Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Idan ɗayanku ya farka daga baccinsa to ya face hancinsa sau uku, domin cewa Shaiɗan yana kwana akan karan hancinsa

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «إِذَا اسْتَيْقَظَ أَحَدُكُمْ مِنْ مَنَامِهِ فَلْيَسْتَنْثِرْ ثَلَاثَ مَرَّاتٍ، فَإِنَّ الشَّيْطَانَ يَبِيتُ عَلَى خَيَاشِيمِهِ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Idan ɗayanku ya farka daga baccinsa to ya face hancinsa sau uku, domin cewa Shaiɗan yana kwana akan karan hancinsa".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana kwaɗaitar da wanda ya farka daga baccinsa cewa ya face hancinsa sau uku; facewa ita ce fitar da ruwa daga hanci bayan shigar da shi, hakan domin cewa Shaiɗan yana kwana akan karan hanci - shi ne hancin gaba ɗayansa -.

Fa’idoji
  1. An shar'antawa dukkan wanda ya farka daga bacci ya face hanci dan gusar da gurbin Shaiɗan daga hancinsa, idan ya kasance zai yi alwala, to umarnin ya fi ƙarfafuwa a lokacin.
  2. Face hanci yana daga cikar fa'idar shaƙa ruwa; domin shaƙa ruwa tsarkake cikin hanci ne, facewa kuma hakan yana fitar da datti tare da ruwan.
  3. Ƙayyade shi da baccin dare, dan yin riƙo daga lafazin "yana kwana"; domin kwana ba ya kasancewa sai daga baccin dare, kuma cewa shi ne lokacin zatan tsawaitawa da zirfafawa.
  4. A cikin hadisin akwai dalili akan cakuɗuwar Shaiɗan ga mutum alhali shi ba ya jin hakan.
Madogara

صحيح البخاري (4/ 126) (3295). صحيح مسلم (1/ 212) (238). توضيح الأحكام، للشيخ للبسام (1/ 211). سُبل السلام، للصنعاني (1/ 64). فتح ذي الجلال والإكرام بشرح بلوغ المرام، لابن عثيمين (1/ 179). منحة العلَّام، لعبد الله الفوزان (1/ 166).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
SIFFAR ALWALA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com