Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

LADUBBAN CI DA SHA

Hadisai 20

Idann dayanku ya ci abinci to kar ya goge hannunsa har sai ya sude shi.

عَنْ ابْنِ عَبَّاسٍ رضي الله عنهما أَنَّ النَّبِيَّ صلى الله عليه وسلم قَالَ: ««إذَا أَكَلَ أَحَدُكُمْ طَعَامًا فَلا يَمْسَحْ يَدَهُ حَتَّى يَلْعَقَهَا، أَوْ يُلْعِقَهَا».
Daga Dan Abbas Allah ya yarda da su" Annabi tsira da amincin Allah ya ce: Idann dayanku ya ci abinci to kar ya goge hannunsa har sai ya sude shi.
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi mai tsira da amincin Allah ya umarci wanda ya ci wani abinci kada ya goge hannunsa, ko kar ya wanke hannaunsa har sai ya sude shi ko yasa a sude masa domin bai san a ina albarkar abincin take ba, don haka ne Annabi ya yi umarni da sude yatsun, ba mamaki albarka na cikin abin da ya makale a jikin hannaun.

Madogara

صحيح البخاري، تحقيق: محمد زهير بن ناصر الناصر، ط1، دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم: محمد فؤاد عبد الباقي)، 1422هـ. صحيح مسلم، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي، دار إحياء التراث العربي، بيروت، 1423هـ. الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري، ط1، دار الفكر، دمشق، 1381هـ. تأسس الأحكام للنجمي، ط2، دار علماء السلف، 1414هـ. عمدة الأحكام من كلام خير الأنام صلى الله عليه وسلم، لعبد الغني المقدسي، دراسة وتحقيق: محمود الأرناؤوط، مراجعة وتقديم: عبد القادر الأرناؤوط، ط2، دار الثقافة العربية، دمشق، بيروت، مؤسسة قرطبة، 1408هـ. تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، للبسام، حققه وعلق عليه وخرج أحاديثه وصنع فهارسه: محمد صبحي بن حسن حلاق، ط10، مكتبة الصحابة، الإمارات - مكتبة التابعين، القاهرة، 1426هـ.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

"Duk abun Shan da ya sa Maye to Haramun ne"

عن عائشة رضي الله عنها: «أَنَّ رسول الله صلى الله عليه وسلم سُئِل عن الْبِتْعِ؟ فقال: كل شَرَابٍ أَسْكَر فهو حَرَامٌ».
An rawaito daga Nana Aisha -Allah ya yarda da ita: "Cewa Manzon Allah SAW an tambayr shi game da tsumi sai ya ce: "Duk abun Shan da ya sa Maye to Haramun ne"
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara

- صحيح البخاري، تحقيق: محمد زهير بن ناصر الناصر، ط1، دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم: محمد فؤاد عبد الباقي)، 1422ه. - صحيح مسلم، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي، دار إحياء التراث العربي، بيروت، 1423 هـ - عمدة الأحكام من كلام خير الأنام صلى الله عليه وسلم لعبد الغني المقدسي، دراسة وتحقيق: محمود الأرناؤوط، مراجعة وتقديم: عبد القادر الأرناؤوط، ط2، دار الثقافة العربية، دمشق ، بيروت، مؤسسة قرطبة، 1408 هـ - تأسيس الأحكام للنجمي، ط2، دار علماء السلف، 1414هـ. - الإلمام بشرح عمدة الأحكام لإسماعيل الأنصاري، ط1، دار الفكر، دمشق، 1381ه - تيسير العلام شرح عمدة الأحكام للبسام، حققه وعلق عليه وخرج أحاديثه وصنع فهارسه: محمد صبحي بن حسن حلاق، ط10، مكتبة الصحابة، الإمارات - مكتبة التابعين، القاهرة، 1426 هـ.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Haramta giya ya sauka ne kuma ana yin ta daga abubuwa biyar ne: inibi, dabino, zuma, alkama, da sha'ir"

عن عَبْدُ الله بن عمر رضي الله عنهما أن عمر قال -على منبر رسول الله- صلى الله عليه وسلم : "أما بعد، أيها الناس، إنه نزل تحريم الخمر وهي من خمسة: مِنَ العنب، والتمر، والعسل، والحنطة، والشعير. والخمر: مَا خَامَرَ العَقْلَ. ثَلاثٌ وَدِدْتُ أَنَّ رَسُولَ الله صلى الله عليه وسلم كَانَ عَهِدَ إلَيْنَا فِيهَا عَهْداً نَنْتَهِي إلَيْهِ: الجَدُّ، والكَلالَةُ، وأَبْوَابٌ مِنَ الرِّبَا".
Daga Abdullah Dan Umar -Allah ya yarda da su- cewa Umar ya ce:- yana kan minbarin Manzon Allah tsira da aminci su tabbata a gare shi:" Bayan haka, ya ku mutane,tabbas hukuncin haramta giya ya sauka alhaliana yin ta ce daga abubuwa biyar: Inibi,da Zuma,da Alkama da Sha'ir; bin da ake cewa giya: Shi ne duk abin da zai gusar da hankali
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Umar Dan Khaddab -Allah ya yarda da shi- ya yi huduba a masallaci Manzon Allah -tsira da aminci su tabbata a gare shi- kuma akan minbarinsa, kuma ya tabbatar da cewa lallai giya itaa ce duk wani abu da zai iya jirkita hankali, ba wacce aka yi da inibi ba kawai, duk wani abin sha wanda zai iyi jirkita hankali ko da kuwa da dabino ko zuma ko alkama to suma sun zama giya, kuma hakika Uma r ya fadi abubuwa uku a cikin Hudubarsa wanda akawai rikitarwa a cikinsa kuma yayi burin ace Annabi yana raye, cikim wadan nan abubuwa guda uka da ya da aka kure matuka izuwa gare shi sune Gadon Kaka, da Gadon Mamacin da bashi da Da ko Mahaifi, da wasu abubuwa kan Riba, kuma Alhamdulillah cewa lallai Hukuncin wannan abubuwa guda uku sananne ne, kuma wannan ba yana nufin cewa Annabi baiyi bayaninsu ba Hakika Annabi ya Isar da Sakonsa, kuma ya bada Amana, kuma ya isar da sakon Allah abun da yafi wannan ma buya da kuma wanda ya fi wannan ma girma kuma Umar yana son yakasance akawai nassi gwari gwari ne a kansu da baya bukatar wani Ijtihadi.

Madogara

صحيح البخاري، محمد بن إسماعيل البخاري الجعفي، تحقيق: محمد زهير الناصر، دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم: محمد فؤاد عبد الباقي)، الطبعة: الأولى 1422هـ. صحيح مسلم، مسلم بن الحجاج القشيري النيسابوري، تحقيق محمد فؤاد عبد الباقي، دار إحياء التراث العربي، بيروت، الطبعة: 1423هـ. تأسيس الأحكام، أحمد بن يحيى النجمي، دار علماء السلف، الطبعة: الثانية 1414هـ. تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، عبد الله بن عبد الرحمن البسام، تحقيق: محمد صبحي حلاق، مكتبة الصحابة، الإمارات، مكتبة التابعين، القاهرة، الطبعة: العاشرة 1426هـ. عمدة الأحكام من كلام خير الأنام -صلى الله عليه وسلم- لعبد الغني المقدسي، دراسة وتحقيق: محمود الأرناؤوط، مراجعة وتقديم: عبد القادر الأرناؤوط، دار الثقافة العربية، دمشق، بيروت، مؤسسة قرطبة، الطبعة: الثانية 1408هـ. المعجم الوسيط، مجمع اللغة العربية بالقاهرة، (إبراهيم مصطفى، أحمد الزيات، حامد عبد القادر، محمد النجار)، الناشر: دار الدعوة.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Kada ɗayanku ya kuskura ya taɓa azzakarinsa da damansa, a halin yana fitsari, kuma kada ya yi tsarki na bayan gida da damansa, ko kuma ya yi nunfashi a ƙwarya

عَنْ أَبِي قَتَادَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «لَا يُمْسِكَنَّ أَحَدُكُمْ ذَكَرَهُ بِيَمِينِهِ وَهُوَ يَبُولُ، وَلَا يَتَمَسَّحْ مِنَ الْخَلَاءِ بِيَمِينِهِ، وَلَا يَتَنَفَّسْ فِي الْإِنَاءِ».
Daga Abu Katada - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Kada ɗayanku ya kuskura ya taɓa azzakarinsa da damansa, a halin yana fitsari, kuma kada ya yi tsarki na bayan gida da damansa, ko kuma ya yi nunfashi a ƙwarya".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana wasu ladubba; yayin da ya hana mutum ya riƙe azzakarinsa a halin fitsari da hannunsa na dama, ko kuma a gusar da najasa daga gaba ko baya da hannun dama; domin dama an tanadeta ne dan manyan abubuwa, kamar yadda ya yi hani mutum ya yi numfashi a cikin ƙwaryar (kofi) da yake sha acikinta.

Fa’idoji
  1. Bayanin rigayar musulunci a ladubba da tsafta.
  2. Nisantar abubuwan ƙazanta, idan an yi buƙatuwa zuwa taɓa su, to ya kasance da hagu ne.
  3. Bayanin matsayin dama da falalarta akan hagu.
  4. Cikar shari'ar musulunci da tarowar koyarwarta.
Madogara

صحيح البخاري (1/ 42) (154). صحيح مسلم (1/ 225) (267). تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، للبسام (ص41). تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام، لابن عثيمين (1/ 45).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Cewa wani mutum ya ci a wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da hannun hagunsa, sai Ma’aikin Allah ce da shi: "Ka ci da hannun damanka ." Ya ce: Ba zan iya ba. Ya ce: "Ba za ko ka iya ba

عَنْ سَلَمَةَ بْنِ الْأَكْوَعِ رضي الله عنه: أَنَّ رَجُلًا أَكَلَ عِنْدَ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ بِشِمَالِهِ، فَقَالَ: «كُلْ بِيَمِينِكَ»، قَالَ: لَا أَسْتَطِيعُ، قَالَ: «لَا اسْتَطَعْتَ»، مَا مَنَعَهُ إِلَّا الْكِبْرُ، قَالَ: فَمَا رَفَعَهَا إِلَى فِيهِ.
Daga Salamah Dan Akwa'a - Allah Ya yarda da shi -: Cewa wani mutum ya ci a wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da hannun hagunsa, sai Ma’aikin Allah ce da shi: "Ka ci da hannun damanka ." Ya ce: Ba zan iya ba. Ya ce: "Ba za ko ka iya ba", ba abin da ya hana shi sai girman kai, ya ce: Bai kara daga shi zuwa bakinsa ba.
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ga wani mutum yana ci da hannunsa na hagu, sai ya umarce shi da ya ci da hannunsa na dama, sai mutumin ya amsa masa dan girman kai da karya da cewa shi ba zai iya ba! sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi mummunan addu'a akansa da haramta masa ci da dama, sai Allah Ya amsa addu'arsa da shanyewar hannunsa na dama, bai kara daga shi zuwa bakinsa ba bayan hakan da abinci ko abin sha.

Fa’idoji
  1. wajabcin ci da dama, da haramcin ci da hagu.
  2. Girman kai daga aikata hukunce-hukuncen shari'a mai aikata shi yana cancantar ukuba.
  3. Girmamawar Allah ga AnnabinSa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da amsa addu'arsa.
  4. Halaccin umarni da aikin alheri da hani daga abin ki a kowanne hali har a cikin halin ci.
Madogara

صحيح مسلم (3/ 1599) (2021). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 239). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 183). كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (3/ 396).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

‌Lallai Shaiɗan yana halatta abin cin da ba'a ambaci sunan Allah a kansa ba

عَنْ حُذَيْفَةَ رَضيَ اللهُ عنه قَالَ: كُنَّا إِذَا حَضَرْنَا مَعَ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ طَعَامًا لَمْ نَضَعْ أَيْدِيَنَا حَتَّى يَبْدَأَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَيَضَعَ يَدَهُ، وَإِنَّا حَضَرْنَا مَعَهُ مَرَّةً طَعَامًا، فَجَاءَتْ جَارِيَةٌ كَأَنَّهَا تُدْفَعُ، فَذَهَبَتْ لِتَضَعَ يَدَهَا فِي الطَّعَامِ، فَأَخَذَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ بِيَدِهَا، ثُمَّ جَاءَ أَعْرَابِيٌّ كَأَنَّمَا يُدْفَعُ فَأَخَذَ بِيَدِهِ، فَقَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «إِنَّ الشَّيْطَانَ يَسْتَحِلُّ الطَّعَامَ أَنْ لَا يُذْكَرَ اسْمُ اللهِ عَلَيْهِ، وَإِنَّهُ جَاءَ بِهَذِهِ الْجَارِيَةِ لِيَسْتَحِلَّ بِهَا فَأَخَذْتُ بِيَدِهَا، فَجَاءَ بِهَذَا الْأَعْرَابِيِّ لِيَسْتَحِلَّ بِهِ فَأَخَذْتُ بِيَدِهِ، وَالَّذِي نَفْسِي بِيَدِهِ، إِنَّ يَدَهُ فِي يَدِي مَعَ يَدِهَا».
Daga Huzaifa - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Mun kasance idan muka halarci abinci tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ba ma sanya hannuwanmu har sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya fara sanya hannunsa, kuma mu wani lokaci mun halarci abinci tare da shi, sai wata kunyanga ta zo kai ka ce ana turota ne, sai ta tafi dan ta sanya hannunta a cikin abincin, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya riƙe hannunta, sannan wani balaraben ƙauye ya zo, kai kace ana turo shi ne, sai ya riƙe hannunsa, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «‌Lallai Shaiɗan yana halatta abin cin da ba'a ambaci sunan Allah a kansa ba, kuma shi (shaidan) ya zo da wannan kuyangar ne dan ya halatta shi da ita sai na riƙe hannunta, sai ya zo da wannan balaraben ƙauyen dan ya halatta shi da shi, sai na riƙe hannunsa, lallai hannunsa yana cikin hannuna tare da hannunta».
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Huzaifa - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa su idan suka halarci abinci tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - basa sanya hannayensu a cikin abin cin har sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya fara ya sanya hannunsa, cewa mu wani lokaci mun halarci abinci tare da shi, sai wata kuyanga (baiwa) ta zo saboda tsananin saurinta kai ka ce ana turota, sai ta tafi dan ta sanya hannunta a cikin abin cin, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya riƙe hannunta, sannan wani balaraben ƙauye ya zo kai ka ce ana turo shi ne, sai ya riƙe hannunsa kafin ya taɓa abin cin, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbat agare shi - ya ce: Lallai Shaiɗan yana samun dama a cikin abin ci idan ya fara cinsa ba tare da ambatan Allah - Maɗaukakin sarki - ba, lallai ya zo da wannan kuyangar ne dan ya halatta cin abin cin da ita sai na riƙe hannunta, sai ya zo da wannan balaraben ƙauyen dan ya halatta abin cin da shi, sai na riƙe hannunsa, na rantse da wanda raina yake a hannunsa, lallai hannun Shaiɗan yana hannuna tare da hannunta, sannnan ya ambaci sunan Allah ya ci.

Fa’idoji
  1. Girmamawar da sahabbai suke yi wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da kuma ladabinsu tare da shi.
  2. yana cikin ladabin cin abin ci shi ne yaro ya jira sai babba da mai daraja ya fara cin abin cin.
  3. Shaiɗan yana tunkuɗo wasu daga cikin rafkanannu dan wasu ayyukan da shi ya yarda da su; dan ya samu damar kaiwa ga manufarsa, yana daga hakan abinda ke cikin wannan hadisin.
  4. Nawawi ya ce: Malamai sun ce: An so ya bayyana Bismillah dan wani ma ya ji sai ya faɗakar da shi akanta.
  5. Idan wani ya zo yana so ya ci abin ci baka ji shi ya ambaci sunan Allah ba to ka riƙe hannunsa har sai ya ambaci sunan Allah.
  6. Wajabcin canza abin ƙi ga wanda yake masani, da kuma canza abin ƙi da hannu ga wanda yake da iko.
  7. Wannan hadisin aya ce daga cikin ayoyin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, inda Allah - Maɗaukakin sarki - Ya sanar da shi abinda ya faru a cikin wannan ƙissar.
  8. Shaiɗan ba ya samun damar cin abin cin masu imani saidai idan ba'a ambaci sunan Allah a kansa ba.
  9. An so koyawa mutane ladabin ci da sha a cikin Musulunci.
  10. An so rantsuwa; dan ƙarfafa umarni ga mai ji.
  11. Nawawi ya ce: Ambatan Allah a shan ruwa da nono da zuma da miya da magani da sauran abubuwan sha kamar ambatan Allah ne a abin ci.
  12. Nawawi ya ce: Da a ce zai bar ambatan Allah a farkon abinci da gangan ko da mantuwa ko da jahilci ko tilasta masa aka yi ko ya kasa dan wani abu mai bijirowa sannan ya samu damar yi a tsakiyar cin abin cin nasa to an so ya ambaci Allah sai ya ce: “Bismillahi awwalahu wa ãkhirahu”. Ma’ana: (Da sunan Allah a farkonsa da ƙarshensa); saboda faɗinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: "Idan ɗayanku zai ci abin ci to ya ambaci sunan Allah, idan ya manta ambatan sunan Allah a farkonsa to ya ce: Da sunan Allah a farkonsa da ƙarshensa". Abu Dawud ne ya ruwaito shi.
Madogara

صحيح مسلم (3/ 1597) (2017). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 51). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (4/ 192). كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (10/ 202). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 600).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Allah ya albarkace ku da ɗan abinci biyu

عن عائشة رضي الله عنها كان رسولُ اللهِ صلى الله عليه وسلم يَأْكُلُ طَعَامًا في سِتَّةٍ مِنْ أَصْحَابِهِ، فَجَاءَ أَعْرَابِيٌّ، فَأَكَلَهُ بِلُقْمَتَيْنِ، فقال رسولُ اللهِ صلى الله عليه وسلم : «أَمَا إِنَّهُ لَوْ سَمَّى لَكَفَاكُمْ».
A kan Aisha, Allah ya yarda da ita, Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cin sahabbansa shida, don haka wani Badawiyi ya zo, kuma ya ci shi da bakinku, don haka ya ce: "Allah ya albarkace ku da ɗan abinci biyu."
Ibnu Majah ne ya Rawaito shi - Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana cin abinci tare da sahabbansa shida, sai wani Balarabe ya zo tare da su sai ya shiga tare da su sai ya ci sauran tare da mors biyu. Koyaya, idan mutum bai sami guba ba, ana cire albarkar daga cikin abincinsa.

Madogara

- سنن الترمذي لمحمد بن عيسى الترمذي، تحقيق وتعليق: أحمد محمد شاكر ومحمد فؤاد عبد الباقي وإبراهيم عطوة عوض -شركة مكتبة ومطبعة مصطفى البابي الحلبي، مصر الطبعة: الثانية، 1395 هـ - 1975 م - سنن ابن ماجه لابن ماجه أبو عبد الله محمد بن يزيد القزويني، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي- دار إحياء الكتب العربية - فيصل عيسى البابي الحلبي. - مسند الإمام أحمد بن حنبل المحقق: شعيب الأرنؤوط - عادل مرشد، وآخرون إشراف: د عبد الله بن عبد المحسن التركي مؤسسة الرسالة الطبعة: الأولى، 1421 هـ - 2001 م. - شرح رياض الصالحين؛ للشيخ محمد بن صالح العثيمين، مدار الوطن، الرياض، 1426هـ. - نزهة المتقين بشرح رياض الصالحين، تأليف مصطفى سعيد الخن-مصطفى البغا-محي الدين مستو-علي الشربجي-محمد أمين لطفي-مؤسسة الرسالة-بيروت –لبنان-الطبعة الرابعة عشرة 1407. - بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين لسليم بن عيد الهلالي دار ابن الجوزي، الطبعة الأولى 1418. - دليل الفالحين لطرق رياض الصالحين -المؤلف: محمد علي بن محمد بن علان الصديقي-اعتنى بها: خليل مأمون شيحا-دار المعرفة للطباعة والنشر والتوزيع، بيروت – لبنان-الطبعة: الرابعة، 1425 هـ - 2004 م. -المعجم الوسيط-المؤلف: مجمع اللغة العربية بالقاهرة- (إبراهيم مصطفى / أحمد الزيات / حامد عبد القادر / محمد النجار)-الناشر: دار الدعوة. - مختصر الشمائل المحمدية- محمد بن عيسى الترمذي، الناشر: المكتبة الإسلامية - عمان – الأردن- اختصره وحققه محمد ناصر الدين الألباني.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

To ku haɗu akan abincinku, kuma ku ambaci sunan Allah akansa, za'a sanya muku albarka a cikinsa

عَنْ وَحْشِيِّ بْنِ حَرْبٍ رَضيَ اللهُ عنه: أَنَّهُمْ قَالُوا: يَا رَسُولَ اللَّهِ، إِنَّا نَأْكُلُ وَلَا نَشْبَعُ، قَالَ: «فَلَعَلَّكُمْ تَأْكُلُونَ مُتَفَرِّقِينَ؟» قَالُوا: نَعَمْ. قَالَ: «فَاجْتَمِعُوا عَلَى طَعَامِكُمْ، وَاذْكُرُوا اسْمَ اللَّهِ عَلَيْهِ، يُبَارَكْ لَكُمْ فِيهِ».
Daga Wahshi ɗan Harb - Allah Ya yarda da shi -: Cewa su sun ce: Ya Manzon Allah, lallai mu mun kasance muna ci ba ma ƙoshi, ya ce: «Wataƙila kuna ci ne a rarrabe?» Ya ce: Eh. Ya ce: «To ku haɗu akan abincinku, kuma ku ambaci sunan Allah akansa, za'a sanya muku albarka a cikinsa».
Abu Dawud ne ya rawaito shi da Ibnu Majah da AhmadDarajaHasan ne
Sharhi

Wasu daga cikin sahabbai sun tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai suka ce: Lallai mu mun kasance muna ci amma bama ƙoshi. Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce musu: Wataƙila kuna rarrabuwa a lokacin ci; sai kowa ya ci shi kaɗai? Suka ce: Eh. Ya ce: To ku haɗu ku ci ba'a rarrabe ba, kuma ku ambaci sunan Allah a lokacin ci da faɗin: Bismillah (Da sunan Allah), za'a sanya muku albarka a cikinsa, kuma zaku ƙoshi.

Fa’idoji
  1. Haɗuwa a abinci da kuma ambatan Allah a lokacin ci sababi ne na samun albarka a cikin abinci, da kuma ƙoshi daga cinsa.
  2. Rabuwa dukkaninta sharri ce, haɗuwa kuwa dukkaninta alheri ce.
  3. Kwaɗaitarwa akan haɗuwa da kuma ambatan Allah a lokacin abinci.
  4. Sindi ya ce: Da haɗuwa ne albarkatu suke sauka a cikin abin ci, kuma da ambatan Allah ne Shaiɗan yake hanuwa daga kaiwa ga abinci.
Madogara

سنن أبي داود (5/ 588) (3764). سنن ابن ماجه (4/ 418) (3286). مسند أحمد (25/ 485) (16078). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (4/ 217). نزهة المتقين بشرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 607). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 59).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
8 cikin 20
Hadisai 20
  1. Idann dayanku ya ci abinci to kar ya goge hannunsa har sai ya sude shi.
  2. "Duk abun Shan da ya sa Maye to Haramun ne"
  3. Haramta giya ya sauka ne kuma ana yin ta daga abubuwa biyar ne: inibi, dabino, zuma, alkama, da sha'ir"
  4. Kada ɗayanku ya kuskura ya taɓa azzakarinsa da damansa, a halin yana fitsari, kuma kada ya yi tsarki na bayan gida da damansa, ko kuma ya yi nunfashi a ƙwarya
  5. Cewa wani mutum ya ci a wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da hannun hagunsa, sai Ma’aikin Allah ce da shi: "Ka ci da hannun damanka ." Ya ce: Ba zan iya ba. Ya ce: "Ba za ko ka iya ba
  6. ‌Lallai Shaiɗan yana halatta abin cin da ba'a ambaci sunan Allah a kansa ba
  7. Allah ya albarkace ku da ɗan abinci biyu
  8. To ku haɗu akan abincinku, kuma ku ambaci sunan Allah akansa, za'a sanya muku albarka a cikinsa
  9. Kada ku kwatanta, domin Annabi - Salati da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya hana Alkurani, sannan ya ce: Ban da mutum ya nemi izinin dan uwansa.
  10. Na karshensu ya shayar da mutane
  11. Mun kasance a zamanin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - muna cin abinci yayin tafiya, muna sha a tsay
  12. Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - bai taba zagin abinci ba, idan ya so shi, ya ci, in kuma ya ki shi, to ya bar shi.
  13. Dayanku baya shan giya a tsaye, saboda haka duk wanda ya manta, to ya tashi
  14. Manzon Allah -SAW- ya hana shan ruwa daga korama ko gora
  15. Manzon Allah - Salatin Allah da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya hana kwarangwal mata.
  16. Lalle Allah Yana yarda da bawanda idan ya ci abin ci, yana gode masa a kai, ko in ya sha abin sha sai ya gode masa akan hakan
  17. Na Kasance tare da Anas Bn Malik -Allah ya yarda da shi- a wajen wasu Mutane Maguzawa, sai aka zo da Alawa a cikin Daro na Azurfa, amma bai Sha ba
  18. Lallai cewa Manzon Allah SAW yayi Umarni da Suxe Yatsu da kuma kwano kuma ya ce: Lallai cewa ku baku san a wanne Albarkar take ciki ba
  19. Ya kai yaro, ka ambaci Allah, ka ci da damanka, ka ci abin da ke gabanka
  20. Idan ɗayanku zai ci; to, ya ci da damansa, idan zai sha; to, ya sha da damansa, domin cewa Shaiɗan yana ci da hagunsa, kuma yana sha da hagunsa

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com