Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

RUKUNAN ALWALA

Hadisai 2

Azabar wuta ta tabbata ga duga-dugai

عن أبي هريرة وعبد الله بن عمرو وعائشة رضي الله عنهم عن رسول الله صلى الله عليه وسلم : أنه قال: (ويلٌ للأعْقَاب من النَّار).
Daga Abu Huraira da Abdullahi Dan Amru da A'isha - Allah ya yarda dasu - daga Manzo tsira da aminci su tabbata a gare shi - yace" Azabar wuta ta tabbata ga duga - dugai,
Muslim ne ya rawaito shi - Buhari da Muslim suka rawaito shi da ruwayoyin saDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi tsira da amincin Allah yana tsoratar da al'umma game da yin wasa da lamarin alwala da kuma gaza yin ta cikakkiya, ya kuma kwadaitar da a irika yinta cikakkiya, kasncewar an fi samun lam'a a duga - dugai, ruwa baya mamaye su sosai, wanda hakan ka iya jawo matsala ga tsarki da salla, sai Annabi ya bamu labarin azaba mai tsanani ga duga - dugai da kuma mai duga- dugan mai yin wasa da alwala

Madogara

الإلمام بشرح عمدة الأحكام لإسماعيل الأنصاري، ط1، دار الفكر، دمشق، 1381هـ تيسير العلام شرح عمدة الأحكام للبسام، حققه وعلق عليه وخرج أحاديثه وصنع فهارسه: محمد صبحي بن حسن حلاق، ط10، مكتبة الصحابة، الإمارات - مكتبة التابعين، القاهرة، 1426 هـ تنبيه الأفهام شرح عمدة لأحكام لابن عثيمين، ط1، مكتبة الصحابة، الإمارات، 1426هـ عمدة الأحكام من كلام خير الأنام صلى الله عليه وسلم لعبد الغني المقدسي، دراسة وتحقيق: محمود الأرناؤوط، مراجعة وتقديم: عبد القادر الأرناؤوط، ط2، دار الثقافة العربية، دمشق، بيروت، مؤسسة قرطبة، 1408 هـ. صحيح البخاري، تحقيق: محمد زهير بن ناصر الناصر، ط1، دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم: محمد فؤاد عبد الباقي)، 1422هـ. صحيح مسلم، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي، دار إحياء التراث العربي، بيروت، 1423 هـ.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Cewa wani mutum ya yi alwala, sai ya bar tabo (Lam’a) gurin farce a kan ƙafafunsa, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya gan shi (wurin) sai ya ce: "Koma ka kyautata alwalarka" Sai ya dawo, sannan ya yi sallah

عَنْ جَابِرٍ رضي الله عنه قال: أَخْبَرَنِي عُمَرُ بْنُ الْخَطَّابِ: أَنَّ رَجُلًا تَوَضَّأَ فَتَرَكَ مَوْضِعَ ظُفُرٍ عَلَى قَدَمِهِ فَأَبْصَرَهُ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَقَالَ: «ارْجِعْ فَأَحْسِنْ وُضُوءَكَ» فَرَجَعَ، ثُمَّ صَلَّى.
Daga Jabir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Umar Dan Alkhaddab ya bani labari: Cewa wani mutum ya yi alwala, sai ya bar tabo (Lam’a) gurin farce a kan ƙafafunsa, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya gan shi (wurin) sai ya ce: "Koma ka kyautata alwalarka" Sai ya dawo, sannan ya yi sallah.
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne a baki dayan ruwayoyin sa
Sharhi

Umar - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ga wani mutum ya gama alwalarsa, sai ya bar gwargwadan farce a ƙafarsa (Lam’a) ruwa bai same shi ba, sai ya ce masa yana mai nuni zuwa gurin da bai sami ruwa ba: Ka koma ka kyautata alwalarka ka cikata ka ba wa kowacce gaba haƙƙinta na ruwa. Sai mutumin ya koma ya cika alwalarsa, sannan ya yi sallah.

Fa’idoji
  1. Wajabcin gaggawa zuwa horo da aikin alheri, da fadakar da wanda bai sani ba da rafkananne, musamman ma idan barnar ta kasance lalacewar ibadarsa za ta kasance akan akan barnar.
  2. Wajabcin game gabban alwala da ruwa, kuma cewa wanda ya bar wani yanki daga gaba - koda ƙarami ne - alwala ba ta ingantuwa daga gare shi, kuma sakewa ce ta wajaba idan ya jima kafin ya gani.
  3. Halaccin kyautata alwala, hakan ta hanyar cikata da kyautata akan yadda aka yi umarni da ita a shari'ance.
  4. Kafafuwa biyu suna daga gabban alwala, kuma shafa ba ta isuwa a cikinsu, kawai babu makawa sai an wanke su.
  5. Jerantawa, yana kamata tsakanin gabban alwala, ta yadda zai wanke kowacce gaba kafin ta gabaninta ta bushe.
  6. Rashin sani da mantuwa ba sa sarayar da wajibi, kawai suna sarayar da zunubi ne, wannan mutumin wanda bai kyautata alwalarsa ba saboda rashin sani, Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi bai sarayar masa da wajibi ba, wato alwala, kawai ya umarce shi ya saketa.
Madogara

صحيح مسلم (1/ 215) (243). توضيح الأحكام مِن بلوغ المرام، لعبد الله البسام (1/ 247). شرح سنن أبي داود، لعبد المحسن العباد (29/ 13 بترقيم الشاملة آليا).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com