Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Ku yi duba zuwa ga wanda yake ƙasa da ku, kada ku yi duba zuwa ga wanda yake sama da ku, hakan zai sa (ku godewa Allah) ba za ku raina ni’imominSa gareku ba

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضيَ اللهُ عنهُ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «انْظُرُوا إِلَى مَنْ أَسْفَلَ مِنْكُمْ، وَلَا تَنْظُرُوا إِلَى مَنْ هُوَ فَوْقَكُمْ، فَهُوَ أَجْدَرُ أَلَّا تَزْدَرُوا نِعْمَةَ اللهِ عَلَيْكُمْ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Ku yi duba zuwa ga wanda yake ƙasa da ku, kada ku yi duba zuwa ga wanda yake sama da ku, hakan zai sa (ku godewa Allah) ba za ku raina ni’imominSa gareku ba».
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya umarci musulmi ya yi duba a cikin al'amuran duniya a matsayi da dukiya da kuma alfarma da wasunsu zuwa ga wanda yake ƙasa da shi a hali, kuma kada ya yi duba a cikin al'amuran duniyarsa zuwa ga na sama da shi wanda ya fi shi, domin wannan duban zuwa ga na ƙasa shi ne mafi cancantar da zai sa ba zaka wulaƙanta ni'imar Allah gareka ba.

Fa’idoji
  1. Wadatar zuci tana daga mafi girman ɗabi'un muminai, kuma ita alama ce akan yarda da ƙaddarar Allah.
  2. Ibnu Jarir ya ce: Wannan hadisi ne mai tattaro nau’ukan alheri; domin mutum idan ya ga wata falala a kansa a duniya sai ransa ya nemi irin hakan, kuma ya raina a binda ke gurinsa na ni'imar Allah - Maɗaukakin sarki - kuma ya yi kwaɗayin ƙari dan ya risku da hakan ko abinda ke kusa da hakan, wannan abinda ke faruwa ne a mafi yawancin mutane, amma idan ya yi duba a cikin al'amuran duniya zuwa ga wanda baikai shi ba a cikinta sai ni'imar Allah - Maɗaukakin sarki - ta bayyana agare shi, sai ya gode mata ya yi tawali'u, ya kuma aikata alheri a cikinsa.
Madogara

صحيح البخاري (8/ 102) (6490). صحيح مسلم (4/ 2275) (2963). كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (7/ 261). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 534). تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص316). توضيح الأحكام من بلوغ المرام ، لعبد الله البسام (7/ 287). منحة العلام شرح بلوغ المرام، لعبد الله الفوزان (10/ 17).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
TSARKAKE ZUKATA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com