Allah ba ya karbar sallar dayanku idan ya yi hadasi har sai ya yi alwala
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه عَنِ النَّبِيِّ صلى الله عليه وسلم قَالَ: «لَا يَقْبَلُ اللهُ صَلَاةَ أَحَدِكُمْ إِذَا أَحْدَثَ حَتَّى يَتَوَضَّأَ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Allah ba ya karbar sallar dayanku idan ya yi hadasi har sai ya yi alwala"
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa daga sharuddan ingancin sallah: Tsarki, to yana wajaba akan wanda ya yi nufin sallah ya yi alwala, in ya kasance wani abu mai warware alwala daga masu warware alwala ya faru agare shi; kamar bayan gida ko fitsari ko bacci ko wasunsu.
Fa’idoji
Sallar wanda ba shi da tsarki ba'a karbarta har sai ya yi tsarki, da yin wanka daga babban kari da kuma alwala daga karamin kari.
Alwala ita ce daukar ruwa da motsashi a baki da kuma fitar da shi, sannan jawo ruwa da numfashinsa zuwa cikin hancinsa, sannan fitar da shi da face shi, sannan wanke fuskarsa sau uku, sannan wanke hannayensa tare da gwiwoyin hannu sau uku, sannan shafar dukkanin kansa sau daya, sannan wanke kafafuwansa tare da idon sawu sau uku.
Madogara
صحيح البخاري (9/ 23) (6954).
صحيح مسلم (1/ 204) (225).
تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، للبسام (ص17).
تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام، لابن عثيمين (1/ 11).
Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com