناصر الدين الألباني، الناشر: دار باوزير للنشر والتوزيع، الطبعة: الأولى، 1424 هـ - 2003 م.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن عبد الله بن زيد رضي الله عنه يَذْكُر أنه: «رأى رسول الله صلى الله عليه وسلم توضأ فَمَضْمَض، ثم اسْتَنْثَرَ، ثم غسل وجهه ثلاثا، ويَدَه اليُمنى ثلاثا والأخرى ثلاثا، ومسح برأسه بماء غير فَضْلِ يَدِهِ، وغسل رجْلَيْه حتى أنْقَاهُما».
Daga Abdullahi Bn Zaid -Allah ya yarda da shi- yana bayanin cewa shi: "Lallai cewa shi yaga Manzon Allah SAW yayi Al-wala sai ya yi Alwala sai ya kuskure bakinsa, sannan ya face, sannan ya wanke fuskarsa sau Uku,da hannunsa na Dama sau Uku, xayanma sau uku, kuma ya shafi kansa da Ruwa ba na ragowar hannunsa ba, kuma ya wanke Qafarsa har ya tsaftace ta"
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Lallai cewa Manzon Allah SAW yayi Al-wala sai ya yi Alwala sai ya kuskure bakinsa, sannan ya face, sannan ya wanke fuskarsa sau Uku,da hannunsa na Dama sau Uku, xayanma sau uku, kuma ya shafi kansa da Ruwa ba na ragowar hannunsa ba, kuma ya wanke Qafarsa har ya tsaftace ta
Madogara
المنهاج شرح صحيح مسلم، تأليف: محيي الدين يحيى بن شرف النووي، الناشر: دار إحياء التراث العربي، الطبعة: الثانية 1392هـ.
مرعاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح، تأليف: عبيد الله بن محمد المباركفوري، الناشر: إدارة البحوث العلمية والدعوة والإفتاء، الطبعة: الثالثة - 1404هـ.
فتح ذي الجلال والإكرام، شرح بلوغ المرام، تأليف: محمد بن صالح بن محمد العثيمين، الناشر: المكتبة الإسلامية، تحقيق: صبحي بن محمد رمضان، وأُم إسراء بنت عرفة.
توضِيحُ الأحكَامِ مِن بُلوُغ المَرَام، للبسام، نشر: مكتَبة الأسدي، مكّة المكرّمة، الطبعة: الخامِسَة، 1423هـ - 2003 م.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن المغيرة بن شعبة رضي الله عنه : أن النبي صلى الله عليه وسلم توضأ، فمسح بِنَاصِيَتِهِ، وعلى العِمَامة والخُفَّين.
Daga Mugira Bn Shu'aba -Allah ya yarda da shi- Lallai cewa Annabi SAW yayi Al-wala sai ya shafi tsakiyar kansa, da kuma kan Rawaninsa da Huffinsa
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara
صحيح مسلم، تأليف: مسلم بن الحجاج النيسابوري، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي الناشر: دار إحياء التراث العربي – بيروت.
سبل السلام شرح بلوغ المرام، تأليف: محمد بن إسماعيل بن صلاح الصنعاني، الناشر: دار الحديث الطبعة: بدون طبعة وبدون تاريخ.
توضيح الأحكام مِن بلوغ المرام، تأليف: عبد الله بن عبد الرحمن بن صالح البسام، الناشر: مكتبة الأسدي، مكة المكرّمة الطبعة: الخامِسَة، 1423 هـ - 2003 م.
منحة العلام في شرح بلوغ المرام، تأليف: عبد الله بن صالح الفوزان، الناشر: دار ابن الجوزي الطبعة: الأولى، 1427 هـ - 1431 هـ.
تسهيل الإلمام بفقه الأحاديث من بلوغ المرام، تأليف: صالح بن فوزان بن عبد الله الفوزان، الطبعة: الأولى، 1427 هـ - 2006 م.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن جابر بن عبد الله رضي الله عنهما قال: كان النبي صلى الله عليه وسلم إذا توضأ أدار الماء على مِرْفَقَيْهِ.
Daga Jabir Allah ya yarda da shi ya ce: Manzon Allah SAW ya kasance idan yayi Al-wala yakan kwaranya ruwa akan Damatsensa
Al-Baihaki ne Ya Rawaito shi - Al-Dar Al-Kutni Ya Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Hadisin yana bayanin cewa yana daga cikin Farillan Alwala wanke Hannaye zuwa tsintsiyar Hannu, da kuma qarfafawa kan game guiwar hannu yana cikinsu a wajen wanke hannaye
Madogara
سنن الدارقطني، تحقيق: شعيب الأرنؤوط وآخرون، ط1، مؤسسة الرسالة، بيروت، لبنان، 1424 هـ.
سنن البيهقي الكبرى، أحمد بن الحسين بن علي أبو بكر البيهقي، مكتبة دار الباز - مكة المكرمة ، 1414 – 1994، تحقيق: محمد عبد القادر عطا.
السلسلة الصحيحة، المؤلف: محمد ناصر الدين الألباني، الناشر: مكتبة المعارف – الرياض, الطبعة الأولى, 1422ه.
تسهيل الإلمام بفقه الأحاديث من بلوغ المرام للحافظ أحمد بن علي بن حجر العسقلاني، شرحه الشيخ د. صالح بن فوزان الفوزان، اعتنى بإخراجه: عبد السلام السليمان، ط 1، 1427ه/2006م.
توضيح الأحكام من بلوغ المرام للحافظ أحمد بن علي بن حجر العسقلاني، عبدالله بن عبد الرحمن البسام ، مكتبة الأسدي، مكة، ط الخامسة، 1423هـ.
منحة العلام في شرح بلوغ المرام، تأليف عبد الله بن صالح الفوزان، ط 1، 1427هـ، دار ابن الجوزي - الرياض.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comKowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com