عَنْ عَبْدِ اللهِ بْنِ زَيْدٍ رضي الله عنه: أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ تَوَضَّأَ مَرَّتَيْنِ مَرَّتَيْنِ.
Daga Abdullahi ɗan Zaid - Allah Ya yarda da shi -: Lallai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi alwala sau biyu-biyu.
Bukhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance a wasu lokutansa idan zai yi alwala yana wanke Kowacce gaɓa daga gaɓɓan alwalarsa sau biyu, sai ya wanke fuska - daga cikin wankewar akwai kuskurar baki da shaƙa ruwa - da hannaye da ƙafafuwa sau biyu.
Fa’idoji
- Wajibi a wanke gaɓɓan alwala (shi ne) sau ɗaya abin da ya ƙaru, to, shi mustahabbi ne.
- Halaccin alwala sau bibiyu a wasu lokutan.
- Abin shar'antawa a shafar kai (shi ne) sau ɗaya.
Madogara
صحيح البخاري (1/ 43) (158)، إرشاد الساري لشرح صحيح البخاري (1/ 244).