Abdullahi Dan Zaid - Allah Ya yarda da shi - yana bayyana siffar alwalar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi a aikace, sai ya nemi karamar kwarya (buta) ta ruwa, a farko sai ya fara da wanke tafukansa, sannan ya karkatar da kwaryar ya zuba ruwa sai ya wankesu sau uku a wajen kwaryar, sannan ya shigar da hannunsa a cikin kwaryar ya kanfato daga gareta kanfata uku yana kuskurar baki a kowacce kanfata yana shaka ruwa yana facewa, sannan ya kanfato daga kwaryar (butar) sai ya wanke fuskarsa sau uku, sannan ya kanfato daga gareta sai ya wanke hannayensa zuwa gwiwoyin hannaye sau biyu-biyu, sannan ya shigar da hannayensa cikin kwaryar, ya shafi kansa da hannayensa ya fara da magabacin kansa har ya kai zuwa keyarsa saman wuya, sannan ya dawo da su har ya kai gurin da ya fara daga gare shi, sannan ya wanke kafafuwansa tare da idan sawu.
- yanayin malami shi ne mafi kusancin hanyoyi zuwa fahimta da tabbatar da ilimi, daga hakan koyarwa a aikace.
- halaccin maimaitawa sau uku a wasu daga gabobin alwala da yi sau biyu a sashinsu, wajibi (shi ne) sau daya.
- Wajabcin jerantawa tsakanin gabban alwala kamar yadda ya zo a cikin hadisin.
- Iyakar fuska daga matsirar gashin kai na al'ada zuwa abinda ya sauka daga gemu da haba a tsawo, daga kunne zuwa kunne a fadi.
صحيح البخاري (1/ 48) (186). صحيح مسلم (1/ 210) (235). الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري (1/ 18). الإفهام في شرح عمدة الأحكام، لابن باز (ص72). تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، لعبد الله البسام (ص29). تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام، لابن عثيمين (1/ 27). شرح العمدة للسعدي (ص 50).