Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Wanda ya yi alwala, kuma ya kyautata alwalar, laifukansa za su fita daga jikinsa har su fice ta ƙarƙashi farcensa

عن عثمان بن عفان رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «مَنْ تَوَضَّأَ فَأَحْسَنَ الْوُضُوءَ خَرَجَتْ خَطَايَاهُ مِنْ جَسَدِهِ حَتَّى تَخْرُجَ مِنْ تَحْتِ أَظْفَارِهِ».
Daga Usaman Bn Affan -Allah Ya yarda da shi- ya ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Wanda ya yi alwala, kuma ya kyautata alwalar, laifukansa za su fita daga jikinsa har su fice ta ƙarƙashi farcensa".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi tsira da amincin Allah su tabba a gare shi yana ba da labari cewa wanda ya yi alwala tare da kula da sunnonita da ladubbanta, to, hakan zai kasance daga sababi na kankare laifuka, da share kukurai, har sai zunubansa sun fita ta ƙarƙashin farcensa na hannu da ƙafa.

Fa’idoji
  1. Kwaɗaitarwa a kan koyan alwala da sunnonita da kuma ladubbanta, kana da aiki da hakan.
  2. Falalar alwala, kuma tana kankare zunubai ƙanana, amma manya sai an musu tuba.
  3. Sharaɗin fitar laifukan shi ne cika alwalar, da kuma yinta ba tare da kurakurai ba, kamar dai yadda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya bayyana.
  4. Kankare zububai a wannan Hadisin an ƙayyadeshi ne da nisantar manyan laifuka, da kuma tuba daga su, Allah maɗaukaki ya ce: Idan kuka nisanci manyan abubuwan da ake hanaku, to, zamu kankare muku laifukanku.
Madogara

صحيح مسلم (1/ 216) (245). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (5/ 9). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمصطفى الخِن وغيره (2/ 763). بهجة الناظرين، سليم الهلالي (2/ 247).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
FALALAR ALWALA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com