Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Kada ɗayanku ya kuskura ya taɓa azzakarinsa da damansa, a halin yana fitsari, kuma kada ya yi tsarki na bayan gida da damansa, ko kuma ya yi nunfashi a ƙwarya

عَنْ أَبِي قَتَادَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «لَا يُمْسِكَنَّ أَحَدُكُمْ ذَكَرَهُ بِيَمِينِهِ وَهُوَ يَبُولُ، وَلَا يَتَمَسَّحْ مِنَ الْخَلَاءِ بِيَمِينِهِ، وَلَا يَتَنَفَّسْ فِي الْإِنَاءِ».
Daga Abu Katada - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Kada ɗayanku ya kuskura ya taɓa azzakarinsa da damansa, a halin yana fitsari, kuma kada ya yi tsarki na bayan gida da damansa, ko kuma ya yi nunfashi a ƙwarya".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana wasu ladubba; yayin da ya hana mutum ya riƙe azzakarinsa a halin fitsari da hannunsa na dama, ko kuma a gusar da najasa daga gaba ko baya da hannun dama; domin dama an tanadeta ne dan manyan abubuwa, kamar yadda ya yi hani mutum ya yi numfashi a cikin ƙwaryar (kofi) da yake sha acikinta.

Fa’idoji
  1. Bayanin rigayar musulunci a ladubba da tsafta.
  2. Nisantar abubuwan ƙazanta, idan an yi buƙatuwa zuwa taɓa su, to ya kasance da hagu ne.
  3. Bayanin matsayin dama da falalarta akan hagu.
  4. Cikar shari'ar musulunci da tarowar koyarwarta.
Madogara

صحيح البخاري (1/ 42) (154). صحيح مسلم (1/ 225) (267). تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، للبسام (ص41). تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام، لابن عثيمين (1/ 45).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
LADUBBAN CI DA SHA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com