عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «مَا يَزَالُ البَلاَءُ بِالمُؤْمِنِ وَالمُؤْمِنَةِ فِي نَفْسِهِ وَوَلَدِهِ وَمَالِهِ حَتَّى يَلْقَى اللَّهَ وَمَا عَلَيْهِ خَطِيئَةٌ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Bala'i ba zai gushe ga mumini da mumina ba a kansa da ɗansa da dukiyarsa har sai ya gamu da Allah ba shi da wani laifi".
Tirmizi da Ahmad sun rawaito shiDarajaHasan ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa bala'i da jarraba ba zasu gushe ba ga bawa mumini da mumina, a kansa da lafiyarsa da jikinsa, da 'ya'yansa na rashin lafiya ko mutuwa ko sabawa ko wanin haka, haka a dukiyarsa na bukatuwa da tafiya kasuwanci da sata, da tawayar rayuwa da kunci a cikin arziki, har Allah Ya kankare masa dukkanin zunubansa da kurarkuransa da wannan bala'in har idan ya gamu da Allah zai zama ya tsarkaka daga dukkan zunubai da kurakuran da ya aikata.
Fa’idoji
- Daga cikin rahamar Allah ga bayinSa muminai shi ne ya kankare musu zunubansu a duniyarsu ta hanyar wasu masibu na duniya da aibobinta.
- Bala'i shi akarankansa yana kankare zunubai da sharaɗin imani, idan bawa ya yi hakuri bai yi fushi ba za'a ba shi lada.
- Kwaɗaitarwa akan hakuri a dukkan al'amura, cikin abinda yake so da abinda yake ki, ya yi hakuri har ya bada abinda Allah Ya wajabta masa, kuma ya yi hakuri har ya nisanci abinda Allah Ya haramta, yana kwaɗayin ladan Allah, kuma yana tsoron ukubarSa.
- FaɗinSa: "Da mumini da mumina", karin lafazin mumina a cikinsa akwai dalili akan karin karfafawa ga mace; in ba haka ba da ya ce: "Da mumini" da mace ta shiga cikinsa; domin hakan ba ya kebantar namiji, idan bala'i ya afkawa mace to haka itama an yi mata alkawari da kwatankwacin wannan sakamakon na kankare zunubai da kurakurai.
- Falalar da ta jerantu akan bala'i tana daga abinda zai sawwakawa bawa abinda yake gamuwa da shi na raɗaɗi akai akai.
Madogara
سنن الترمذي (4/ 204) (2399).
مسند أحمد (13/ 248) (7859).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 113).
تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص51).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (1/ 273).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 80).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ صُهَيْبٍ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «عَجَبًا لِأَمْرِ الْمُؤْمِنِ، إِنَّ أَمْرَهُ كُلَّهُ خَيْرٌ، وَلَيْسَ ذَاكَ لِأَحَدٍ إِلَّا لِلْمُؤْمِنِ، إِنْ أَصَابَتْهُ سَرَّاءُ شَكَرَ، فَكَانَ خَيْرًا لَهُ، وَإِنْ أَصَابَتْهُ ضَرَّاءُ صَبَرَ، فَكَانَ خَيْرًا لَهُ».
Daga Suhaib - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce -: ’’Lamarin mumini da ban mamaki yake, dukkannin al’amuransa alheri ne, kuma hakan ba ya kasancewa ga kowa sai ga mumini ,idan abin farinciki ne ya same shi sai ya gode wa Allah sai, sai ya zamar masa alheri, idan kuma na sharri ne ya same shi sai ya yi haƙuri, shi ma sai ya zamar masa alheri’’.
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
(Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi yana mamaki daga sha'anin mumini da halayensa ta ɓangaren kyautatawa; hakan domin halayensa dukkansu alheri ne, kuma hakan ba ya kasancewa ga wani sai ga mumini; Idan farin ciki ya same shi sai ya godewa Allah; sai ya samu lada saboda godiyarsa. Idan kuma cuta ta same shi sai ya yi haƙuri ya nemi lada a wurin Allah, sai ya samu lada saboda haƙuri, shi a kowanne hali yana cikin lada.
Fa’idoji
- Falalar godiya akan farin ciki da kuma haƙuri akan cuta, wanda ya aikata hakan alherin duniya da na lahira za su same shi, wanda bai godewa ni'ima ba, kuma bai yi haƙuri akan musiba ba, to lada ya wuce shi, kuma zai samu zunubi.
- Falalar imani, kuma cewa lada a kowanne hali ba ya kasancewa sai ga ma'abota imani.
- Godiya a lokacin farin ciki, da haƙuri akan cuta suna daga ɗabi'un mumini.
- Imani da hukuncin Allah da kuma ƙaddararSa yana sanya mumini a cikin cikakkiyar yarda a kowanne halinsa, saɓanin wanin mumini wanda yake kasancewa a cikin fushi, idan ya sami Ni’ima daga Allah madaukakin sarki sai ya shagalta da ita daga biyayya ga Allah, amadadin haka ma sai ya juyar da ita a saɓonSa.
Madogara
صحيح مسلم (4/ 2295) (2999).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 82).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (1/ 197).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 59).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن أنس بن مالك رضي الله عنه قال: «إنكم لتعملون أعمالا هي أَدَقُّ في أعينكم من الشَّعْرِ، كنا نَعُدُّهَا على عهد رسول الله - صلى الله عليه وسلم - من المُوبِقَاتِ».
Daga Anas -Allah ya yarda da shi- ya ce: "Lallai ku wallahi kuna yin wasu Ayyuka mafi siranta daga gashi a Idanuwanku, mu kuma muna xaukar su a lokacin Manzon Allah SAW suna cikin Masu Hallakarwa"
Buhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين لسليم الهلالي، ط1، دار ابن الجوزي، الدمام، 1415ه.
تطريز رياض الصالحين للشيخ فيصل المبارك، ط1، تحقيق: عبد العزيز بن عبد الله آل حمد، دار العاصمة، الرياض، 1423 هـ.
دليل الفالحين لطرق رياض الصالحين لمحمد علي بن محمد بن علان، ط4، اعتنى بها: خليل مأمون شيحا، دار المعرفة،بيروت، 1425 ه.
رياض الصالحين للنووي، ط1، تحقيق: ماهر ياسين الفحل، دار ابن كثير، دمشق، بيروت، 1428 هـ.
كنوز رياض الصالحين، مجموعة من الباحثين برئاسة حمد بن ناصر العمار، ط1، كنوز إشبيليا، الرياض، 1430هـ.
صحيح البخاري، تحقيق: محمد زهير بن ناصر الناصر، ط1، دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم: محمد فؤاد عبد الباقي)، 1422ه.
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين لمجموعة من الباحثين، ط14، مؤسسة الرسالة، 1407هـ.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن أنس -رضي الله عنه - أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: "إذا أراد الله بعبده الخير عجل له العقوبة في الدنيا، وإذا أراد بعبده الشر أمسك عنه بذنبه حتى يُوَافِيَ به يومَ القيامة".
Daga Anas -Allah ya yarda da shi- Manzon Allah -Tsira da Amincin Allah su tabbata gare shi- ya ce: "Idan Allah ya so Alkairi ga bawansa sai ya gaggauta masa Ukuba tun daga Duniya, kuma Idan ya so Sharri da Bawansa sai ya kame ga barin kamashi da laifinsa har sai yaje Ranar Lahira.
Al-Tirmithi Ya Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Manzon Allah -Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi- cewa daga Alamar son Allah bawan sa da Alkairi yayi masa Magani da yi masa wata ukuba akan zunubansa a cikin Duniya har ya futa daga Duniya kuma babu komai akansa na zunubi da za'a kama shi da shi Ranar Alkiyama; domin cewa duk wanda akai masa Ukuba a Duniya ti Ukubarsa a Lahira zatayi Sauki, kuma yana daga cikin Alamomin nufin Sharri ga bawa a yi watsi da shi da Zunubansa a Duniya har yaje Ranar Al-kiyama da Tarin zunubansa har Allah ya yi masa sakamako da abunda ya cancance shi Ranar Alkiyama.
Madogara
الملخص في شرح كتاب التوحيد، للشيخ صالح الفوزان, دار العاصمة, الطبعة الأولى، 1422ه.
الجديد في شرح كتاب التوحيد، لمحمد بن عبد العزيز السليمان القرعاوي, تحقيق: محمد بن أحمد سيد, مكتبة السوادي، الطبعة: الخامسة، 1424ه.
جامع الترمذي, تحقيق: أحمد شاكر, شركة مكتبة ومطبعة مصطفى البابي, الطبعة: الثانية، 1395هـ.
صحيح الجامع الصغير, للألباني, المكتب الإسلامي.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن النُّعمان بن بَشير رضي الله عنه قال: سَمِعْتُ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ -وَأَهْوَى النُّعْمَانُ بِإِصْبَعَيْهِ إِلَى أُذُنَيْهِ-: «إِنَّ الْحَلَالَ بَيِّنٌ وَإِنَّ الْحَرَامَ بَيِّنٌ، وَبَيْنَهُمَا مُشْتَبِهَاتٌ لَا يَعْلَمُهُنَّ كَثِيرٌ مِنَ النَّاسِ، فَمَنِ اتَّقَى الشُّبُهَاتِ اسْتَبْرَأَ لِدِينِهِ وَعِرْضِهِ، وَمَنْ وَقَعَ فِي الشُّبُهَاتِ وَقَعَ فِي الْحَرَامِ، كَالرَّاعِي يَرْعَى حَوْلَ الْحِمَى يُوشِكُ أَنْ يَرْتَعَ فِيهِ، أَلَا وَإِنَّ لِكُلِّ مَلِكٍ حِمًى، أَلَا وَإِنَّ حِمَى اللهِ مَحَارِمُهُ، أَلَا وَإِنَّ فِي الْجَسَدِ مُضْغَةً، إِذَا صَلَحَتْ صَلَحَ الْجَسَدُ كُلُّهُ، وَإِذَا فَسَدَتْ فَسَدَ الْجَسَدُ كُلُّهُ، أَلَا وَهِيَ الْقَلْبُ».
Daga Nu'umanu dan Bashir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa : - sai Nu'uman ya sakko da 'yan yatsunsa zuwa kunnuwansa -: "Lallai halal a bayyane yake kuma haram ma a bayyane yake, a tsakaninsu akwai wasu al'amura masu rikitarwa da yawa daga mutane ba sa saninsu, wanda ya kiyaye shubuhohi ya kuɓuta a addininsa da mutuncinsa, wanda ya afka cikin shubuhohi ya afka a cikin haram, kamar mai kiwo ne da yake kiwo a gefen shinge ya kusata ya yi kiwo a cikinsa, ku saurara! lallai kowane sarki yana da shinge, ku saurara! lallai shingen Allah shi ne abubuwan da ya haramta, ku saurara lallai! Lallai a jiki akwai wata tsoka, idan ta gyaru jiki ya gyaru dukkaninsa, idan ta ɓaci jiki ya ɓaci dukkaninsa, ku saurara! ita ce zuciya".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana wata ƙa'ida mai gamewa game da abubuwa, cewa sun kasu a shari'a zuwa kashi uku: Bayyanannen halal, da bayyanannen haram, da al'amura masu rikitarwa waɗanda hukuncinsu ba a bayyane yake ba ta bangaren halacci da haramci, da yawa daga mutane basa sanin hukuncinsu.
Wanda ya bar waɗannan abubuwan masu rikitarwa gareshi, to, addininsa ya kuɓuta ta hanyar nisanta daga fadawa a cikin haram, kuma mutuncinsa ya kuɓuta daga zancen mutane da abin da za su dinga aibatashi a kansa saboda aikata wannan abin rikitarwar. Wanda bai nisanci shubuhohi ba, to, haƙiƙa ya kai kansa ko dai ga faɗawa a cikin haram, ko aibatawar mutane ga mutuncinsa. Kuma Manzo - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya buga misali don ya bayyana halin wanda yake aikata shubuhohi, kuma cewa shi kamar mai kiwo ne da yake kiwon dabbobinsa kusa da ƙasar da mai ita ya sa mata shinge, dabbobin mai kiwon sun kusa su yi kiwon a cikin wannan shingen don kusancinsu gareshi, to, haka nan wanda yake aikata a bin da a cikinsa akwai shubha, to, shi da wannan ɗin yana kusantowa ga haram, kuma yana kusa da ya afka cikinsa. Bayan wannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ba da labarin cewa a cikin jiki akwai wata tsoka (ita ce zuciya) jiki yana gyaruwa da gyaruwarta, kuma yana ɓaci da ɓacinta.
Fa’idoji
- Kwaɗaitarwa a kan barin abu mai rikitarwa wanda hukuncinsa bai bayyana ba.
Madogara
صحيح البخاري (1/ 20) (52).
صحيح مسلم (3/ 1219) (1599).
التحفة الربانية في شرح الأربعين حديثا النووية (ص18).
شرح الأربعين النووية، لابن عثيمين (ص105).
فتح القوي المتين في شرح الأربعين وتتمة الخمسين، للعباد (ص41).
فتح الباري لابن حجر (4/ 291).
شرح النووي على مسلم (11/ 28).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ عُمَرَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا قَالَ: أَخَذَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ بِمَنْكِبِي، فَقَالَ: «كُنْ فِي الدُّنْيَا كَأَنَّكَ غَرِيبٌ أَوْ عَابِرُ سَبِيلٍ»، وَكَانَ ابْنُ عُمَرَ، يَقُولُ: إِذَا أَمْسَيْتَ فَلاَ تَنْتَظِرِ الصَّبَاحَ، وَإِذَا أَصْبَحْتَ فَلاَ تَنْتَظِرِ المَسَاءَ، وَخُذْ مِنْ صِحَّتِكَ لِمَرَضِكَ، وَمِنْ حَيَاتِكَ لِمَوْتِكَ.
Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ka kasance a duniya kamar kai baƙo ne ko mai ƙetare hanya", Ibnu Umar ya kasance yana cewa:
Idan ka kai maraice to kada ka saurari safiya, idan ka wayi gari to kada ka saurari yammaci, ka yi riƙo daga lafiyarka dan rasshin lafiyarka, kuma daga rayuwarka dan mutuwarka.
Bukhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Ibnu Umar - Allah Ya yarda da shi - ya ambata cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya riƙe kafaɗarsa - ita ce mahaɗar damuttsa da allan kafaɗa - kuma ya ce masa:
Ka kasance a duniya kamar kai baƙo ne, wanda ya zo garin da ba shi da masauki a cikinsa da zai sauka, kuma babu wani mazaunin da zai kwantar masa da rai, ya kaɗaita daga iyalai da 'yan uwa, waɗanda sune sababin shagalta daga Mahalicci, kai ka kasance mafi tsanani daga baƙo shi ne mai ƙetare hanya mai neman ƙasarsa; domin cewa baƙo zai iya zama a garuruwan baƙunta kuma ya zauna a cikinsu, saɓanin mai ketare hanya mai nufin gari, domin cewa daga sha'aninsa saukakawa da rashin tsayuwa, da kwadayi akan saduwa da garinsa, kamar yadda matafiyi ba ya bukatuwa ga sama da abinda zai kai shi zuwa karshen tafiyarsa, haka nan mumini ba ya bukatuwa a duniya sama da abinda zai kai shi wuri.
Sai Ibnu Umar ya yi aiki da wannan nasihar kuma ya kasance yana cewa: Idan ka wayi gari to kada ka jira maraice, idan ka shiga maraice to kada ka jira safiya, ka ƙirga kanka a cikin ma'abota ƙaburbura, kuma cewa rayuwa ba ta kaɗaita daga lafiya da rashin lafiya. Ka yi gaggawa a lokutan lafiyarka da aikin ɗa'a dan rashin lafiyarka; ka ribaci ayyuka na gari a cikin lafiya kafin rashin lafiya ta tsare tsakaninka da su, ka ribaci rayuwarka a duniya, ka tara abinda zai anfaneka bayan mutuwarka.
Fa’idoji
- Ɗora tafin hannun malami akan kafaɗar ɗalibi a lokacin koyarwa dan natsarwa da kuma faɗakarwa.
- Farawa da nasiha da shiryarwa ga wanda yake neman hakan.
- Kyakkyawar koyarwar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da buga misalai masu wadatarwa, da faɗinsa: "Ka kasance a duniya kamar kai baƙo ne ko mai ketare hanya".
- Saɓanin mutane a tafiyarsu zuwa lahira; mai ƙetare hanya, matsayi ne mafi ɗaukaka a zuhudu daga matsayin baƙo.
- Bayanin ƙaranta buri, da yi wa mutuwa tanadi.
- Hadisin ba ya nuni akan barin arziƙi da haramta abubuwan jin daɗin duniya; sai dai yana nuni akan kwaɗaitarwa a cikin zuhudu a cikinta, da ƙarantawa daga gareta.
- Gaggawa zuwa ga ayyuka na gari kafin lokacin da ba shi da iko akansu, rashin lafiya ko mutuwa su tsare.
- Falalar Abdullahi ɗan Umar - Allah - Ya yarda da su - yayin da ya tasirantu da wannan wa'azin daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
- Ƙasar muminai ita ce aljanna, mutum baƙo ne a duniya, shi matafiyi ne zuwa gidan lahira, kada ya ratayar da zuciyarsa da wani abu daga baƙunta, kai zuciyarsa mai rataya ce da ƙasarsa wacce zai koma gareta, zamansa a duniya dan ya biya buƙatarsa ne da kuma shirinsa dan komawa zuwa ƙasarsa.
Madogara
صحيح البخاري (8/ 89) (6416).
التحفة الربانية في شرح الأربعين حديثًا النووية، لإسماعيل الأنصاري (ص90).
شرح الأربعين النووية، لابن عثيمين (ص390).
فتح القوي المتين في شرح الأربعين وتتمة الخمسين، للنووي وابن رجب (ص131).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «لَا تَحَاسَدُوا، وَلَا تَنَاجَشُوا، وَلَا تَبَاغَضُوا، وَلَا تَدَابَرُوا، وَلَا يَبِعْ بَعْضُكُمْ عَلَى بَيْعِ بَعْضٍ، وَكُونُوا عِبَادَ اللهِ إِخْوَانًا الْمُسْلِمُ أَخُو الْمُسْلِمِ، لَا يَظْلِمُهُ وَلَا يَخْذُلُهُ، وَلَا يَحْقِرُهُ التَّقْوَى هَاهُنَا» وَيُشِيرُ إِلَى صَدْرِهِ ثَلَاثَ مَرَّاتٍ «بِحَسْبِ امْرِئٍ مِنَ الشَّرِّ أَنْ يَحْقِرَ أَخَاهُ الْمُسْلِمَ، كُلُّ الْمُسْلِمِ عَلَى الْمُسْلِمِ حَرَامٌ، دَمُهُ، وَمَالُهُ، وَعِرْضُهُ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce : Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Kada ku yi hassada, kuma kada ku yi cinikin koɗe (shi ne wani ya zo sayan wani abu sai wani a kasuwar wanda ba ya nufin sayan sai ya zo ya ce a siyar mini a kaza sai ya faɗi sama da kuɗin kayan), kuma kada ku yi gaba, kada ku juyawa juna baya, kuma kada wani ya yi ciniki akan cinikin wani, ku zama bayin Allah 'yan uwan juna Musulmi ɗan uwan musulmi ne, kada ya zalince shi kuma kada ya ƙi taimakonsa, kada ya wulaƙanta shi tsoron Allah a nan yake" - ya yi nuni zuwa ƙirjin sa, sau uku - "Ya ishi mutum sharri ya wulaƙanta ɗan uwansa Musulmi, kowane Musulmi akan Musulmi haramun ne (ya zubda) jininsa, da dukiyarsa da mutuncinsa". Mutuncinsa".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi wa musulmi wasiyya ta alheri ga ɗan'uwansa musulmi, kuma ya bayyana sashin abinda yake wajaba akansa na wajibai da ladubba daura da su; daga hakan: Wasiyya ta farko: Kada ku yi wa juna hassada, ita ce sashinku ya yi burin gushewar ni'imar sashi. Na biyu: Kada ku yi cinikin koɗe shi ne mutumin da ba ya nufin yin siyan abin siyan sai ya yi ƙari a farashin abin siyan; kawai yana nufin anfanar mai siyarwar, ko cutar da mai siyan. Na uku: Kada ku yi ƙiyayya, ita ce nufin shigar da cuta kuma ita ce kishiyar soyayya; sai dai idan ƙiyayyar ta kasance ne a lamarin Allah ne - Maɗaukakin sarki -; to shi wajibi ce. Na huɗu: Kada ku juyawa juna baya, shi ne kowane ɗaya daga cikinku ya juyawa ɗan'uwansa bayansa da ƙeyarsa sai ya bijire masa kuma ya ƙaurace masa. Na biyar: Kada sashinku ya yi ciniki akan cinikin sashi, shi ne yacewa mai siyan: A wurina akwai irinta da ƙasa da farashinta ko ta fita kyau kuma farashinta bai kai nata ba. Sannan tsira da aminci su tabbata a gare shi ya yi wasiyya da wasiyya mai tattaro (ma'anoni da hikimomi masu yawa) sai ya ce: Ku zama kamar 'yan'uwa ta hanyar barin abubuwan da aka hana, da kuma nuna soyayya da sassauci da tausayi da sauƙaƙawa da taimakekeniya a aikin alheri, tare da tsarkakakkiyar zuciya da kuma yin nasiha a kowane hali. Daga abinda wannan 'yan uwantakar take hukuntawa: Kada ya zalinci ɗan'uwansa musulmi kuma ya yi ta'addanci akansa. Kada ya bari a zalinci ɗan'uwansa sai ya ƙi taimakonsa a gurin da yake da ikon ya taimake shi, kuma ya ɗauke masa zalincin. Kuma kada ya wulaƙanta shi ya raina shi ya dinga kallonsa da kallo na raini da izgili; shi mai fitowa ne daga girman kai a cikin zuciya. Sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana har sau uku cewa tsoron Allah a cikin zuciya yake, wanda a cikin zuciyarsa akwai tsoron Allah wanda yake hukunta kyakkyawar ɗabi'a, da tsoron Allah da muraƙabarSa to cewa shi ba zai wulaƙanta musulmi ba, kuma ya ishe shi ɗabi'u na sharri da ƙasƙanci ya wulaƙanta ɗan'uwansa musulmi, hakan saboda girmankan dake cikin zuciyarsa. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ƙarfafa hakan abinda ya wuce cewa kowane musulmi akan musulmi haramun ne: jininsa: Shi ne ya yi masa ta'addanci da kisa ko abinda bai kai kisa ba kamar rauni ko duka da makamancinsu, haka nan dukiyarsa: Shi ne ya ci dukiyar ba tare da wani haƙƙi ba, haka nan mutuncinsa: Shi ne ya zarge shi a kansa ko tsareshi.
Fa’idoji
- Umarni da dukkan abinda 'yan uwantaka ta imani take hukunta wa, da kuma hani daga binda yake kishiyantarta na maganganu da ayyuka.
- Madogarar tsoron Allah ita ce abinda ke cikin zuciya na sanin Allah, da tsoronSa da muraƙabarSa, kuma wannan taƙawar taba fitowa ne daga ayyuka na gari.
- Kaucewa ta zahiri tana nuni akan raunin taƙawa ta zuciya.
- Hani daga cutar da musulmi ta kowace fuska daga fuskoki na magana ne ko aiki.
- Ba hassada ba ne musulmi ya yi burin ya zama tamkar waninsa, ba tare da burin gushewar (ni'ima ba) daga wani, wannan ana kiransa kishi; kuma wannan ya halatta yana taimako akan rigegeniya zuwa ayyukan alheri.
- A ɗabi'ar mutum yana ƙin ace wani ya fishi a wani abu na falaloli, to idan ya so gushewarta daga ɗayan to wannan ita ce hassada, idan kuma ya so rigegeniya to wannan shi ne kishin da ya halatta.
- Idan ya bayyanawa mai saye cewa mai siyarwar ya ha'ince shi ha'inci mai muni a cikin siyansa to wannan ba ya cikin cinikin musulmi akan cinikin ɗan'uwansa; kai wannan yana daga mahukuntar nasiha, amma da sharaɗin niyyarsa ta zama ita ce yi wa ɗan'uwansa mai siye nasiha ba wai cutar da mai siyarwar ba, ayyuka kuwa (ana musu hukunci ne) da niyyoyi.
- Idan musu cinikin ba su yarda da cinikin ba kuma farashin bai tabbata ba to hakan ba ya daga cikin ciniki akan cinikin ɗan'uwansa.
- Kiyayya saboda Allah ba ta cikin ƙiyayyar da aka yi hani a kanta a cikin hadisin, kai shi wajibi ne ma, kuma yana daga mafi amintakar igiyar imani.
Madogara
صحيح مسلم (4/ 1986) (2564).
التحفة الربانية في شرح الأربعين حديثًا النووية، لإسماعيل الأنصاري (ص79).
شرح الأربعين النووية، لابن عثيمين (ص339).
فتح القوي المتين في شرح الأربعين وتتمة الخمسين، النووي وابن رجب (ص118).
الأحاديث الأربعون النووية وعليها الشرح الموجز المفيد، لعبد الله المحسن (ص67).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضيَ اللهُ عنهُ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «انْظُرُوا إِلَى مَنْ أَسْفَلَ مِنْكُمْ، وَلَا تَنْظُرُوا إِلَى مَنْ هُوَ فَوْقَكُمْ، فَهُوَ أَجْدَرُ أَلَّا تَزْدَرُوا نِعْمَةَ اللهِ عَلَيْكُمْ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Ku yi duba zuwa ga wanda yake ƙasa da ku, kada ku yi duba zuwa ga wanda yake sama da ku, hakan zai sa (ku godewa Allah) ba za ku raina ni’imominSa gareku ba».
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya umarci musulmi ya yi duba a cikin al'amuran duniya a matsayi da dukiya da kuma alfarma da wasunsu zuwa ga wanda yake ƙasa da shi a hali, kuma kada ya yi duba a cikin al'amuran duniyarsa zuwa ga na sama da shi wanda ya fi shi, domin wannan duban zuwa ga na ƙasa shi ne mafi cancantar da zai sa ba zaka wulaƙanta ni'imar Allah gareka ba.
Fa’idoji
- Wadatar zuci tana daga mafi girman ɗabi'un muminai, kuma ita alama ce akan yarda da ƙaddarar Allah.
- Ibnu Jarir ya ce: Wannan hadisi ne mai tattaro nau’ukan alheri; domin mutum idan ya ga wata falala a kansa a duniya sai ransa ya nemi irin hakan, kuma ya raina a binda ke gurinsa na ni'imar Allah - Maɗaukakin sarki - kuma ya yi kwaɗayin ƙari dan ya risku da hakan ko abinda ke kusa da hakan, wannan abinda ke faruwa ne a mafi yawancin mutane, amma idan ya yi duba a cikin al'amuran duniya zuwa ga wanda baikai shi ba a cikinta sai ni'imar Allah - Maɗaukakin sarki - ta bayyana agare shi, sai ya gode mata ya yi tawali'u, ya kuma aikata alheri a cikinsa.
Madogara
صحيح البخاري (8/ 102) (6490).
صحيح مسلم (4/ 2275) (2963).
كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (7/ 261).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 534).
تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص316).
توضيح الأحكام من بلوغ المرام ، لعبد الله البسام (7/ 287).
منحة العلام شرح بلوغ المرام، لعبد الله الفوزان (10/ 17).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comKowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com