Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Cewa wani mutum ya ci a wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da hannun hagunsa, sai Ma’aikin Allah ce da shi: "Ka ci da hannun damanka ." Ya ce: Ba zan iya ba. Ya ce: "Ba za ko ka iya ba

عَنْ سَلَمَةَ بْنِ الْأَكْوَعِ رضي الله عنه: أَنَّ رَجُلًا أَكَلَ عِنْدَ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ بِشِمَالِهِ، فَقَالَ: «كُلْ بِيَمِينِكَ»، قَالَ: لَا أَسْتَطِيعُ، قَالَ: «لَا اسْتَطَعْتَ»، مَا مَنَعَهُ إِلَّا الْكِبْرُ، قَالَ: فَمَا رَفَعَهَا إِلَى فِيهِ.
Daga Salamah Dan Akwa'a - Allah Ya yarda da shi -: Cewa wani mutum ya ci a wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da hannun hagunsa, sai Ma’aikin Allah ce da shi: "Ka ci da hannun damanka ." Ya ce: Ba zan iya ba. Ya ce: "Ba za ko ka iya ba", ba abin da ya hana shi sai girman kai, ya ce: Bai kara daga shi zuwa bakinsa ba.
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ga wani mutum yana ci da hannunsa na hagu, sai ya umarce shi da ya ci da hannunsa na dama, sai mutumin ya amsa masa dan girman kai da karya da cewa shi ba zai iya ba! sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi mummunan addu'a akansa da haramta masa ci da dama, sai Allah Ya amsa addu'arsa da shanyewar hannunsa na dama, bai kara daga shi zuwa bakinsa ba bayan hakan da abinci ko abin sha.

Fa’idoji
  1. wajabcin ci da dama, da haramcin ci da hagu.
  2. Girman kai daga aikata hukunce-hukuncen shari'a mai aikata shi yana cancantar ukuba.
  3. Girmamawar Allah ga AnnabinSa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da amsa addu'arsa.
  4. Halaccin umarni da aikin alheri da hani daga abin ki a kowanne hali har a cikin halin ci.
Madogara

صحيح مسلم (3/ 1599) (2021). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 239). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 183). كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (3/ 396).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
LADUBBAN CI DA SHA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com