Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi alwala sau ɗaiɗai

عَنِ ‌ابْنِ عَبَّاسٍ رضي الله عنهما قَالَ: تَوَضَّأَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ مَرَّةً مَرَّةً.
Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi alwala sau ɗaiɗai.
Bukhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance a sashin lokutansa idan zai yi alwala sai ya wanke kowacce gaɓa daga gaɓɓan alwalarsa sau ɗaiɗai, sai ya wanke fuska - daga [cikin wanke fuska] akwai kuskurar baki da shaƙa ruwa - da hannaye da ƙafafuwa sau ɗaiɗai, wannan shi ne gwargwadon wajibi.

Fa’idoji
  1. Wajibi a wanke gaɓɓai (shi ne) sau ɗaiɗai, abin da ya ƙaru, to, mustahabbi ne.
  2. Halaccin yin alwala sau ɗaiɗai a wasu lokuta
  3. Abin shar'anta wa a shafar kai (shi ne) sau ɗaiɗai.
Madogara

صحيح البخاري (1/ 43) (157)، إرشاد الساري لشرح صحيح البخاري (1/ 244).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
SUNNONI DA LADUBBAN ALWALA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com