Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Lalle Allah Yana yarda da bawanda idan ya ci abin ci, yana gode masa a kai, ko in ya sha abin sha sai ya gode masa akan hakan

عن أنس بن مالك رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «إِنَّ اللهَ لَيَرْضَى عَنِ الْعَبْدِ أَنْ يَأْكُلَ الْأَكْلَةَ فَيَحْمَدَهُ عَلَيْهَا، أَوْ يَشْرَبَ الشَّرْبَةَ فَيَحْمَدَهُ عَلَيْهَا».
Daga Anas Ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: Lalle Allah Yana yarda da bawanda idan ya ci abin ci, yana gode masa a kai, ko in ya sha abin sha sai ya gode masa akan hakan.
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana bayyana godiyar da bawa ya ke yi wa Ubangijinsa a kan falalarSa da ni’imarSa suna cikin al’amuran da ake samun yardar Allah da su, idan ya ci abin ci sai ya ce: Na gode wa Allah. Idan ya sha abin sha sai ya ce: Alhamdulillah.

Fa’idoji
  1. Karamcin Allah Mabuwayi, haƙiƙa shi ne ya ba da arziƙi, kuma yake yarda da a gode masa.
  2. Yardar Allah ana samunta da abu mafi sauƙi, kamar godiya ga Allah bayan ci da sha.
  3. Yana daga cikin ladubban ci da sha: Godiya ga Allah maɗaukaki bayan ci da sha.
Madogara

صحيح مسلم (4/ 2095) (2734). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمصطفى الخن وغيره (1/ 164). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 215). شرح رياض الصالحين من كلام سيد المرسلين، لابن عثيمين (2/ 203). كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين. تطرز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص764).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
LADUBBAN CI DA SHA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com