Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Ka fadamin wata magana a Musulunci da ba zan tambayi waninka game da ita ba, ya ce: "Ka ce na yi imani da Allah, sannan ka tabbatu akan hakan

عَنْ أَبِي عَمْرٍو- وَقِيلَ: أَبِي عَمْرَةَ-، سُفْيَانَ بْنِ عَبْدِ اللَّهِ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: قُلْتُ: يَا رَسُولَ اللهِ، قُلْ لِي فِي الْإِسْلَامِ قَوْلًا لَا أَسْأَلُ عَنْهُ أَحَدًا غَيْرَكَ، قَالَ: «قُلْ: آمَنْتُ بِاللهِ، ثُمَّ اسْتَقِمْ».
Daga Abu Amr kuma an ce: Abu Amrata - Sufyan ibnu Abdullahi - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ce: Ya Manzon Allah, Ka fadamin wata magana a Musulunci da ba zan tambayi waninka game da ita ba, ya ce: "Ka ce na yi imani da Allah, sannan ka tabbatu akan hakan".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Sahabi Sufayanu dan Abdullahi - Allah Ya yarda da shi - ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da ya sanar da shi wata magana mai tattaro ma'anonin Musulunci, da zai yi riko da ita, wacce ba zai tambayi waninsa game da ita ba? Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Ka ce: Na kadaita Allah, kuma na yi imani da cewa Shi ne Ubangijina kuma Allah na, Mahaliccina, Abin bautata na gaskiya ba Shi da abokin tarayya, Sannan ya jawu ga biyayya ga Allah ta hanyar bada farillan Allah, da barin abubuwan da Allah Ya haramta, ya kuma ci gaba akansu.

Fa’idoji
  1. Asalin Addini shi ne imani da Allah da UbangidantakarSa da AllantakarSa da sunayenSa da siffofinSa.
  2. Muhimmancin tabbatuwa bayan imani, da kuma ci gaba a cikin ibada, da tabbata akan hakan.
  3. Imani sharadi ne na karbar ayyuka.
  4. Imani da Allah, ya kunshi abinda kudire shi yake wajaba daga akidun imani da tushensu, da abinda yake bin hakan, daga ayyukan zuciyoyi, da jawuwa da mika wuya ga Allah a badini da zahiri.
  5. Tabbatuwa lazimtar hanya ce, ta hanyar aikata wajibai da barin abubuwan da aka hana.
Madogara

صحيح مسلم (1/ 65) (38). مسند أحمد (24/ 141) (15416). المفهم (1/137). جامع العلوم والحكم (1/507). فتح القوي المتين للعباد (ص 76). شرح الأربعين النووية لعبد الكريم الخضير (ص 285). شرح الأربعين لصالح آل الشيخ (ص 305).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
IMANI DA ALLAH MAI GIRMA DA ƊAUKAKA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com