Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana alwala a lokacin kowacce sallah

عن عَمْرُو بْنُ عَامِرٍ عَنْ ‌أَنَس بن مالك قَالَ: كَانَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَتَوَضَّأُ عِنْدَ كُلِّ صَلَاةٍ، قُلْتُ: كَيْفَ كُنْتُمْ تَصْنَعُونَ؟ قَالَ: يُجْزِئُ أَحَدَنَا الْوُضُوءُ مَا لَمْ يُحْدِثْ.
Daga Amr ɗan Amir daga Anas ɗan Malik ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana alwala a lokacin kowacce sallah, sai na ce: Yaya kuka kasance kuna aikatawa? sai ya ce: Alwala tana isar ɗayanmu muddin dai bai yi kari (hadasi) ba.
Bukhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana alwala a kowacce sallar farilla ko da alwalarsa ba ta karye ba, hakan don tabbatar da lada da kuma falala. Ya halatta ya sallaci sama da sallah (ɗaya) da alwala ɗaya muddin dai yana da alwala.

Fa’idoji
  1. Mafi yawancin aikin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - shi ne yin alwala ga kowace sallah; don neman mafi cika.
  2. An so yin alwala a lokacin kowace sallah.
  3. Halaccin yin sama da sallah (ɗaya) da alwala ɗaya.
Madogara

صحيح البخاري (1/ 53) (214)، شرح ابن بطّال (1/321)، إرشاد الساري لشرح صحيح البخاري (1/ 285).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
FALALAR ALWALA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com