Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

’’Lamarin mumini da ban mamaki yake, dukkannin al’amuransa alheri ne, kuma hakan ba ya kasancewa ga kowa sai ga mumini

عَنْ صُهَيْبٍ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «عَجَبًا لِأَمْرِ الْمُؤْمِنِ، إِنَّ أَمْرَهُ كُلَّهُ خَيْرٌ، وَلَيْسَ ذَاكَ لِأَحَدٍ إِلَّا لِلْمُؤْمِنِ، إِنْ أَصَابَتْهُ سَرَّاءُ شَكَرَ، فَكَانَ خَيْرًا لَهُ، وَإِنْ أَصَابَتْهُ ضَرَّاءُ صَبَرَ، فَكَانَ خَيْرًا لَهُ».
Daga Suhaib - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce -: ’’Lamarin mumini da ban mamaki yake, dukkannin al’amuransa alheri ne, kuma hakan ba ya kasancewa ga kowa sai ga mumini ,idan abin farinciki ne ya same shi sai ya gode wa Allah sai, sai ya zamar masa alheri, idan kuma na sharri ne ya same shi sai ya yi haƙuri, shi ma sai ya zamar masa alheri’’.
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

(Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi yana mamaki daga sha'anin mumini da halayensa ta ɓangaren kyautatawa; hakan domin halayensa dukkansu alheri ne, kuma hakan ba ya kasancewa ga wani sai ga mumini; Idan farin ciki ya same shi sai ya godewa Allah; sai ya samu lada saboda godiyarsa. Idan kuma cuta ta same shi sai ya yi haƙuri ya nemi lada a wurin Allah, sai ya samu lada saboda haƙuri, shi a kowanne hali yana cikin lada.

Fa’idoji
  1. Falalar godiya akan farin ciki da kuma haƙuri akan cuta, wanda ya aikata hakan alherin duniya da na lahira za su same shi, wanda bai godewa ni'ima ba, kuma bai yi haƙuri akan musiba ba, to lada ya wuce shi, kuma zai samu zunubi.
  2. Falalar imani, kuma cewa lada a kowanne hali ba ya kasancewa sai ga ma'abota imani.
  3. Godiya a lokacin farin ciki, da haƙuri akan cuta suna daga ɗabi'un mumini.
  4. Imani da hukuncin Allah da kuma ƙaddararSa yana sanya mumini a cikin cikakkiyar yarda a kowanne halinsa, saɓanin wanin mumini wanda yake kasancewa a cikin fushi, idan ya sami Ni’ima daga Allah madaukakin sarki sai ya shagalta da ita daga biyayya ga Allah, amadadin haka ma sai ya juyar da ita a saɓonSa.
Madogara

صحيح مسلم (4/ 2295) (2999). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 82). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (1/ 197). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 59).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
TSARKAKE ZUKATA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com