Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

FALALAR ALWALA

Hadisai 6

((Hakika Al'umata za'a kirawo su ranar Al-kiyama masu Fari da kyalkyali na daga guraben Alwala)).wanda ya sami damar tsawaita Farinsa daga gareku to ya aikata.Acikin wani Lafazi na Muslim:((Naga Aba Huraira yana Alwala,sai ya wanke Fuskarsa da Hannayensa har ya kusa isa Kafadunsa biyu,sannan ya wanke Kafafunsa biyu har saida ya daga izuwa Kaurinsa biyu,sannan yace:Na ji Manzan Allah-tsira da amincin Allah su tabbata agareshi-yana cewa:Hakika Al'umata za'a kirawo su ranar Al'kiyama masu Fari da kyalkyali na daga guraben Alwala))wanda ya sami damar tsawaita Farinsa da kyalkyalinsa to ya aikata.Kuma acikin wani lafazin na Muslim:Na ji Badadina-tsira da amincin Allah su tabbata agareshi-yana cewa:((Adon Mumini yana kaiwa inda Alwala takai((.

عن أبي هريرة رضي الله عنه قال قال رسول الله صلى الله عليه وسلم : ((إن أمتي يُدْعَون يوم القيامة غُرًّا مُحَجَلِّين من آثار الوُضُوء)). فمن اسْتَطَاع منكم أن يُطِيل غُرَّتَه فَليَفعل. وفي لفظ لمسلم: ((رأَيت أبا هريرة يتوضَّأ، فغسل وجهه ويديه حتى كاد يبلغ المنكبين، ثم غسل رجليه حتى رَفَع إلى السَّاقين، ثم قال: سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول: إنَّ أمتي يُدْعَون يوم القيامة غُرًّا مُحَجَّلِين من آثار الوُضُوء)) فمن استطاع منكم أن يطيل غُرَّتَه وتَحْجِيلَه فَليَفعَل. وفي لفظ لمسلم: سمعت خليلي صلى الله عليه وسلم يقول: ((تَبْلُغ الحِليَة من المؤمن حيث يبلغ الوُضُوء)).
((An karbo daga Abi Huraira Allah ya yarda dashi yace Manzan Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi yace:((Hakika Al'umata za'a kirawo su ranar Al-kiyama masu Fari da kyalkyali na daga guraben Alwala)).wanda ya sami damar tsawaita Farinsa daga gareku to ya aikata.Acikin wani Lafazi na Muslim:((Naga Aba Huraira yana Alwala,sai ya wanke Fuskarsa da Hannayensa har ya kusa isa Kafadunsa biyu,sannan ya wanke Kafafunsa biyu har saida ya daga izuwa Kaurinsa biyu,sannan yace:Na ji Manzan Allah-tsira da amincin Allah su tabbata agareshi-yana cewa:Hakika Al'umata za'a kirawo su ranar Al'kiyama masu Fari da kyalkyali na daga guraben Alwala))wanda ya sami damar tsawaita Farinsa da kyalkyalinsa to ya aikata.Kuma acikin wani lafazin na Muslim:Na ji Badadina-tsira da amincin Allah su tabbata agareshi-yana cewa:((Adon Mumini yana kaiwa inda Alwala takai((.
Muslim ne ya rawaito shi duka Riwar ta sa biyun - Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi tsira da aminci su tabbata agareshi yana yiwa Al'umarsa bushara da cewa hakika Allah maitsarki da daukaka yana kebantarsu da Alamar fifiko da daukaka ranar Alkiyama,a tsakanin Al'umai,ta yarda za'a kirawosu sai su zo agaban Halittu Fuskokinsu daHannayensu da Kafafuwansu suna kyalkyali na haske, wancananka gurbine daga guraben wannan Ibada maigirma,itace Alwala wacce suka dinga maimaitata abisa wannan Gabobi masu Alfarma don neman yardar Allah, da kuma neman ladansa, sai sakamakonsu ya kasance wannan girmamawar maigirma kebantacciya.Sannan Abu Huraira Allah ya yarda dashi yake cewa: "Wanda ya sami ikon tsawaita wannan Fari to ya aikata" domin cewashi duk sanda ya tsawaita bigiran wankewa daga Gaba Fari da kyalkyali zai karu, domin cewa adon Hasken yana kaiwa inda Ruwan Alwala ya kai, sai dai abin shar'antawa kawai wanke Hannaye biyu acikin Alwala ya zama zuwa gwiwar Hannaye biyu ya shigar da gwiwar da farawa da Dantse da wanke wani yanki daga gareshi, da kuma wanke Diga Digai biyu izuwa Idon sawaye biyu ya shigar da Idon sawayen biyu da farawa da kauri, kuma ba'a shara'anta wanke Dantse da kauri acikin Alwala ba

Madogara

الإلمام بشرح عمدة الأحكام لإسماعيل الأنصاري، ط1، دار الفكر، دمشق، 1381هـ. تأسيس الأحكام للنجمي، ط2، دار علماء السلف، 1414هـ. تيسير العلام شرح عمدة الأحكام للبسام، حققه وعلق عليه وخرج أحاديثه وصنع فهارسه: محمد صبحي بن حسن حلاق، ط10، مكتبة الصحابة، الإمارات - مكتبة التابعين، القاهرة، 1426هـ. تنبيه الأفهام شرح عمدة لأحكام لابن عثيمين، ط1، مكتبة الصحابة، الإمارات، 1426هـ. عمدة الأحكام من كلام خير الأنام -صلى الله عليه وسلم- لعبد الغني المقدسي، دراسة وتحقيق: محمود الأرناؤوط، مراجعة وتقديم: عبد القادر الأرناؤوط، ط2، دار الثقافة العربية، دمشق، بيروت، مؤسسة قرطبة، 1408 هـ. شرح العمدة للسعدي، قيده عنه تلميذه: عبد الله العوهلي، تقديم: عبد الله بن عبد العزيز العقيل، تحقيق: أنس بن عبد الرحمن بن عبد الله العقيل، ط1، دار التوحيد، الرياض، 1431هـ. صحيح البخاري، تحقيق: محمد زهير بن ناصر الناصر، ط1، دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم: محمد فؤاد عبد الباقي)، 1422هـ. صحيح مسلم، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي، دار إحياء التراث العربي، بيروت، 1423هـ.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Shaiɗan yana ƙulli uku akan ƙarshen kan ɗayanku idan ya yi bacci, yana buga (hannunsa) akan kowane ƙulli, ka yi dare mai tsawo, sai ka yi bacci

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «يَعْقِدُ الشَّيْطَانُ عَلَى قَافِيَةِ رَأْسِ أَحَدِكُمْ إِذَا هُوَ نَامَ ثَلاَثَ عُقَدٍ يَضْرِبُ كُلَّ عُقْدَةٍ عَلَيْكَ لَيْلٌ طَوِيلٌ، فَارْقُدْ، فَإِنِ اسْتَيْقَظَ فَذَكَرَ اللَّهَ، انْحَلَّتْ عُقْدَةٌ، فَإِنْ تَوَضَّأَ انْحَلَّتْ عُقْدَةٌ، فَإِنْ صَلَّى انْحَلَّتْ عُقْدَةٌ، فَأَصْبَحَ نَشِيطًا طَيِّبَ النَّفْسِ، وَإِلَّا أَصْبَحَ خَبِيثَ النَّفْسِ كَسْلاَنَ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Shaiɗan yana ƙulli uku akan ƙarshen kan ɗayanku idan ya yi bacci, yana buga (hannunsa) akan kowane ƙulli, ka yi dare mai tsawo, sai ka yi bacci, idan ya farka sai ya ambaci Allah, sai kulli ɗaya ya warware, idan ya yi alwala sai ƙulli ɗaya ya warware, idan ya yi sallah sai ƙulli (ɗaya) ya warware, sai ya wayi gari mai yawan nishaɗi mai daɗin rai, inba haka ba sai ya wayi gari mai mummunar rai mai yawan kasala".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin halin Shaiɗan da kuma yakinsa ga mutumin da yake nufin tsayuwa dan sallar dare ko Asuba. domin mumini idan ya tafi yin bacci shaiɗan yana ƙulli uku akan ƙyaraysa - yana nufin: Ƙarshen kansa -. Idan mumini ya farka kuma ya ambaci Allah - Maɗaukakin sarki - bai amsa waswasin shaiɗan ba; sai ƙulli (ɗaya) ya warware. Idan ya yi alwala sai ya warware. Idan ya tashi ya yi sallah sai ƙulli na uku ya warware, sai ya wayi gari mai yawan nishaɗi mai daɗin rai; dan farin cikinsa da abinda Allah Ya datar da shi na aikin ɗa'a, yana mai bushara da abinda Allah Ya yi masa alƙawari na lada da gafara, tare da abinda ya gushe daga gare shi na ƙulle-ƙullen Shaiɗan da nauyayawarsa, in ba haka ba zai wayi gari mai mummunan rai, mai baƙin ciki a zuciya, mai kasala daga ayyukan alheri da biyayya; domin cewa shi abin ɗaurewa ne da marin Shaiɗan, kuma abin nisanta daga kusancin Al-Rahman.

Fa’idoji
  1. Shaiɗan kowane lokaci yana ƙoƙari ta kowace hanya ga mutum; dan ya tsare tsakaninsa da tsakanin biyayya ga Allah - Mai girma da ɗaukaka -, kuma babu tsira ga bawa daga Shaiɗan sai da neman taimakon Allah - Mai girma da ɗaukaka -, da yin riƙo da sabubban kariya da tsari.
  2. Ambatan Allah - Maɗaukakin sarki - da bauta masa suna gadar da nishaɗi a rai da walwalar ƙirji, kuma suna kore kasala da nauyin jiki, kuma suna tafiyar da baƙin ciki da ƙiyayya; domin cewa su suna korar Shaiɗan wannan yana daga wasiwasinsa.
  3. Mumini yana farin ciki da datarwar Allah - Maɗaukakin sarki - gare shi dan tsayuwa da ɗa'arSa, kuma yana baƙin ciki dan taƙaitawarsa a matakan falala da kuma cika.
  4. Gafala da karkata daga ayyukan biyayya shi yana daga aikin Shaiɗan da kuma kyalkyalinsa.
  5. Waɗannan al'amuran guda uku - ambatan Allah, da alwala, da sallah - suna kore Shaiɗan.
  6. Ƙullin Shaiɗan akan ƙarshen kai a keɓance; domin nan ce cibiya ta ƙarfi, kuma fagene na jujjuayawrsu, idan ya yi ɗauri akansa sai ya samu damar da zai yi rinjaye akan ran mutum, da kuma jefa barci a kansa.
  7. Ibnu Hajar al-Asƙalani ya ce: Ambatan dare a cikin faɗinsa: "Na horeka da dare", zahirinsa hakan na faruwa ne a baccin dare kadai.
  8. Ibnu Hajar al-Asƙalani ya ce: Babu wani keɓantaccen abu na Zikiri da aka ware akan wannan, da za’a ce wani ba ya wadatarwa sai shi, kawai, dukkan abinda ambatan Allah ya gasgata akansa ya isar, karatun Alƙur'ni yana shiga ciki, da karatun hadisin Annabi, da shagaltuwa da ilimin shari'a, mafi cancantar abinda za'a tinatar da shi faɗin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Wanda ya farka da daddare sai ya ce: "Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kaɗai yake baShi da abokin tarayya, mulki nasa ne godiya ta tabbata gareShi, Shi Mai iko ne akan dukkan komai, godiya ta tabbata ga Allah, tsarki ya tabbata ga Allah, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Allah ne Mafi girma, babu dabara babu karfi sai ga Allah. Sannan ya ce: Ya Allah Ka gafarta mini, ko ya yi addu'a za'a amsa masa, idan ya yi alwala za'a karbi sallarsa). Bukharine ya ruwaito shi.
Madogara

صحيح البخاري (2/ 52) (1142). صحيح مسلم (1/ 538) (776). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 328). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (2/ 834). كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (15/ 305). فتح الباري شرح صحيح البخاري، لأحمد العسقلاني (10/ 564). طرح التثريب في شرح التقريب، العراقي (3/ 82).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Wanda ya yi alwala, kuma ya kyautata alwalar, laifukansa za su fita daga jikinsa har su fice ta ƙarƙashi farcensa

عن عثمان بن عفان رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «مَنْ تَوَضَّأَ فَأَحْسَنَ الْوُضُوءَ خَرَجَتْ خَطَايَاهُ مِنْ جَسَدِهِ حَتَّى تَخْرُجَ مِنْ تَحْتِ أَظْفَارِهِ».
Daga Usaman Bn Affan -Allah Ya yarda da shi- ya ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Wanda ya yi alwala, kuma ya kyautata alwalar, laifukansa za su fita daga jikinsa har su fice ta ƙarƙashi farcensa".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi tsira da amincin Allah su tabba a gare shi yana ba da labari cewa wanda ya yi alwala tare da kula da sunnonita da ladubbanta, to, hakan zai kasance daga sababi na kankare laifuka, da share kukurai, har sai zunubansa sun fita ta ƙarƙashin farcensa na hannu da ƙafa.

Fa’idoji
  1. Kwaɗaitarwa a kan koyan alwala da sunnonita da kuma ladubbanta, kana da aiki da hakan.
  2. Falalar alwala, kuma tana kankare zunubai ƙanana, amma manya sai an musu tuba.
  3. Sharaɗin fitar laifukan shi ne cika alwalar, da kuma yinta ba tare da kurakurai ba, kamar dai yadda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya bayyana.
  4. Kankare zububai a wannan Hadisin an ƙayyadeshi ne da nisantar manyan laifuka, da kuma tuba daga su, Allah maɗaukaki ya ce: Idan kuka nisanci manyan abubuwan da ake hanaku, to, zamu kankare muku laifukanku.
Madogara

صحيح مسلم (1/ 216) (245). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (5/ 9). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمصطفى الخِن وغيره (2/ 763). بهجة الناظرين، سليم الهلالي (2/ 247).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Tsarki rabin imani ne , kuma (fadin) : Alhamdulillah, (wato): godiya ta tabbata ga Allah, yana cika ma'auni, (fadin) Subhanallah, wato: tsarki ya tabbata ga Allah godiya ta tabbata ga Allah, suna cika ma'auni - ko suna cika - abinda ke tsakanin sammai da kasa

عن أبي مالكٍ الأشعريِّ رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «الطُّهُورُ شَطْرُ الْإِيمَانِ، وَالْحَمْدُ لِلهِ تَمْلَأُ الْمِيزَانَ، وَسُبْحَانَ اللهِ وَالْحَمْدُ لِلهِ تَمْلَآنِ -أَوْ تَمْلَأُ- مَا بَيْنَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ، وَالصَّلَاةُ نُورٌ، وَالصَّدَقَةُ بُرْهَانٌ، وَالصَّبْرُ ضِيَاءٌ، وَالْقُرْآنُ حُجَّةٌ لَكَ أَوْ عَلَيْكَ، كُلُّ النَّاسِ يَغْدُو، فَبَايِعٌ نَفْسَهُ فَمُعْتِقُهَا أَوْ مُوبِقُهَا».
Daga Abu Malik Al-Ash'ari - Allah Ya yarda da shi - ya ce : Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Tsarki rabin imani ne , kuma (fadin) : Alhamdulillah, (wato): godiya ta tabbata ga Allah, yana cika ma'auni, (fadin) Subhanallah, wato: tsarki ya tabbata ga Allah godiya ta tabbata ga Allah, suna cika ma'auni - ko suna cika - abinda ke tsakanin sammai da kasa, sallah haske ce, sadaka garkuwa ce, hakuri haskene, Alkur’ani hujjane gareka ko akanka, dukkanin mutane suna wayar gari, akwai mai saida kansa sai ya 'yanto ta ko ya halakar da ita".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labari: Cewa tsarki na zahiri yana kasancewa ne da alwala da wanka, kuma sharadi ne a sallah. Kuma cewa fadin: Alhamdulillah, (wato) "Godiya ta tabbata ga Allah yana cika ma'auni", shi ne godiya gare shi - tsarki ya tabbatar maSa - da kuma siffantaShi da siffofin cika, za'a auna su ranar alkiyama sai su cika ma'aunin ayyuka. Kuma fadin: Subhanallah, "Tsarki ya tabbata ga Allah godiya ta tabbata ga Allah", Shi ne tsarkake Shi daga kowacce tawaya da kuma siffantaShi da cikakken cika wanda yake dacewa da girmanSa, tare da sonSa da girmamaShi suna cika abinda ke tsakanin sammai da kasa. Kuma: "Sallah haske ce’’ ga bawa a cikin zuciyarsa, da fuskarsa, da cikin kabarinsa, da a tashinsa a taron Alkiyama. Kuma: "Sadaka garkuwace" kuma dalili ce akan gaskiyar imanin mumini, da kuma banbancinsa da munafikin da yake hanuwa daga yin ta (ita sadakar) dan kasancewarsa ba ya yin sadaka a lokacin ta. Kuma: "Hakuri haske ne" - Shi ne tsare rai daga firgici da fushi - wani haskene wanda yake da zafi da kuna, kamar hasken rana; domin shi mai wahalane, kuma yana bukatuwa ga dakewar zuciya da tsareta daga abinda take so; mai shi ba zai gushe ba yana mai haskaka , mai shiriya mai zarcewa akan daidai. Shi ne hakuri akan biyayya ga Allah, da kuma barin sabonSa, da kuma hakuri akan masifu da nau'o'in abubuwan ki a duniya. Kuma: 'Alkur’ani hujjane a gareka" ta hanyar Karanta shi da kuma aiki da shi, ko kuma "Hujjane akanka", ta hanyar barinsa ba tare da wani aiki ba, ko karantawa ba. Sannan - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa dukkanin mutane suna tafiya suna fita suna tashi daga barcinsu suna fita daga gidajensu dan ayyukansu mabanbanta, Daga cikinsu akwai mai tabbata akan biyayya ga Allah, sai ya 'yanto kansa daga wuta, daga cikinsu akwai wanda yake kaucewa daga hakan kuma yake afkawa a cikin sabo sai ya halakar da ita ta hanyar shigarta wuta.

Fa’idoji
  1. Tsaki iri biyu ne; Tsarki na zahiri, yana kasancewa ne da yin alwala da wanka, da kuma tsarkin badini yana kasancewa ne da kadaita Allah da imani da aiki na gari.
  2. Muhimmanicin kiyaye sallah, ita ce haske ga bawa a duniya da kuma ranar alkiyama.
  3. Sadaka dalili ce akan gaskiyar imani.
  4. Muhimmancin aiki da Alkur’ani da gasgata shi, dan ya zama hujja a gareka ba akanka ba.
  5. Rai idan ba ka shagaltar da ita da da'a ba, za ta shagaltar da kai da sabo.
  6. Kowanne mutum ba makawa sai ya yi aiki; kodai ya 'yanto ransa da biyayya (ga Allah) ko ya halakar da ita da sabo.
  7. Hakuri yana bukatar juriya da neman lada, kuma acikinsa akwai wahala.
Madogara

صحيح مسلم (1/ 203) (223)، شرح الأربعين لابن دقيق العيد (ص 84)، شرح الأربعين النووية للعثيمين (ص: 231)، الرياض الزكية شرح الأربعين النووية للخضير (ص 293)، فتح القوي المتين في شرح الأربعين للعباد (ص 79)

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana alwala a lokacin kowacce sallah

عن عَمْرُو بْنُ عَامِرٍ عَنْ ‌أَنَس بن مالك قَالَ: كَانَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَتَوَضَّأُ عِنْدَ كُلِّ صَلَاةٍ، قُلْتُ: كَيْفَ كُنْتُمْ تَصْنَعُونَ؟ قَالَ: يُجْزِئُ أَحَدَنَا الْوُضُوءُ مَا لَمْ يُحْدِثْ.
Daga Amr ɗan Amir daga Anas ɗan Malik ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana alwala a lokacin kowacce sallah, sai na ce: Yaya kuka kasance kuna aikatawa? sai ya ce: Alwala tana isar ɗayanmu muddin dai bai yi kari (hadasi) ba.
Bukhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana alwala a kowacce sallar farilla ko da alwalarsa ba ta karye ba, hakan don tabbatar da lada da kuma falala. Ya halatta ya sallaci sama da sallah (ɗaya) da alwala ɗaya muddin dai yana da alwala.

Fa’idoji
  1. Mafi yawancin aikin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - shi ne yin alwala ga kowace sallah; don neman mafi cika.
  2. An so yin alwala a lokacin kowace sallah.
  3. Halaccin yin sama da sallah (ɗaya) da alwala ɗaya.
Madogara

صحيح البخاري (1/ 53) (214)، شرح ابن بطّال (1/321)، إرشاد الساري لشرح صحيح البخاري (1/ 285).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Tsarki rabin imani ne, kuma (faɗin) godiya ta tabbata ga Allah, yana cika ma'auni, (faɗin) tsarki ya tabbata ga Allah godiya ta tabbata ga Allah, suna cika ma'auni - ko suna cika - abinda ke tsakanin sammai da ƙasa

عَنْ أَبِي مَالِكٍ الحَارِثِ بْنِ عَاصِمٍ الأَشْعَرِيِّ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «الطُّهُورُ شَطْرُ الْإِيمَانِ، وَالْحَمْدُ لِلهِ تَمْلَأُ الْمِيزَانَ، وَسُبْحَانَ اللهِ وَالْحَمْدُ لِلهِ تَمْلَآنِ -أَوْ تَمْلَأُ- مَا بَيْنَ السَّمَاءِ وَالأَرْضِ، وَالصَّلَاةُ نُورٌ، وَالصَّدَقَةُ بُرْهَانٌ، وَالصَّبْرُ ضِيَاءٌ، وَالْقُرْآنُ حُجَّةٌ لَكَ أَوْ عَلَيْكَ، كُلُّ النَّاسِ يَغْدُو، فَبَايِعٌ نَفْسَهُ فَمُعْتِقُهَا أَوْ مُوبِقُهَا»
Daga Abu Malik al-Haris al’Ash'ari - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Tsarki rabin imani ne, kuma (faɗin) godiya ta tabbata ga Allah, yana cika ma'auni, (faɗin) tsarki ya tabbata ga Allah godiya ta tabbata ga Allah, suna cika ma'auni - ko suna cika - abinda ke tsakanin sammai da ƙasa, sallah haske ce, sadaka garkuwa ce, haƙuri haskene, Alƙur’ani hujjane gareka ko a kanka, dukkanin mutane suna wayar gari, akwai mai saida kansa sai ya 'yanto shi ko kuma ya halakar da shi».
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labari: Cewa tsarki na zahiri yana kasancewa ne da alwala da wanka, kuma sharadi ne a sallah. Kuma cewa fadin: Alhamdulillah, (wato) "Godiya ta tabbata ga Allah yana cika ma'auni", shi ne godiya gare shi - tsarki ya tabbatar maSa - da kuma siffantaShi da siffofin cika, za'a auna su ranar alkiyama sai su cika ma'aunin ayyuka. Kuma fadin: Subhanallah, "Tsarki ya tabbata ga Allah godiya ta tabbata ga Allah", Shi ne tsarkake Shi daga kowacce tawaya da kuma siffantaShi da cikakken cika wanda yake dacewa da girmanSa, tare da sonSa da girmamaShi suna cika abinda ke tsakanin sammai da kasa. Kuma: "Sallah haske ce’’ ga bawa a cikin zuciyarsa, da fuskarsa, da cikin kabarinsa, da a tashinsa a taron Alkiyama. Kuma: "Sadaka garkuwace" kuma dalili ce akan gaskiyar imanin mumini, da kuma banbancinsa da munafikin da yake hanuwa daga yin ta (ita sadakar) dan kasancewarsa ba ya yin sadaka a lokacin ta. Kuma: "Hakuri haske ne" - Shi ne tsare rai daga firgici da fushi - wani haskene wanda yake da zafi da kuna, kamar hasken rana; domin shi mai wahalane, kuma yana bukatuwa ga dakewar zuciya da tsareta daga abinda take so; mai shi ba zai gushe ba yana mai haskaka , mai shiriya mai zarcewa akan daidai. Shi ne hakuri akan biyayya ga Allah, da kuma barin sabonSa, da kuma hakuri akan masifu da nau'o'in abubuwan ki a duniya. Kuma: 'Alkur’ani hujjane a gareka" ta hanyar Karanta shi da kuma aiki da shi, ko kuma "Hujjane akanka", ta hanyar barinsa ba tare da wani aiki ba, ko karantawa ba. Sannan - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa dukkanin mutane suna tafiya suna fita suna tashi daga barcinsu suna fita daga gidajensu dan ayyukansu mabanbanta, Daga cikinsu akwai mai tabbata akan biyayya ga Allah, sai ya 'yanto kansa daga wuta, daga cikinsu akwai wanda yake kaucewa daga hakan kuma yake afkawa a cikin sabo sai ya halakar da ita ta hanyar shigarta wuta.

Fa’idoji
  1. Tsaki iri biyu ne; Tsarki na zahiri, yana kasancewa ne da yin alwala da wanka, da kuma tsarkin badini yana kasancewa ne da kadaita Allah da imani da aiki na gari.
  2. Muhimmanicin kiyaye sallah, ita ce haske ga bawa a duniya da kuma ranar alkiyama.
  3. Sadaka dalili ce akan gaskiyar imani.
  4. Muhimmancin aiki da Alkur’ani da gasgata shi, dan ya zama hujja a gareka ba akanka ba.
  5. Rai idan ba ka shagaltar da ita da da'a ba, za ta shagaltar da kai da sabo.
  6. Kowanne mutum ba makawa sai ya yi aiki; kodai ya 'yanto ransa da biyayya (ga Allah) ko ya halakar da ita da sabo.
  7. Hakuri yana bukatar juriya da neman lada, kuma acikinsa akwai wahala.
Madogara

صحيح مسلم (1/ 203) (223). شرح الأربعين لابن دقيق العيد (ص 84). شرح الأربعين النووية للعثيمين (ص: 231). الرياض الزكية شرح الأربعين النووية للخضير (ص 293). فتح القوي المتين في شرح الأربعين للعباد (ص 79).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com