Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

ALWALA

Hadisai 37

Idan dayanku zai yi alwala to ya sanya ruwa a hancinsa sannan ya face, wanda zai yi tsarkin hoge to ya yi shi wutiri

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «إِذَا تَوَضَّأَ أَحَدُكُمْ فَلْيَجْعَلْ فِي أَنْفِهِ ثُمَّ لِيَنْثُرْ، وَمَنِ اسْتَجْمَرَ فَلْيُوتِرْ، وَإِذَا اسْتَيْقَظَ أَحَدُكُمْ مِنْ نَوْمِهِ فَلْيَغْسِلْ يَدَهُ قَبْلَ أَنْ يُدْخِلَهَا فِي وَضُوئِهِ، فَإِنَّ أَحَدَكُمْ لاَ يَدْرِي أَيْنَ بَاتَتْ يَدُهُ». ولفظ مسلم: «إِذَا اسْتَيْقَظَ أَحَدُكُمْ مِنْ نَوْمِهِ فَلَا يَغْمِسْ يَدَهُ فِي الْإِنَاءِ حَتَّى يَغْسِلَهَا ثَلَاثًا، فَإِنَّهُ لَا يَدْرِي أَيْنَ بَاتَتْ يَدُهُ».
Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: "Idan dayanku zai yi alwala to ya sanya ruwa a hancinsa sannan ya face, wanda zai yi tsarkin hoge to ya yi shi wutiri, idan dayanku ya farka daga baccinsa to ya wanke hannunsa kafin ya shigar da su a ruwan alwalarsa, domin cewa dayanku ba ya sanin a'ina hannunsa ya kasance". Lafazin Muslim: "Idan dayanku ya farka daga baccinsa kada ya nutsa hannunsa a cikin kwarya har sai ya wankesu sau uku, domin cewa shi ba ya sanin a'ina hannunsa ya sakance ".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana sashin huklunce-hukuncen tsarki, daga cikinsu: Na farko: Cewa wanda zai yi alwala to ya wajaba akansa ya shigar da ruwa a cikin hancinsa da numfashi, sannan ya fitar da shi ta numfashi kuma. Na biyu: Cewa wanda ya yi nufin tsarkake kazanta mai fita daga gareshi da gusar da ita ba tare da ruwa ba kamar duwatsu da makancinsu to tsarkakewarsa ta zama akan adadin mara mafi karancinsa uku, mafi yawa wanda zai kawar da abinda ya fita zai kuma tsarkake wurin. Na uku: Cewa wanda ya farka daga baccin dare kada ya shigar da tafinsa a cikin kwarya dan ya yi alwala har sai ya wankesu sau uku a wajen kwaryar, domin cewa shi bai san a'ina hannunsa ya kasance ba, ba zai iya amintar da najasa akan su ba, zai iya yiwuwa Shaidan ya yi wasa da su kuma ya dora abubuwa masu cutarwa garesu ga mutum ko mai bata ruwan.

Fa’idoji
  1. Shaka ruwa yana wajaba a cikin alwala, shi ne: Shigar da ruwa a cikin hanci ta hanyar numfashi, hakan nan facewa yana wajaba, shi ne: Fitar da ruwa daga hanci ta hanyar numfashi.
  2. Anso mara a tsarkin hoge.
  3. Halaccin wanke hannaye bayan baccin dare sau uku.
Madogara

صحيح البخاري (1/ 43) (162). صحيح مسلم (1/ 233) (278). تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، للبسام (ص19). الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري (1/ 11).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Idan bawa musulmi ya yi alwala - ko kuma mumini - sai ya wanke fuskar sa, to kowane kuskuren da ya yi kallo da shi da idanun sa zai fice daga fuskar sa tare da ruwa - ko kuma tare da ƙarshen ɗigon ruwa

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضيَ اللهُ عنهُ أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «إِذَا تَوَضَّأَ الْعَبْدُ الْمُسْلِمُ -أَوِ الْمُؤْمِنُ- فَغَسَلَ وَجْهَهُ خَرَجَ مِنْ وَجْهِهِ كُلُّ خَطِيئَةٍ نَظَرَ إِلَيْهَا بِعَيْنَيْهِ مَعَ الْمَاءِ -أَوْ مَعَ آخِرِ قَطْرِ الْمَاءِ-، فَإِذَا غَسَلَ يَدَيْهِ خَرَجَ مِنْ يَدَيْهِ كُلُّ خَطِيئَةٍ كَانَ بَطَشَتْهَا يَدَاهُ مَعَ الْمَاءِ -أَوْ مَعَ آخِرِ قَطْرِ الْمَاءِ-، فَإِذَا غَسَلَ رِجْلَيْهِ خَرَجَتْ كُلُّ خَطِيئَةٍ مَشَتْهَا رِجْلَاهُ مَعَ الْمَاءِ -أَوْ مَعَ آخِرِ قَطْرِ الْمَاءِ- حَتَّى يَخْرُجَ نَقِيًّا مِنَ الذُّنُوبِ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -: Lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Idan bawa musulmi ya yi alwala - ko kuma mumini - sai ya wanke fuskar sa, to kowane kuskuren da ya yi kallo da shi da idanun sa zai fice daga fuskar sa tare da ruwa - ko kuma tare da ƙarshen ɗigon ruwa - idan ya wanke hannayen sa, kowane kuskure zai fita daga hannayen sa waɗanda hannayen sa suka damƙa tare da ruwa - ko tare da ƙarshen ɗigon ruwa -, idan ya wanke ƙafafuwan sa kowane kuskuren da ƙafafuwan sa suka tafi gare shi zasu fita tare da ruwa - ko tare da ƙarshen ɗigon ruwa - har sai ya fita tsarkakakke daga zunubai".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa idan musulmi ko mumini ya yi alwala sai ya wanke fuskarsa a cikin alwalar duk ƙaramin kuskuren da ya kalla da idanuwansa zai fita daga fuskarsa tare da ruwan da ya zuba bayan wankewar ko tare da ƙarshen ɗigon ruwan, idan ya wanke hannayensa kowane ƙaramin kuskuren da hannayensa suka aikata shi zai fita daga hannayensa tare da ruwan ko tare da ƙarshen ɗigon ruwan, idan ya wanke ƙafafuwansa kowane ƙaramin kuskuren da ƙafafuwansa suka taka (zuwa gare shi) zai fita tare da ruwan ko tare da ƙarshen ɗigon ruwan har sai ya fita tsarkakke daga ƙananan zunubai idan ya gama alwalar.

Fa’idoji
  1. Falalar kiyayewa akan alwala, kuma cewa ita tana kankare zunubai.
  2. Daga shiryarwar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa shi yana kwaɗaitar da mutane a cikin ayyukan ɗa'a da kuma ibadu ta hanyar ambatan lada da sakamako akan su.
  3. Kowace gaɓa daga gaɓɓan mutum tana faɗawa cikin wani abu daga saɓo, saboda haka zunubai suke bin kowace gaɓar da ta aikatasu, kuma suna fita daga kowace gaɓar da ya tuba daga gareta.
  4. Alwala, a cikinta akwai tsarkaka ta gani ɓaro-ɓaro, kuma tana kasancewa ne a lokacin da kake wanke gaɓɓan alwala, da kuma tsarkakewa ta ma'ana tana kasancewa ne daga zunuban da suka faru daga gaɓɓan.
Madogara

صحيح مسلم (1/ 215) (244). كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (3/ 108). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (2/ 181). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 208). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 157).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Allah ba ya karbar sallar dayanku idan ya yi hadasi har sai ya yi alwala

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه عَنِ النَّبِيِّ صلى الله عليه وسلم قَالَ: «لَا يَقْبَلُ اللهُ صَلَاةَ أَحَدِكُمْ إِذَا أَحْدَثَ حَتَّى يَتَوَضَّأَ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Allah ba ya karbar sallar dayanku idan ya yi hadasi har sai ya yi alwala"
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa daga sharuddan ingancin sallah: Tsarki, to yana wajaba akan wanda ya yi nufin sallah ya yi alwala, in ya kasance wani abu mai warware alwala daga masu warware alwala ya faru agare shi; kamar bayan gida ko fitsari ko bacci ko wasunsu.

Fa’idoji
  1. Sallar wanda ba shi da tsarki ba'a karbarta har sai ya yi tsarki, da yin wanka daga babban kari da kuma alwala daga karamin kari.
  2. Alwala ita ce daukar ruwa da motsashi a baki da kuma fitar da shi, sannan jawo ruwa da numfashinsa zuwa cikin hancinsa, sannan fitar da shi da face shi, sannan wanke fuskarsa sau uku, sannan wanke hannayensa tare da gwiwoyin hannu sau uku, sannan shafar dukkanin kansa sau daya, sannan wanke kafafuwansa tare da idon sawu sau uku.
Madogara

صحيح البخاري (9/ 23) (6954). صحيح مسلم (1/ 204) (225). تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، للبسام (ص17). تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام، لابن عثيمين (1/ 11).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com