Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Ya kai yaro, ka ambaci Allah, ka ci da damanka, ka ci abin da ke gabanka

عن عُمر بن أبي سلمة رضي الله عنه قال: كُنْتُ غُلَامًا فِي حَجْرِ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، وَكَانَتْ يَدِي تَطِيشُ فِي الصَّحْفَةِ، فَقَالَ لِي رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «يَا غُلَامُ، سَمِّ اللهَ، وَكُلْ بِيَمِينِكَ، وَكُلْ مِمَّا يَلِيكَ» فَمَا زَالَتْ تِلْكَ طِعْمَتِي بَعْدُ.
Daga Umar ɗan Abu Salama - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na kasance yaro a kulawar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, hannuna ya kasance yana yawo a faranti, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce da ni: "Ya kai yaro, ka ambaci Allah, ka ci da damanka, ka ci abin da ke gabanka" hakan bai gushe ba shi ne irin cin abincina bayan nan.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Umar Dan Abu Salama - Allah Ya yarda da su - ɗan matar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - Ummu salamah - Allah Ya yarda da ita - yana ba da labari - (cewa) ya kasance ƙarƙashin renonsa da kulawarsa -, cewa ya kasance a tsakiyar cin abinci yana yawo da hannunsa asasannin ƙwarya (kwanon abin ci) don ya ɗauki abincin, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya sanar da shi ladubba uku daga ladubban cin abinci. Na farkonsu: Faɗin "Da sunan Allah" a farkon ci. Na biyunsu: Cin abinci da dama. Na ukunsu: Cin abinci daga ɓangaren da yake kusa daga gare shi na abincin.

Fa’idoji
  1. Daga ladubban ci da sha (akwai) ambaton Allah a farkonsa.
  2. Sanar da yara ladubba, musamman ma waɗanda ke ƙarƙashin kulawar mutum.
  3. Tausayin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da yalwar ƙirjinsa a koyar da yara da ladabtar da su.
  4. Daga ladubban abinci akwai cin abin da ke gaban mutum, sai dai idan ya kasance nau'uka ne da yawa, to, yana da damar da zai ɗauki wanda ya so.
  5. Lazimtar sahabbai da abin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ladabtar da su da shi, hakan abin fahimta ne daga faɗin Umar: Hakan bai gushe (irin) cin abincina ba bayan nan.
Madogara

صحيح البخاري (7/ 68) (5376)، (3/ 61) (2092). صحيح مسلم (3/ 1599) (2022). شرح النووي على مسلم (13/ 193). توضيح الأحكام مِن بلوغ المرام، للبسام (5/ 440). فتح ذي الجلال والإكرام شرح بلوغ المرام، لابن عثيمين (4/ 616). منحة العلام في شرح بلوغ المرام، لعبد الله الفوزان (7/ 439). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (3/ 169).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
LADUBBAN CI DA SHA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com